Xi Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Matakan Gina Sin Mai Zaman Lafiya Da Nufin Tabbatar Da Zamanantar Da Kasar
A baya-bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin umarni, dangane da aiwatar da matakan samar...
A baya-bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin umarni, dangane da aiwatar da matakan samar...
Idan ana son ambatar sunayen kasashen da ke neman tabbatar da ci gaban kasashe daban daban na bai daya a duniya, to, ba za a rasa kasar Sin ba. Shugaban kasar, Xi Jinping, ya jaddada sau da dama cewa, “Ba zai yiwu a samu walwalar duniya da kwanciyar hankali bisa tushen mai kudi na kara samun kudi, yayin da mara kudi ke kara faduwa cikin kangin talauci ba.” Don daidaita yanayin rashin ci gaba dake damun dimbin kasashe, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya ta Global Development Initiative (GDI) shekaru 5 da suka gabata. Kana a kwanan baya, shugaban ya aika da sako ga taron manyan jami’ai kan cika shekaru 5 da gabatar da shawarar GDI da ya gudana a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, inda ya sake nanata cewa, ci gaban tattalin arziki tushe ne na jin dadin rayuwar jama’a. Shawarar GDI ta kunshi bayanai masu nasaba da fannoni 6, wato dora matukar muhimmanci kan neman ci gaban tattalin arziki, da kokarin inganta rayuwar jama’a, da rage gibin dake tsakanin kasashe masu tasowa da masu sukuni, da amfani da fasahohin zamani don amfanar da al’ummun kasashe daban daban, da sauya salon tattalin arziki zuwa mai kare muhalli, da kokarin aiwatar da nagartattun manufofin da aka tsara. Cikin shekaru 5 da suka wuce, shawarar GDI ta samu karbuwa sosai a duniya. Zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 130 sun goyi bayan shawarar, kana kasashe kusan 100 sun kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa tare da kasar Sin. Kana a bisa tsare-tsare masu alaka da shawarar, an ware kudin da yawansa ya kai fiye da dala biliyan 23, wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa masu amfanar da jama’a fiye da 1800, da horar da mutane masu neman koyon fasahohi fiye da dubu 200, da taimaka wa yunkurin raya tattalin arziki a kasashe fiye da 120. A kasar Najeriya ma ana iya ganin amfanin shawarar GDI. Wani bayanin da jaridar The Guardian ta kasar Najeriya ta watsa a kwanan baya ya ambata cewa, kasar Sin ta aiwatar da ayyuka da dama masu amfanawa jama’a a Najeriya, misali haka rijiyoyi, da kafa dakunan karatu da ake koyar da fasahohin dijital, da yayata fasahar noman shinkafar da aka tagwaita irinta, da samar da tallafin na’urorin da ake bukata a asibitoci, da dai sauransu. Kana a cikin ayyukan, aikin gina gandun noman laimar kwado ya janyo hankali sosai, har ma ma’aikatar aikin gona ta kasar Najeriya ta bayyana shi a matsayin nasarar da aka samu a fannin kokarin neman samun isasshen abinci. Kasar Sin ta nuna wa duniya ra’ayinta na tabbatar da ci gaban kasashe daban daban, ta hanyar gabatar da shawarar GDI shekaru 5 da suka wuce, wadda ta yi matukar kokarin aiwatarwa daga bisani. Hakan ya shaida cewa, kasar Sin aminiya ce ga duk wata kasa dake neman raya tattalin arzikinta. (Bello Wang)
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu jami’an JKS, da shugabannin gwamnati, za su aza kwandunan furannin karrama ‘yan mazan...
