An bude baje kolin masana’antun al’adu da na yawon bude ido na kasar Sin na 2026 jiya Alhamis a birnin Tianjin da ke arewacin kasar. Baje kolin ya ja hankalin masana’antun al’adu da yawon bude ido sama da 2,500 daga kasashe da yankuna 20.
Taron na kwanaki 4 wanda ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta dauki nauyi, ya kuma samu halartar hukumomin da kungiyoyin masana’antun na kasa da kasa guda 10.
Baje kolin mai taken “Zurfafa Dunkulewar Al’adu da Yawon Bude Ido, Samar da Kyakkyawar Rayuwa Mai Fasahohin Zamani,” na kunshe da wuraren nune-nune 10 da suka hada da na ala’du da yawon bude ido da harkokin kasuwanci ta dijital masu tasowa da kayayyakin bude ido da wuraren hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da na bude ido na cikin gida da na kayayyakin sayayya.
Mataimakiyar shugaba, kuma sakatare-janar ta dandalin bunkasa tattalin arzikin bangaren yawon bude ido na duniya Pansy Ho Chiu-king, ta ce tana fatan baje kolin zai ingiza hadin gwiwa tsakanin masana’antun kasa da kasa da taimakawa kayayyakin al’adu da na yawon bude ido na kasar Sin shiga kasuwannin duniya, da jawo karin jarin waje da kwarewa zuwa kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)














