ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Hare-haren Ƴan Bindiga A Wasu Ƙauyukan Kaduna

by Leadership Hausa
3 weeks ago
Bindiga

Mun dai ƙara dawo, domin yin sharhi, domin wannan Jaridar, ba sau ɗaya ba sau biyu ba, ba kuma sau uku ba, ta yi sharhi kan koma bayan da aka samu a shekarun baya, na rashin iya gudanar da shugabanci na gari, a ƙasar.

Kazalika, a sharhin Jaridar na baya, ta bayyana jeren yawan ƴan Adama da aka kashe a wasu ƙauyuka da kuma yin tir da gazarwar tsare-tsaren da mhukunta suka samar.

Duk a sharhin na baya, Jaridar ta kuma buƙaci da a tabbatar da an wanzar da yin gaskiya.

ADVERTISEMENT

Bayan kasheshen da ƴan bindiga suka yi a, Kajuru, after Zangon Kataf, da kuma wanda suka yi a Chikun, bayan kisan da suka yi, a ranar bikin Kirsimete, da sauran kashe-kashen rashin imani da suka aiwatar a yankin Arewa maso Yamma, hakan na ci gaba da zama, abin baƙin ciki.

Wannan sharhin Jaridar na yanzu, ya bijoro ne, biyo bayan sake kai wasu sabbin hare-haren da ƴan bindigar suka ƙaddamar a ƙauyen Naridon, na mazaɓar Kamaru, da harin masarautar Chawai, a ƙaramar hukumar Kauru a Kaduna.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Miyagun, sun kai harin ne, a daren ranar, 27 na watan Yulin 2026, inda suka ɗauki rayukan waɗanda ba su ji, kuma basu gani ba har guda talatin, wanɗanda daga cikinsu, akwai maza tara, mata goma sai kuma yara sha ɗaya.

Bugu da ƙari, a ranar ɗaya na watan Agustan 2026, Cocin Catholic Diocese da ke a garin Kafanchan, ta gudanar da bizne mutane 27, da ƴan bindiga suka hallaka.

Ya zuwa yanzu, sau uku ke nan, ana kai hare-hare a cikin dai wannan ƙauyen duk a cikin watanni sha ɗaya.

Mun ƙara bijero da wannan sharhin ne, ba wai domin cewa, irin waɗannan rubuce-rubucen za su iya kawo ƙarshen gazawar da mahukuntan, suka yi a shekaru bay aba, sai domin a sake fargar da su.

Wannan sharhin, ƙunshe yake da hujoji da dama, musamman na irin ƙalubalen rashen tsaro, da Nijeriya ke ci gaba da fuskanta, wanda kuma ya waja, mahukunta su farka daga barcinsu, domin yin wani abu akai.

A cewar wani ganau, mai suna Mark Ɓincent, hare-haren na kwana-kwanan, sun zo ne, a cikin jimamin firgici da tsoratarwa, musamman duba da cewa, an gudanar da su ne, a tsakiyar dare, inda aƙalla ƴan bidiga  hamsin ɗauke da muggan makamai, suka aikata ta’asarsu.

Ya ce, sun gudanar da kashe-kashen ne, ta hanyar shiga daga gida zuwa gida, suka rinƙa harbe mutane, inda ya ƙara da cewa, akwai gidan da ƴan bindigar, suka kashe ɗaukacin alhalin gidan, a cikin ɗakinsu na kwana.

Wasu da suka arce zuwa dazuka, domin tseratar da rayuwarsu, ƴan bindigar sun bi sahunsu, suka kuma hallaka su.

Ya ci gaba da cewa, duk a cikin daren ranar, akwai gidan da aka hallaka yara biyar, inda yaro ɗaya da ya rayu, ke kwance a Asibiti ake ci gaba da ceto rayuwarsa.

Bayan kwana ɗaya da aukuwar hare-haren, kafar yaɗa labarai ta waje ta AP, ta tuntuɓi kwamishinan trsaron cikin gida na Kaduna, kan kai hare-haren, sai dai, ya ka da baki ya ce, har yanzu, ba a yi masa cikaken bayani, kan lamarin ba.

Ƴan bindigar dai, sun gama cin Karesu babu babbaka sun kuma yi gaba, yayin da kuma ake ci gaba da ƙidayar yawan gawarwakin da aka hallaka

Harin na ƙauyen Naridon, ba shi ne, karo na farko ba, domin ƙungiyar CAN ta tabbatar da cewa, an kai irin waɗannan hare-haren ma, a wata Agustan 2025, inda aka hallaka mutane bakwai.

Haka zalika, a watan Yunin 2026, duk a ƙauyen na Naridon, wasu maharani sun kashe mutane tara tare da raunata mutane sha ɗaya.