Ofishin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da sashen kula da harkokin hadin kan jam’iyyu da kungiyoyi na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin, da ofishin kula da harkokin ‘yan kasashen waje ‘yan asalin kasar Sin na majalisar gudanarwar kasar Sin, da ofishin kula da harkokin yankin Hong Kong, da yankin Macau na majalisar gudanarwar kasar Sin, da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, da kuma kungiyar hadin gwiwar ‘yan kasashen waje ‘yan asalin kasar Sin ta kasar Sin, sun gudanar da bikin murnar ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, a yau Litinin 28 ga wata, don murnar cika shekaru 77 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. Zaunannen memban hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa, ya kamata a bi tunanin shugaba Xi Jinping, game da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, da kiyaye yin hadin gwiwa tare da bangarori daban daban, da rike tutar ra’ayin kaunar kasa, da tabbatar da raya hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban masu kaunar kasar Sin, da sa kaimi ga hada kan Sinawa a ciki da waje, don raya kasar Sin ta zamani mai tsarin gurguzu, da cimma burin farfadowar al’ummar kasar Sin baki daya. (Zainab Zhang)
A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce a ranar Juma’a 25 ga watan nan, aka gudanar da babbar tattaunawar jami’ai, ta murnar cika shekaru 5 da aka gabatar da shawarar inganta ci gaban duniya GDI a hedkwatar MDD dake birnin New York. Guo, ya ce cikin sakonsa na taya murnar taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce an gabatar da shawarar GDI ne da nufin ingiza hadin gwiwar bunkasa ci gaban duniya, da kara karsashi a turbar bunkasa duniya, da taimakawa wajen gaggauta aiwatar da muradun ci gaba mai dorewa na MDD na nan zuwa shekarar 2030. Guo, ya kara da cewa irin muhimman matakai, da nasarorin da aka cimma daga shawarar GDI cikin shekaru 5 da suka gabata, sun isa shaida game da aniyar kasar Sin ta ingiza ci gaban bil Adama, da zaman jituwa a duniya, da ma yadda kasar ke kara azamar gabatar da dabarun warware matsaloli, wanda hakan ya mayar da Sin babbar mai samar da gudunmawar ingiza ci gaban bai daya ga dukkanin kasashe. Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin sassa, wajen ci gaba da sauya ajandar SDGs zuwa matakai na hakika, da ingiza manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama. (Saminu Alhassan)
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce ribar da manyan kamfanoni masu masana’antu na kasar suka samu cikin watanni 8...
A lokacin kaka na bana, shugabannin Sin da Amurka sun sake ganawa da juna, kuma wannan batu ya yi matukar jawo hankalin sassan kasa da kasa. Bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Amurka, tun daga ranar 23 zuwa 25 ga wannan wata. A yayin ziyarar, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi mai zurfi kan batutuwan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da manyan tsare-tsare kan yanayin duniya, da manyan batutuwan dake shafar kasa da kasa, kuma sun cimma matsaya kan abubuwa guda takwas, inda shugabannin biyu suka amince su gina dangantaka mai ma’ana, bisa manyan tsare-tsare cikin kwanciyar hankali a tsakanin Sin da Amurka, wacce ke da tushen girmama juna, da adalci da kuma zaman daidai wa daida, wanda hakan ya shata taswira madaidaiciya, game da yadda za a raya dangantaka tsakanin kasashen biyu. Girmama juna yana nufin kasashen biyu su girmama ikon mallakar kasashensu, da cikakkun yankunan kasa, da tsarin zamantakewar al’umma, da moriyarsu da manyan batutuwan da suke baiwa muhimmanci. Adalci yana nufin kasashen biyu su yi hadin gwiwar cimma moriyar juna, da daidaita matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari, da yin watsi da ra’ayin takara a tsakanin kasa da kasa, mai haifar da riba ga wasu da tarin asara ga saura, da kuma yin watsi da neman fifiko daga bangare daya. Matsayin daidaito yana nufin