Yau Asabar, babbar hukumar kula da kasuwa ta Sin wato SAMR, ta fitar da alkaluman da ke nuna cewa, kamfanonin da aka kafa a fannin sabbin masana’antu suna samun ci gaba, wanda hakan ke hanzarta sauye-sayuen masana’antun kasar.
Alkaluman sun nuna cewa, a rabin farko na bana, sabbin kamfanoni 400,000 da aka kafa dake da alaka da “masana’antu masu tasowa guda 8” na Sin, wadanda suke da matukar muhimmanci wajen gina karfin juriyar masana’antu da tsarin samar da kayayyaki, suna ci gaba da taka rawar gani bisa jagorancin kirkire-kirkire.
Bugu da kari, an kafa sabbin kamfanoni 55,000 dake da alaka da fasahar AI, adadin ya karu da kashi 28% bisa makamancin lokacin a bara, kuma an kafa sabbin kamfanoni 116,000 a fagen mutum-mutumin inji masu siffar dan Adam, adadin ya karu da kashi 9.5%, wanda hakan ya haifar da sabbin ci gaban tattalin arziki cikin sauri.
A fannin masana’antu masu fasahar zamani, ya zuwa karshen watan Yunin bana, jimillar kamfanonin dake da alaka da wannan a Sin ta kai 330,000, inda aka kafa sabbin kamfanoni 15,000 a rabin farko na banan. Daga cikinsu, adadin sabbin kamfanonin da aka kafa a fannin masana’antar kera jiragen sama da rokoki masu dauke da kayayyaki ya karu da kashi 185.7% bisa makamancin lokaci a bara, masana’antar kera igiyar sadarwar intanet na fiber da optical cable ta karu da kashi 129.4%, ita kuma masana’antar kera na’urorin hada laturoni na integrated circuit ta karu da kashi 24.2%.
Hukuamr SAMR ta kuma bayyana cewa, nan gaba za a mayar da hankali kan manyan fannoni guda uku, wato inganta yanayin kasuwanci da kiyaye gasa mai adalci, da kuma habaka ingancin ci gaba, ta yadda za a fadada yanayin ci gaba mai adalci da tsari ga dukkan nau’ikan kamfanoni.(Safiyah Ma)














