An Watsa Shirin Bincike Mai Taken “Yadda Aka Kawar Da Laifukan Zamba Ta Yanar Gizo Da Wayar Salula A Arewacin Myanmar” A Tashar CCTV-1 Ta CMG
An fara watsa shirin bincike mai sassa uku mai taken “Yadda aka kawar da laifukan zamba ta yanar gizo da wayar salula a arewacin Myanmar”, ta tashar CCTV-1 ta babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na Sin wato CMG a takaice, tun daga ranar 5 zuwa 7 ga watan nan na Oktoba, da karfe 18:00 na yammacin kowace rana. An dauka da tsara wannan shirin ne bisa hadin gwiwar ma'aikatar tsaron jama'ar kasar da CMG, wanda ya nuna cikakken yadda hukumomin tsaron jama'a na Sin tare da hukumomi masu alaka suka gudanar da aikin musamman na yaki da laifuffukan da suka shafi Sin a arewacin Myanmar, da kuma tarihin gwagwarmaya mai wahala, da nasarori a fannin kawar da kungiyoyin aikata laifuka irin su "manyan iyalai hudu" na arewacin Myanmar gaba daya. Shekarar da muke ciki, ita ce shekara ta farko ta aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, “shirin shekaru biyar-biyar da ya shafi bunkasa tsaron jama’a” ya riga ya sanya yaki da magance laifukan zamba ta yanar gizo da waya, cikin manyan ayyukan da aka fi mayar da hankali a kansu. Gwamnatin Sin ta kuma kaddamar da kawancen kasa da kasa mai kunshe da kasashe 46 don yaki da zamba ta yanar gizo da wayar salula. (Bilkisu Xin)



















