Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ware Naira miliyan 300 domin gudanar da bikin auren gata ga ma’aurata 1,500 a jihar.
Gwamnan na ci gaba da al’adar da gwamnatocin da suka gabata a jihar suka assasa, ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen tallafin zamantakewa domin rage wa jama’a wasu matsalolin rayuwa nauyi.
A yayin wani shirin wayar da kan ma’aurata kafin aure da aka gudanar a Gidan Gwamnati ranar Alhamis, Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar, Aminu Daurawa, ya bayyana yadda bikin zai gudana da kuma irin tallafin da kowanne ma’aurata za su samu.
Daurawa ya ce kowace amarya za ta samu Naira 200,000 a matsayin sadaki daga cikin kuɗaɗen da gwamnatin jihar ta ware, kuma za a saka kuɗin kai tsaye cikin asusun bankinta domin tabbatar da gaskiya a fili kuma a bayyane.
Baya ga kuɗi, gwamnatin jihar za ta samar wa ma’auratan kayan ɗaki, tufafi da abinci a matsayin wani ɓangare na tallafin.
Daurawa ya bayyana cewa bikin auren gatan ba zai kasance ba tare da wasu sharuɗɗa da Hukumar Hisbah ta gindaya ba, waɗanda ake sa ran ma’auratan za su bi domin cin gajiyar shirin.














