Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Ci Gaba Da Rike Kambin Wuri Mafi ’Yancin Hada-Hadar Tattalin Arziki A Duniya
Yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ya sake zama wuri mafi ’yancin hada-hadar tattalin arziki a duniya, kamar...
Yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ya sake zama wuri mafi ’yancin hada-hadar tattalin arziki a duniya, kamar...
An fara watsa shirin bincike mai sassa uku mai taken “Yadda aka kawar da laifukan zamba ta yanar gizo da wayar salula a arewacin Myanmar”, ta tashar CCTV-1 ta babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na Sin wato CMG a takaice, tun daga ranar 5 zuwa 7 ga watan nan na Oktoba, da karfe 18:00 na yammacin kowace rana. An dauka da tsara wannan shirin ne bisa hadin gwiwar ma'aikatar tsaron jama'ar kasar da CMG, wanda ya nuna cikakken yadda hukumomin tsaron jama'a na Sin tare da hukumomi masu alaka suka gudanar da aikin musamman na yaki da laifuffukan da suka shafi Sin a arewacin Myanmar, da kuma tarihin gwagwarmaya mai wahala, da nasarori a fannin kawar da kungiyoyin aikata laifuka irin su "manyan iyalai hudu" na arewacin Myanmar gaba daya. Shekarar da muke ciki, ita ce shekara ta farko ta aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, “shirin shekaru biyar-biyar da ya shafi bunkasa tsaron jama’a” ya riga ya sanya yaki da magance laifukan zamba ta yanar gizo da waya, cikin manyan ayyukan da aka fi mayar da hankali a kansu. Gwamnatin Sin ta kuma kaddamar da kawancen kasa da kasa mai kunshe da kasashe 46 don yaki da zamba ta yanar gizo da wayar salula. (Bilkisu Xin)
Mataimakin wakilin Sin na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Sun Lei, ya yi jawabin martani ga kasashen yamma a yayin muhawarar gama gari ta Kwamitin na Uku na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a jiya Litinin, inda ya baiwa wasu tsirarrun kasashe shawara da su daina kirkiro da yada labaran karya game da Sin, kuma su daina yin amfani da batun kare hakkin dan Adam don cimma muradun su a bangaren siyasa. Sun Lei, ya bayyana cewa, wakilan Burtaniya, da Ostiraliya, da Japan, da Ireland, da Czech da Lithuania a cikin jawabansu, sun yi zargi marar tushe, da bata suna da gangan ga yanayin kare hakkin dan Adam na Sin, kuma Sin ta nuna rashin jin dadi da adawa mai karfi a kan hakan. Wadannan kasashe da aka ambata suna ganin sun fi kowa, kuma kullum suna nuna kamar su malaman kare hakkin dan Adam ne. Amma matsalolin kare hakkin dan Adam sun yi fice a cikin kasashensu, don haka ba su da cancantar yin magana kan kare hakkin dan Adam kwata-kwata, balle ma su yi wa Sin tsokaci marar tushe. A wannan ranar kuma, Sun Lei ya yi jawabi a karkashin batun “Matakan Kawar da Ta’addanci na Kasa da Kasa”, na Kwamiti na Shida na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana adawa, da mayar da yaki da ta’addanci a matsayin harkar siyasa da kayan aiki. A cewarsa, yayin fuskantar barazanar ta’addanci, babu wata kasa da za ta iya kare kanta ita kadai. Ya ce kasar Sin na cikin sassa da ta’addanci ya shafa, kuma ETIM kungiya ce ta ta’addanci ta kasa da kasa, wadda kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya sanya cikin jerin sunayen kungiyoyin ta’addanci, wadda kuma ta kai hare-haren ta’addanci da dama a cikin kasar Sin. Don haka, Sin na kira ga bangarori daban daban da su dauki matakan da suka dace, kana su hada kai wajen yaki da kuma kawar da ETIM, da sauran kungiyoyin ta’addanci makamantansu. (Bilkisu Xin)
A yayin zama na 63 na majalisar kare hakkin bil’adama ta MDD ko UNHRC, wanda ya gudana a jiya Litinin, an amince da kuduri mai taken “Ingiza samar da damar cin gajiyar hakkin bil’adama ga kowa” wanda kasar Sin ta gabatar a madadin kasashe 47. Cikin jawabinsa na gabatarwa, jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland Jia Guide, ya ce gina yanayi na kyakkyawar dama, muhimmin jigo ne na kiyaye ikon dukkanin rukunonin jama’a, ta yadda za su iya cin gajiyar bai daya mai gamsarwa a harkokin zamantakewa, tare da morewa cikakkun hakkokin bil’adama. A nasu tsokacin kuwa, wakilan kasashen Cuba da Masar, cikin wadanda suka bayyana goyon bayan kudurin, sun jinjinawa kasar Sin bisa aiki tukuru da ta yi wajen ingiza jigon “Samar da dama ga kowa”, tare da dorawa kan inda aka tsaya dangane da batun samar da dama ga kowa. Wakilan sun yi imanin cewa, kudurin na kira da a samar da tallafin kwarewa ga kasashe masu tasowa, da ingiza hadin gwiwar kasa da kasa a fannoni masu nasaba da batun, bisa bukatun kasashe masu tasowa. (Saminu Alhassan)
Alkaluma daga dandamalin sayar da tikitin kallon fina-finai sun nuna cewa, zuwa rana ta 5 ta hutun bikin kafuwar kasar...