kiyaye matsayin kasashen biyu na daidaito, da rashin nuna fifiko kan saura, da yin watsi da manufar kama-karya, da daidaita batutuwan da suke nuna damuwa a kai daidai wa daida, da nuna daidaito kan hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. Game da hakan, shugaban kwalejin nazarin batutuwan kasa da kasa, kuma direktan cibiyar nazarin harkokin Amurka na jami’ar Fudan ta kasar Sin Wu Xinbo, ya yi nuni da cewa, a watan Mayun shekarar bana shugaba Xi Jinping ya gabatar da sabuwar taswirar raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, wato kiyaye fannoni hudu, a wannan karo kuma, bangarorin biyu sun yi amfani da kalmomi uku don kara fayyace sabuwar ma’anar raya dangantakar dake tsakanin kasashan biyu, kuma shugabannin kasashen biyu sun gabatar da taswirar raya dangantakar kasashen ta dogon lokaci yadda ya kamata. (Zainab Zhang)
Jirgin saman dakon kayayyaki na kamfanin FedEx dauke da manyan dabbar Panda guda biyu, wato Ping Ping da Fu Shuang, ya sauka a birnin Atlanta na kudu maso gabashin kasar Amurka da safiyar Lahadin nan. Pandan guda biyu, za su kasance a gidan adana namun daji na Atlanta har tsawon shekaru 10, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin yarjejeniyar da aka kulla, tsakanin gidan zoo na Atlanta da kuma kungiyar kare namun daji ta kasar Sin. Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya samu rahotannin isar likitocin dabbobi da masu kula da dabbar Panda na Sin birnin Atlanta, gabanin isar Pandan guda biyu, da nufin karbarsu, da taimakawa wajen kula da su yayin da suke a kebe, kana da ba su horo, da daidaita yanayin rayuwarsu a sabon muhalli. A ranar Alhamis, mataimakiyar shugaban lura da ayyukan tattarawa, da kare dabbobi na gidan adana namun daji na birnin Atlanta Gina Ferrie, ta ce suna cikin mararin sake dawowar dabbar Panda gidan Zoo na Atlanta bayan kusan shekaru biyu. Ferrie, ta shaidawa Xinhua cewa, "Mun jima muna shirin karbar bakuncin Ping Ping da Fu Shuang. Mun samar da karin abubuwan da za su bukata a muhallinsu, ciki har da sabbin dakuna masu fadi, da yanayin samun karin haske a waje da doron kasa, da sauran yanayi da zai ba su damar yin kyakkyawar rayuwa." Ping Ping, namijin Pandan an haife shi ne a ranar 17 ga watan Maris na shekara 2020, yayin da macen mai suna Fu Shuang, aka haife ta a ranar 18 ga watan Oktoban shekarar 2020, sun kuma tashi ta filin jirgin saman kasa da kasa na Shuangliu dake birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin, zuwa gidan adana dabbobi na birnin Atlanta dake Amurka da sanyin safiyar Lahadin nan. (Saminu Alhassan)
A yau Lahadi ne aka kammala bikin nune-nune na cinikayyar dijital na kasa da kasa karo na biyar, a birnin...
A yau Lahadi ne rundunar ‘yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA reshen kudancin kasar, ta gudanar da atisayen hadin gwiwa na dakarun sojojin ruwa da na sama, a kewayen tsibirin Huangyan Dao na yankin tekun kudancin kasar Sin. Wata sanarwa da reshen rundunar ya fitar, ta ce atisayen aiki ne na wajibi da aka gudanar, a matsayin martani ga matakan wasu kasashe na haifar da barazana ga zaman lafiya da daidaito a yankin. Kazalika, sanarwar ta ce atisayen na da nufin yin gwaji, da kuma inganta ikon yaki, domin tabbatar da kare ikon mulkin yankunan Sin da kuma muradu da moriyar teku ta kasar Sin. Har ila yau, sanarwar ta ce kasar Sin na da iko kan tsibiran Nanhai, wadanda suka hada da Dongsha Qundao, da Xisha Qundao, da Zhongsha Qundao, da Nansha Qundao. Kuma bisa tarihi, kasar Sin ce ke da ikon mallakar yankin tekun kudancin kasar. Bugu da kari, kasar Sin na da iko da ruwayen cikin gida, da na yankunan teku, da na yankunan iyaka, da na kebantattun yankunan tattalin arziki, da sassan teku da suka nutse, bisa yanayin yankin tsibiran Nanhai Zhudao. Tuni akasarin sassan kasa da kasa suka amince da tsibiran Nanhai Zhudao, a matsayin halastattun yankin kasar Sin. (Saminu Alhassan)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.