ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da ₦2.07bn Alawus-alawus Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu

by Sulaiman and Umar Faruk
3 weeks ago

Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2.07 a watan Agusta 2026 domin biyan wasu alawus-alawus, basussuka da sauran hakkokin ma’aikatan manyan makarantun jihar. Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Isah Abubakar Tunga, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Birnin Kebbi.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Idris ya amince da sakin N172.15m domin biyan alawus-alawus na CATA da CONTTA ga kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT na Jami’ar Abdullahi Fodiyo ta Kimiyya da Fasaha, Aliero (AFUSTA).

Ya kuma ce gwamnati ta amince da shigar da CATA da CONTTA cikin tsarin biyan kudin wata-wata na AFUSTA, wanda zai kai kusan N2.066bn a duk shekara. Haka kuma, an amince da biyan N151.52m na bashin karin matakin shekara-shekara ga ma’aikatan jami’ar.

ADVERTISEMENT

A wani bangare, gwamnatin jihar ta raba sabbin motocin bas na Coaster masu kujeru 32 da na’urar sanyaya iska ga manyan makarantu bakwai, domin saukaka zirga-zirgar dalibai. An kashe kusan N1.75bn wajen sayen motocin bas din.Makarantun da suka amfana da motocin sun hada da AFUSTA, Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu, kwalejojin lafiya na Birnin Kebbi da Ambursa, Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jega, Polytechnic ta Jihar Kebbi da ke Dakingari, da Kwalejin Kwarewa kan Shari’a da Nazarin Shari’a ta Yauri.

Haka kuma, Gwamna Nasir Idris ya amince da nadin Dr. Zayyanu Umar a matsayin shugaba na Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie, Argungu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Kwamishinan ya yabawa gwamnatin jihar bisa kokarin inganta harkar ilimi mai zurfi da walwalar ma’aikata, yana mai cewa matakan da aka dauka za su taimaka wajen rage basussukan ma’aikata da inganta ayyukan manyan makarantun jihar.

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Umar Faruk
+ posts Bio
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnan Kebbi Ya Maye Gurbin Mataimakinsa Da Ibrahim Augie A Zaɓen 2027
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Matashi Ya Shiga Hannu Kan Zargin Wulaƙanta Alƙur’ani A Kebbi
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnan Kebbi Ya Miƙa Yara 5 Da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Ga Iyayensu
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Arangama Ta Yi Sanadin Mutuwar ‘Yan Bindiga 17 Da ‘Yansanda 10 A Kebbi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano

Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana'ar Shayi A Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.