Rundunar sojin ’yantar da jama’ar kasar Sin ta PLA da ke yankin kudancin kasar, ta bayyana a yau Litinin cewa,...
Yanayin sayayya a fadin kasar Sin na tafiya yadda ya kamata yayin da aka kai tsakiyar lokacin hutun ranar kafuwar kasar na kwanaki 7, inda alkaluma na farko-farko ke nuna bunkasar da ke bayyana kuzarin da ke tattare da tattalin arzikin kasar. Cikin kwanaki 3 na farkon hutun, daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Oktoba, yawan masu shiga kantuna su yi sayayya ya karu da kaso 3.4, kana kudin shiga a manyan tituna da cibiyoyin sayayya 78 da ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar ke bibiya, ya karu da kaso 5.3, a mizanin shekara-shekara. Haka kuma, shirin gwamnati na bayar da rangwame yayin musayar tsoffin kayayyaki da sabbi, ya samu cinikin yuan biliyan 19.63, kwatankwacin dala biliyan 2.91 a lokacin, inda masu sayayya miliyan 3.48 suka ci gajiya. Hutun bikin ranar kafuwar kasar Sin daya ne daga cikin lokutan da aka fi yin tafiye-tafiye da sayayya da yawon bude. Hukumomi sun yi hasashen za a yi jimillar tafiye-tafiye biliyan 2.13 tsakanin lardunan kasar cikin kwanaki 7, inda matsakaicin na kowace rana zai kai miliyan 300. Alkaluma na baya sun nuna karfin bukatar tafiye-tafiye, inda a ranar 1 ga watan Oktoba kadai, yawan tafiye-tafiyen jiragen kasa ya kai miliyan 25.2, adadi mafi yawa a rana guda. (Fa’iza Mustapha)
Wani shirin hadin gwiwa tsakanin hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO) da dandalin Codemao na kasar Sin, mai koyar da ilimin sarrafa fasahohi ko Coding, na samun nasara wajen shigar da ilimin fasahar AI cikin makarantun da ke fadin nahiyar Afrika. A cewar Mary Nyasimi, kwararriyar mai tsara shiri a ofishin UNESCO da ke gabashin Afrika, AI da fasahohin dijital na sauya tsarin koyo da koyarwa a fadin nahiyar Afrika, inda suke samar wa dalibai muhimman dabarun da za su amfane su a nan gaba a bangarorin sana’o’i da kirkire-kirkire. Shirin na koyar da matasa ilimin sarrafa fasahohi ko Coding, wanda UNESCO da Codemao suka kaddamar a shekara ta 2021, na da nufin samar da ilimin fasahar AI da na Coding, mai aminci bisa daidaito da tafiya tare da kowa, a fadin nahiyar Asiya da Afrika. A cewar jami’ar, tsakanin shekarar 2021 da 2022, sama da malamai 200 daga kasashen Jamhuriyar Congo da Kenya da Namibia da Thailand, da suka hada da kaso 45 na mata, sun kammala shirin UNESCO na kasa da kasa na farko, na karbar horo kan Coding. Ta kara da cewa, shirin na amfani ne da dabarar koyar da mai koyarwa, inda sabbin malamai da aka horar suke koyar da dubban takwarorinsu da dalibai ilimin fasahohin Coding da dijital, a fadin nahiyar. (Fa’iza Mustapha)
Babban jirgin sama samfurin AG600 mai suna Kunlong da Sin ta kera a cikin gida, wanda ke iya tashi da sauka a kan doron kasa da cikin ruwa, ya kammala aikinsa na bana a Jiagedaqi da ke lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin. Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya bayyana a yau Litinin cewa, jirgin ya yi nasarar kammala ayyukan kai daukin gaggawa da na kare gobarar daji, na tsawon watanni 4 a sararin samaniya. Kuma yayin aikin na watanni 4, ya yi tafiye-tafiye domin sintiri sau 35, inda ya kwashe tsawon sa’o’i 100 na tafiya lami lafiya, ya kuma zubo da ruwa kimanin ton 390. Bisa la’akari da yadda yake iya shawagi a kusa da doron kasa kuma ba tare da gudu sosai ba, da karfinsa na daukar ruwa mai yawa da saukin sauya alkibla, jirgin ya nuna karfinsa na kai daukin gaggawa da kashe gobara a dazuka masu sarkakiya. Kasar Sin ce ta kera jirgin na Kunlong da kanta, domin biyan bukatun kasar na kashe gobarar daji da ayyukan ceto a cikin ruwa. Kuma shi ne irinsa mafi girma a duniya da ba na aikin soja ba, idan aka kwatanta da nauyin da yake iya tashi da shi. Nan gaba, jirgin zai shiga matakin aiki na yau da kullum, inda zai taimaka wa wani sabon samfuri mai karewa da kashe gobarar daji. (Fa’iza Mustapha)
Shugaban kasar Mozambique, Daniel Francisco Chapo, ya ce aikin gona yana da matukar muhimmanci ga Mozambique, don haka yana fatan...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.