Akalla ’yan bindiga 17 da ’yansanda 10 ne suka rasa rayukansu a wata mummunar arangama tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a kauyen Rafin Makuku, da ke karamar hukumar Sakaba ta Jihar Kebbi.
Rundunar ’Yansandan Jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce arangamar ta auku ne a ranar 10 ga Agusta, 2026, yayin da jami’an tsaro ke dakile wasu ’yan bindiga dauke da manyan makamai da ke zirga-zirga tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa jami’an sun yi musayar wuta da ’yan bindigar da misalin karfe 9:25 na safe a yankin Rafin Makuku.
Ya ce jami’an tsaron sun samu nasarar kashe akalla ’yan bindiga 17 tare da kona babura hudu na maharan a yayin arangamar.
Sai dai rundunar ta ce ta yi babban rashi, inda ‘yansanda 10 suka rasa rayukansu, yayin da wasu jami’ai biyu suka samu raunuka kuma suke karbar magani a asibiti.
Haka kuma, wasu ’yan garin Rafin Makuku biyu sun mutu sakamakon musayar wutar.
SP Usman ya bayyana jami’an da suka rasa rayukansu a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma, yana mai cewa rundunar ba za ta manta da irin sadaukarwar da suka yi ba.
Ya ce babban abin da rundunar ta mayar da hankali a kai a yanzu shi ne tallafa wa iyalan jami’an da sauran wadanda lamarin ya shafa, kula da wadanda suka samu raunuka, tare da ci gaba da farautar ’yan bindigar da suka tsere.
Wani mazaunin Rafin Makuku, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa an shafe wani lokaci ana jin karar harbe-harbe mai tsanani a yankin, inda ya ce ya ga gawarwaki da dama, amma bai iya tantance adadin wadanda suka mutu ba.














