ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kammala Kashi 90% Na Titin Jirgin Ƙasan Kaduna – Kano

by Abubakar Sulaiman
4 minutes ago
Kaduna

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin layin dogo mai amfani da ma’aunin hanya na zamani daga Kaduna zuwa Zariya da Kano ya kaci kusan kashi 90 cikin 100, amma matsalar mallakar filaye da biyan diyya a cikin birnin Kaduna na kawo cikas ga kammala haɗin hanyar da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.

Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Funso Adebiyi, ne ya bayyana hakan a ranar 23 ga Oktoba, 2026, yayin ziyarar duba aikin da ya haɗa da tafiya a jirgin ƙasa daga Jaji zuwa Kano. Ya ce gwamnati na ƙoƙarin warware matsalolin filayen, kuma za a ba su kulawa ta musamman bayan tawagar ta koma Abuja.

Adebiyi ya bayyana cewa ɓangaren da tawagar ta duba ya kai kusan kilomita 145 daga cikin jimillar kilomita 200 na hanyar Kaduna zuwa Kano, inda ya ce akwai sauran aikin kusan kilomita 10 a wannan ɓangaren. Ya kuma yaba da ingancin shimfiɗa layin dogo, da magudanan ruwa, da daidaita ƙasa da kuma kare gangaren da ke gefen hanya.

ADVERTISEMENT

Ya ce warware matsalar filaye da biyan diyya a Kaduna zai taimaka wajen haɗa tashar Jaji da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna, ta yadda fasinjoji za su iya tafiya daga Abuja zuwa Kaduna, Zariya da Kano ba tare da katse hanya ba. Sai dai gwamnati ba ta bayyana takamaiman ranar da za a warware matsalar ko ranar fara jigilar fasinjoji a wannan hanyar ba.

Adebiyi ya kuma bayyana cewa ana sa ran kammala sauran sassan layin dogo daga Kano zuwa Kazaure, da Daura da Katsina kafin ƙarshen Disambar 2026. Daraktar Sashen Sufurin Jiragen Ƙasa a ma’aikatar, Injiniya Habiba Buhari, ta ce tawagar ta duba ingancin layin, da magudanan ruwa da sauran abubuwan da suka shafi amincin fasinjoji kafin a kammala aikin da gudanar da gwajin jiragen ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

NNPC Ya Samu Koma Baya Bayan Tura N11.14tn Asusun Tarayya Cikin Watanni Tara

Kaduna
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
  • Abubakar Sulaiman
    Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani
  • Abubakar Sulaiman
    Ba Za Mu Yarda Da Maguɗin Zaɓe Ba – Dino Melaye Ya Gargaɗi INEC
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa A 2027 – Barau

MASU ALAKA

Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu
Labarai

Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

November 5, 2026
Kar Ku Tayar Da Hankulanku, Mun Samo Fetur Fiye Da Lita Biliyan 1.5 – NNPCL
Labarai

NNPC Ya Samu Koma Baya Bayan Tura N11.14tn Asusun Tarayya Cikin Watanni Tara

November 5, 2026
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
Rahotonni

Abubuwa 6 Da Za Su Iya Haramta Maka Yin Zaɓe A Nijeriya

November 5, 2026

LABARAI MASU NASABA

An Kammala Kashi 90% Na Titin Jirgin Ƙasan Kaduna – Kano

An Kammala Kashi 90% Na Titin Jirgin Ƙasan Kaduna – Kano

November 5, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

November 5, 2026
Kar Ku Tayar Da Hankulanku, Mun Samo Fetur Fiye Da Lita Biliyan 1.5 – NNPCL

NNPC Ya Samu Koma Baya Bayan Tura N11.14tn Asusun Tarayya Cikin Watanni Tara

November 5, 2026
Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya Na Mata U-17

Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya Na Mata U-17

November 5, 2026
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

Abubuwa 6 Da Za Su Iya Haramta Maka Yin Zaɓe A Nijeriya

November 5, 2026
Kaduna

Yadda Tinubu Ke Yawan Ciyowa Nijeriya Bashi Abin Tambaya Ne – Atiku

November 5, 2026
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nemi Hukunta Asibitocin Da Suka Ƙi Karɓar Majinyatan Gaggawa

November 5, 2026
Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18

Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18

November 5, 2026
Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

November 4, 2026
Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

November 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.