An Kammala Bikin Nune-nune Na Cinikayyar Dijital Na Kasa Da Kasa Karo Na Biyar
A yau Lahadi ne aka kammala bikin nune-nune na cinikayyar dijital na kasa da kasa karo na biyar, a birnin...
A yau Lahadi ne aka kammala bikin nune-nune na cinikayyar dijital na kasa da kasa karo na biyar, a birnin...
A yau Lahadi ne rundunar ‘yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA reshen kudancin kasar, ta gudanar da atisayen hadin gwiwa na dakarun sojojin ruwa da na sama, a kewayen tsibirin Huangyan Dao na yankin tekun kudancin kasar Sin. Wata sanarwa da reshen rundunar ya fitar, ta ce atisayen aiki ne na wajibi da aka gudanar, a matsayin martani ga matakan wasu kasashe na haifar da barazana ga zaman lafiya da daidaito a yankin. Kazalika, sanarwar ta ce atisayen na da nufin yin gwaji, da kuma inganta ikon yaki, domin tabbatar da kare ikon mulkin yankunan Sin da kuma muradu da moriyar teku ta kasar Sin. Har ila yau, sanarwar ta ce kasar Sin na da iko kan tsibiran Nanhai, wadanda suka hada da Dongsha Qundao, da Xisha Qundao, da Zhongsha Qundao, da Nansha Qundao. Kuma bisa tarihi, kasar Sin ce ke da ikon mallakar yankin tekun kudancin kasar. Bugu da kari, kasar Sin na da iko da ruwayen cikin gida, da na yankunan teku, da na yankunan iyaka, da na kebantattun yankunan tattalin arziki, da sassan teku da suka nutse, bisa yanayin yankin tsibiran Nanhai Zhudao. Tuni akasarin sassan kasa da kasa suka amince da tsibiran Nanhai Zhudao, a matsayin halastattun yankin kasar Sin. (Saminu Alhassan)
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gabatar da jawabi yayin babban taron mahawara na MDD na 81, a jiya...
A yau Asabar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayoyi game da batun fasahar kirkirarriyar...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump sun cimma matsaya kan abubuwa guda takwas, kamar yadda...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ziyarar aiki a kasar Amurka daga ranar 23 zuwa 25 ga watan nan. Bayan ziyarar, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda har ila yau shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi tsokaci kan wannan ziyara ta shugaba Xi ga manema labarai. Wang Yi ya ce, shugaba Xi Jinping ya yi wata doguwar tafiya don ziyartar kasar Amurka, ziyarar da ta jawo hankalin duk duniya, wadda ta zama ziyarar aiki da shugaba Xi ya sake yi bayan shekaru 11. Kazalika, Wang Yi ya ce, ziyarar ce ta sa shugabannin kasashen biyu suka cimma nasarar kawo wa juna ziyara cikin rabin shekara, tare da kafa tarihin mu’amalar Sin da Amurka. Bugu da kari, kafafen yada labarun Sin da na kasashen waje sun mayar da hankali sosai kan ziyarar Xi a wannan karo, inda a ganinsu, ta zama ziyarar tarihi mai cike da babbar ma’ana. Yayin da duniya ke fuskantar tashe-tashen hankula, ziyarar ta kara yayata nasarorin da aka samu a yayin ganawar shugabannin biyu a Beijing, da jagorantar samun karin ci gaba wajen raya kyakkyawar dangantakar Sin da Amurka mai gudana bisa daidaiton manyan tsare-tsare, da shaida cewa, Sin da Amurka suna nuna wa juna goyon-baya da zaman jituwa da kuma samun moriya tare, a wani kokari na samar da alfanu ga kasashen biyu gami da duk duniya baki daya.(Murtala Zhang)
A ranar 25 ga watan nan ne, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yayin da yake halartar babban taron MDD a birnin New York na kasar Amurka, tare kuma da halartar babban taron tattaunawa na cika shekaru biyar da gabatar da shawarar raya ci gaban duk fadin duniya (GDI) da kasar Sin ta karbi bakuncinsa, da karanta sakon shugaba Xi Jinping na murnar taron. A ganawarsa da Antonio Guterres, Han Zheng ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 55 da mayar wa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD. A cikin shekaru 55 da suka gabata, har zuwa yanzu, Sin ta tsaya ga bin ra’ayin mu’amalar mabambantan sassa a duniya, da goya wa MDD baya wajen taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar a-zo-a-gani a matsayin wata babbar kasa, da himmatuwa wajen kara hada akidu da shawarwarinta da ajandar MDD, gami da samar wa duniya sabbin damarmaki bisa sabbin nasarorin da ta samu wajen zamanantar da kasa. Antonio Guterres a nasa bangaren kuwa, gode wa kasar Sin ya yi saboda babban goyon-bayan da take bayarwa ga sha’anin MDD, inda ya ce, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba ga muhimmiyar ajandar MDD, tare da bayar da babbar gudummawa ga ci gaban duk duniya baki daya. Har wa yau, a babban taron tattaunawa na cika shekaru biyar da gabatar da shawarar raya ci gaban duk fadin duniya (GDI), mataimakiyar babban sakataren