ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Takarar NDC Sun Yaba Wa Seriake Dickson Bayan INEC Ta Wallafa Bayanansu

by Bello Hamza
1 month ago
NDC

Mutanen da za su tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Nijeriya Democratic Congress (NDC) sun yaba wa jagoran Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Henry Seriake Dickson, biyo bayan wallafa sunayen ƴan takara na hukuma da Hukumar Zaɓe ta yi.

Wallafa sunayen ƴan takarar da INEC ta yi ya cire fargabar da aka kwashe makonni ana yi tsakanin ƴan takarar jam’iyyar, musamman waɗanda ke neman kujeru a Majalisar Tarayya.

Mambobin jam’iyyar sun bayyana Sanata Dickson a matsayin jagoran kwantar da hankula wanda ya sami nasarar daidaita saɓani sakamakon zaɓen fitar da gwanaye, tare da haɗa kan shugabannin jihohi da kuma kauce wa rikicin cikin gida gabanin zaɓen shekarar 2027.

ADVERTISEMENT

Yayin da suke yaba wa da tsarin, da yawa daga cikin ƴan takara sun jinjina wa zaɓen fitar da gwanaye na jam’iyyar saboda yadda aka gudanar da shi a bayyane kuma ba tare da karɓar kuɗaɗe a hannun ƴan takara ba.

Sanata Nkechi Nwaogu, wadda ita ce ƴar takarar sanata na NDC a Abia ta tsakiya kuma mamba a Majalisar dattawa ta 8, ta yaba da salon shugabancin siyasar Dickson a lokacin ƙalubalen gabatar da sunayen ƴan takara.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

“Jagoran mu Sanata Seriake Dickson ya cancanci yabo saboda yadda ya jagoranci mu lokutan ƙalubale da kuma fitar da ƴan takara,” in ji Nwaogu.

Ta kuma yi kira ga waɗanda basu samu tikiti ba da su kasance masu biyayya

Haka zalika, wani dan takara daga Jihar Edo ya ƙarya jita-jitar cewa an karɓi kuɗi domin ba da tikiti, inda ya bayyana cewa tattaunawar da aka yi da shugabannin jam’iyyar na ƙasa ta maida hankali ne kawai kan haɗin kan jam’iyya da kuma sulhu na dabarun siyasa maimakon buƙatar kuɗi.

Haka kuma, masu neman takarar da ba su samu nasara ba sun alƙawarta goyon bayansu ga jam’iyyar.

Mazi Nnamdi Dickson Iroegbu, wanda ya nemi takarar Majalisar Wakilai ta Aboh Mbaise/Ngor Okpala a Jihar Imo, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da kasancewarsa a jam’iyyar duk da cewa sunansa ba ya cikin jerin sunayen da aka wallafa.

Shugabannin jam’iyyar sun bukaci dukkan mambobi da su haɗa kai, su maida hankali kan ƙoƙarin sulhunta mambobi bayan zaɓen fitar da gwanaye, kuma su kasance a bayan ƴan takarar NDC a faɗin Nijeriya domin yin adawa ta haɗin kai.

A wata sabuwa kuma,NDC ta tabbatar da Mrs. Asemota a matsayin ƴar takarar Sanatan Edo ta kudu.

Jam’iyyar Nijeriya Democratic Congress (NDC) ta bayyana cewa Mrs. Epelle-Asemota Bridgitte Osayuki ce yar takarar da aka sani a hukumance domin neman kujerar Sanata a yankin Edo ta Kudu, yayin da ta yi watsi da kuskuren da hukumar zaɓe ta yi na sauya sunanta.

Wannan bayanin ya biyo bayan wallafa bayanan ƴan takara da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi a kwanan nan.

Hàkan na zuwa ne bayan INEC ta saka sunan Mrs. Asemota amma sai tayi amfani da hoton wani mai neman takara daban da kuma shaidun karatunsa.

A wata sanarwa da Agada Abuh Theophilus, Darakta Mai Kula da Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jam’iyyar NDC ya fitar, jam’iyyar ta ɗora alhakin kuskuren a kan wasu mutane a cikin hukumar INEC, kuma ta tabbatar da cewa an bi duk hanyoyin mika sunaye na doka sau da ƙafa.

Yayin da take maida martani kan sukar siyasa da ake yiwa jam’iyyar, NDC ta yi Allah-wadai da yadda cin zarafin yan takarar ta daga jam’iyyun adawa.

Jam’iyyar ta kuma jaddada goyan baya ga yar takararta bisa tsawon shekarun da ta shafe tana hidimta wa al’umma a Jihar Edo da kuma kyakkyawar dangantakar iyalinta a yankin, inda ta tuna cewa ita ce yar takarar Jam’iyyar Labour ta Majalisar Tarayya a zaɓen 2023, kuma tsohuwar Shugabar Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Jihar Edo, sannan tsohuwar shugabar Ƙungiyar Malamai ta ASUSS.

NDC
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Wane Ne Jorge Messi: Mahaifin Lionel Messi?

Wane Ne Jorge Messi: Mahaifin Lionel Messi?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.