Kamfanonin Kasashen Waje Suna Amfani Da Sabbin Damammakin Bikin CIFTIS
An rufe bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima ta kasa da kasa CIFTIS na shekara ta 2026 a ranar...
An rufe bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima ta kasa da kasa CIFTIS na shekara ta 2026 a ranar...
A jiya Litinin ne aka bude babban taro karo na 70, na hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA a birnin Vienna dake Austria. Da yake jawabi a yayin taron, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Sin Shan Zhongde, ya ce amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ya shafi jin dadin dukkan bil’adama, wanda hakan ya sa ya fi muhimmanci ga dukkan bangarorin su tsaya tsayin daka kan goyon bayan ra’ayin cudanyar bangarori daban-daban, da kuma kara zurfafa hadin kai tsakanin su. Shan ya kara da cewa, Sin ta dage wajen bunkasa makamashin nukiliya cikin tsari da tsaro, kuma ta daidaita ci gaban da ke da alaka da kirkire-kirkire da tsaro, da kuma gudanar da hadin gwiwa a bude. A nan gaba, Sin za ta mayar da hankali kan muhimman fannoni guda hudu, na farko shi ne daidaita ci gaba, da tsaro don fadada sabbin fannoni, da nufin yin hadin gwiwar makamashin nukiliya. Na biyu kuma, za ta tabbatar da dorewar ci gaba cikin tsaro, don kiyaye tsaron nukiliya na duniya. Na uku kuma, za a bi tsari mai amfanar da mutane, don inganta kimiyya da fasahar nukiliya, ta yadda za su kawo alherai ga jama’a. Kana na karshe, za a aiwatar da manyan tsare-tsare guda hudu na duniya, don inganta tsarin shugabancin duniya. (Safiyah Ma)
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya yi kira ga jami'an 'yan sandan kasar da su ci gaba da dukufa ga...
Yadda Ya KamataKwanan nan, tsohon firayim ministan Jordan Omar Razzaz, ya shaidawa manema labarai na CMG, cewa yanzu haka ana...
An gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS karo na 18 a birnin New Delhi na kasar Indiya daga ranar 12...
Ministan kiwon lafiya na kasar Sin Lei Haichao, ya ce kasarsa za ta ci gaba da matsa kaimin samar da...
A halin yanzu, ana hanzarta yiwa tsarin cinikayyar tattalin arzikin kasa da kasa kwaskwarima, kuma cinikin hada-hadar ba da hidima...
Fasahar kirkirarriyar basira ko AI, a matsayin wata fasaha mai muhimmanci ga makomar dan Adam, tana da tasiri sosai a...
Bikin baje kolin kasa da kasa kan kasuwancin ba da hidimomi na kasar Sin na shekarar 2026 (CIFTIS), wanda ya...
Ranar 12 ga watan Satumba, rana ce ta hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta duniya ta MDD. A ranar bikin...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.