MDD, Amina Mohammed, da firaministan kasar Pakistan, Muhammad Shahbaz Sharif, da mataimakin shugaban kasar Maldives, Hussain Mohamed Latheef, gami da mataimakin firaministan kasar Laos kuma ministan harkokin wajen kasar, Thongsavanh Phomvihane, sun gabatar da jawabai daya bayan daya, kuma manyan jami’ai daga kasashe sama da 30, da wakilai fiye da 300 daga kasashe sama da 60 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 20 su ma suka halarci taron. Bangarori daban-daban sun yaba sosai da muhimmiyar rawar da shawarar raya ci gaban duk fadin duniya ta taka, tun bayan da aka gabatar da ita shekaru biyar da suka wuce har zuwa yanzu, musamman a fannonin da suka shafi samar da ci gaba mai dorewa ga sassan kasa da kasa, da taimaka wa aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030. (Murtala Zhang)
Mataimakin shugaban kasar Sin, Han Zheng, ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Ghana domin aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma ci gaba da raya dadadden zumunci, da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwa a aikace, tare da ci gaba da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Ghana. Han ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, a birnin New York, a gefen taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 81. A nasa bangare, Mahama ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Ghana da Sin tana da tushe mai kwari na tarihi, kuma Ghana tana matukar godiya da kyakkyawan goyon baya da taimakon da Sin take bayarwa cikin shekaru da dama. Mahama ya bayyana cewa, a kodayaushe Ghana tana bin manufar "kasar Sin daya tak a duniya" sau-da-kafa, kuma tana fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni irin su cinikayya, da zuba jari, da hakar ma'adanai da ayyukan masana'antu, tare da inganta musaya a tsakanin al'ummomin kasashen biyu domin ci gaba da habaka dangantakar da ke tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Gwamnan babban bankin kasar Ghana, Johnson Asiama, ya bayyana cewa, mahukuntan kasar za su yi aiki tare da takwarorinsu na kasar Sin domin kawar da tsarin amfani da kudin wata kasa ta daban wajen biyan kudin cinikayya tsakanin 'yan kasuwar Ghana da masu samar da kayayyaki na kasar Sin. A yayin taron manema labarai na baya-bayan nan da kwamitin manufofin kudi na kasar ya gabatar da yammacin ranar Alhamis da ta gabata, Asiama ya ce, sauya tsarin, wanda zai kawo karshen biyan kudi ta hanyar amfani da kudin wata kasa ta daban ya zama wajibi don inganta cinikayyar Ghana da Sin, yayin da 'yan kasuwa na kasar ke kokarin cin gajiyar manufar soke biyan harajin kwastam da gwamnatin Sin ta samar ga kasashen Afirka 53 da ke da huldar diflomasiyya da ita. A cewar gwamnan babban bankin dai, kasar ta yammacin Afirka na daukar matakan kirkiro da tsarin biyan kudade kai-tsaye tsakanin kudin Ghana (Cedi) da na kasar Sin (RMB); kasancewar amfani da kudin wata kasa ta daban yana haifar da tsarin canza kudin waje sau biyu, lamarin da ke sanya 'yan kasuwa biyan kudin canji sau biyu maimakon sau daya. Kazalika, gwamnan ya bayyana kasar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar kasuwanci ga kasar tasu da ke Yammacin Afirka, inda ya kara da cewa babban bankin Ghana zai ci gaba da yin mu'amala da kasar ta Sin kan batutuwa daban-daban da suka shafi muradun kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron manyan jami’ai albarkacin cika shekaru 5 da gabatar da Shawarar Ci Gaban Duniya (GDI), wanda aka yi a hedkwatar MDD da ke New York a Juma’a. Shugaban ya ce, shekaru 5 ke nan da ya gabatar da shawarar GDI ga babban zauren MDD domin inganta hadin gwiwa wajen samar da ci gaba a duniya, da karfafa kokarin duniya na samun ci gaba da taimakawa wajen gaggauta aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030. Ya ce cikin sama da shekaru 5, an aiwatar da shawarar sosai bisa hadin gwiwar dukkan bangarori, inda ayyukan hadin gwiwa da aka yi karkashin shawarar suka samu wurin zama da kyawawan sakamako a kasashe sama da 20, tare da rubuta sabon babin ci gaba na bai daya da hadin gwiwar moriyar juna. A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma kuma mamba cikin rukunin kasashe masu tasowa, kasar Sin a shirye take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen daukaka falsafar ci gaba mai sanya mutane a gaba da komai da daukaka shawarar GDI da tabbatar da burikan ci gaba masu dorewa sun zama na zahiri da bayar da sabbin, kuma manyan gudunumuwa wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama. (Fa’iza Mustapha)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.