Wannan, abin baƙin ciki ne, duba da cewa, a tsakanin watanni sha ɗaya a ƙauyen na Naridon, an gudanar da bizne mutane n agama gari, a cikin watanni sha ɗaya har karo na uku.

Bayan hari na ɗaya, na biyu har zuwa na uku a ƙauyen, babu wani abu, da ya sauya na ɗaukar ƙwararan matakai, daga ɓangaren mahukunta.

Sai dai, za a iya cewa, bayan harin na uku, gwamnan Kaduna ta umarci jami’an taro, da su ci gaba da ƙara ƙaimi na tabbatar da tsaro, inda kuma shugaban ƙasa, ya danganta kashe-kashen, a matsayin aikin ta’addanci.

Kazalika, ba wai hare-haren na ƙauyen Naridon kaɗai bane, akwai kuma wanda aka ƙaddamar da dare a ƙauyen Lajinge a Sokoto, a ranar 19 ga watan Yulin 2026, inda maharani, suka kashe mutane sha ɗaya, suka kuma ƙone wasu shida da ransu, a cikin gidajensu, ta hanyar yin amfani da Man Fetur.

Haka zalika, duk a cikin wannan makon, a wani hari da maharani suka kai a yankin Otukpo, na jihar Biniwe, sun hallaka mutane shida.

A cikin wasu jihohin ƙasar, a ƙasa da mako biyu, a wasu karkara na ƙasar, an bizne aƙalla mutane 58, kuma ba tare da wallafa cewar, an kama mutun ɗaya, da suka aikata kisan ba.

A kwanan baya dai, a Kaduna ƙungiyar gwanonin Arewacin ƙasar, ta ƙaddamar da wata gidauniya ta tsaro, bisa yin alƙawarin a duk wata kowacce jiha, za ta bayar da gudunmawar Naira biliyan ɗaya, a matsayin na ta gudunmawar.

Ta ƙaddamar da gidauniyar ce, mao biyu, kafin kai hare-haren na ƙauyen Naridon.

Haka zalika, ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta ƙasa da ƙasa wato Amnesty International, da ke ci gaba da bibiyar irin waɗannan kashe-kashen, ta fitar da wani rahoton da ke nuna cewa, a jihohi bakwai na Arewacin ƙasar, a watan Mayun 2025, aƙalla an hallaka mutane 10,217 a cikin shekaru biyu kacal, a  ƙarƙashin mulkin gwamnatin tarayya mai ci.

Rahoton ƙungiyar ya ce, jihar Biniwe, an hallaka kimanin mutane 6,900.

Sai dai, gwamnatin, ko kusa, ba ta son sanin waɗannan alƙaluman kuma ba ta ɗauki wasu ƙwararan matakai, na magance kai hare-haren ba.

A baya mun yi kira da a tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ake yawan samun kai hare-haren, mun kuma yi kira da a samar da tsarin kai ɗaukin gaggawa na dakile hare-hare.

Kazalika, mun yi kira da samar da tsarin samun bayanan sirri, tare da tarwatsa sansanonin ƴan bindiga, mun yi kira da a hukunta duk wanda ke da hannu akai hare-haren.

A nan, za mu kuma sake yin waɗannan kiraye-kirayen, ba wai domin kiraye-kirayen sun yi ƙaranci ba, amma saboda yin gum ɗin na ƙin yin kiran, tamkar wata gazawa ce.

Alumomin da ke a karkara a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa, ta tsakiya da kuma yankin tsakiyar Nijeriya wato Middle, na da haƙƙin kan gawamnati, na ta cika alawarin da ta yi masu, kafin wata waƙi’ar, ta ƙara aukuwa.

Idan har gwamnati za ta iya yin amfani da ɗimbin kuɗaɗe domin gudanar da wasu ayyukan da suka shafi ciyar da ƙasar gaba, shi menene ke hana ta, tabbatar da tsaro a mai ɗorewa, a ƙauyukan da ake yawan samun kai hare-haren ƴan bindiga?

Ya zama wajbi tun daga matakin fadar shugaban ƙasa da gwamnatin Kaduna, da sauran gwamnonin da ke a Arewa, su tashi haiƙan, domin tabbatar da tsaro, kafin a sake samun kai wasu hare-haren.

Kashe rayukan alummar da ba su ji ba su kuma gani ba a ƙauyen na Naridon, lamari ne, da wuce batun yin sharhi a Jirida kawai, amma sai idan har gwamnati ta nuna gaske take domin magance kai hare-haren.

Wannan Jaridar koda Tawadar Alƙamin zai ƙare, za ta ci gaba da yin rubuce-rubuce kan matsalar.

Bindiga
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Bindiga

2027: Zaɓen Osun Ya Nuna Yadda Jam'iyyun Adawa Za Su Iya Kayar Da Tinubu 

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.