Bari Mu Leka Yadda Fasahar Sin Ke Taimakawa Wajen Inganta Gasar Cin Kofin Afirka
Saura kasa da shekara guda a bude gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka karo na 6 na shekarar 2027. Masu karbar bakuncin gasar wato kasashe 3 dake gabashin Afirka—Kenya, Uganda da Tanzania—suna iyakacin kokari a mataki na karshe don share fagen wannan babbar gasar kwallon kafa ta Afirka. Ma’aikatan kasar Sin dake ba da taimako wajen gina manyan ababen bukatu na gasar sun zama ginshigai wajen inganta wannan gasa dake tafe. A Kenya, filin wasa na Talanta da kamfanonin Sin ke gudanar da gininsa, zai iya daukar mutane dubu 60, kuma daya ne daga cikin manyan filayen wasa na gudanar da gasar cin kofin Afirka na 2027. Aikin ya yi amfani da fasahar rufi da ake kira a Turance da “Cable domes”, wato amfani da wasu turaku masu inganci a saman rufin ginin, fasaha ce dake sahun gaba a duniya, kuma a karon farko ake amfani da ita a nahiyar Afirka, tamkar yadda aka yi a babban filin wasa na gasar cin kofin duniya na Qatar. Aikin dai na bukatar fasaha da ma’aikata masu matukar kwarewa. Don haka, kamfanonin Sin dake kula da wannan aiki ya bude cibiyar horaswa don bayar da ingantaccen horo bisa wannan aiki ga ma’aikatan kasar ta Kenya. A wasu lokuta, dubban ma’aikata na Sin da Kenya sun yi aiki tare ba rana ba dare. Shugaban Kenya William Samoei Ruto ya sha ziyartar wurin da ake gudanar da aiki, tare da yabawa yadda yake gudana, yana mai bayyana shi da “ Abun alfaharin kasar Kenya”. Bugu da kari, domin tabbatar da nasarar gasar ta cin kofin Afirka na 2027, kamfanin Sin dake ba da taimakon gina filin wasan zai hada hannu da kamfanin Kenya mai gudanar da harkokin gasar don kafa wata tawaga ta musamman ta gudanarwa, don horar da ma’aikatan kwararru a cikin gidan Kenya, wadanda za su iya sarrafa na’urori, da injina masu sarkakiya, da kula da filin ciyayi na musamman, da amfani da tsarin tsaro na fasaha, domin ba da tabbaci ga gasar cikin kwanciyar hankali. Ban da wannan kuma, wannan tawagar kwararru za ta iya taka rawar gani a nan gaba a bangaren gudanarwa bayan gasar a kasar Kenya. Matakin da kamfanin Sin ke dauka na dace sosai da taken “Shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka” na shekarar 2026. Wasanni hanya ce mafi dacewa ta musayar al’adu, kuma filin wasa ba wurin fafatawa kawai ba ne, har ma dandali ne da matasan Afirka ke cika burinsu, kana cibiyar horaswa ba wai kawai tana ba da taimakon fasaha ga aikin ba ne, har ma dandali ne na kara karfin kwarewar ma’aikatan Kenya da kara samun aikin yi. Kafa tawagar kwararrun gudanarwa ba wai kawai za ta samar da hidima ga gasar cin kofin Afirka da ke tafe ba ne, har ma za ta baiwa Kenya kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyuka a nan gaba. Hadin gwiwar Sin da Afirka na gudana daga “Ayyukan da ake gudanarwa” zuwa “Hadin gwiwar da za a iya ji da cin gajiyarsa”. Gasar cin kofin Afirka ta 2027, dandali ne na Afirka, kuma taga ce ta fahimtar hadin gwiwar Sin da Afirka. Lokacin da masu sha’awar gasanni suka shiga filin wasa cikin farin ciki, abin da kafafunsu za su taka shi ne filin wasa da Sin ta gina bisa fasaharta. Daga ginin filin wasa zuwa horar da ma’aikata, daga warware matsalolin fasaha zuwa kula da filin ciyayi da amfani da tsarin tsaro, fasahar Sin na ba da kariya da inganta gasar cin kofin Afirka, wannan ba wai tabbatar da babbar gasa kadai ba ne, har ma ya kunshi hakikanin matakin da Sin ke dauka na tabbatar da hadin gwiwar Sin da Afirka, wato daga “Gina ababen more rayuwa” zuwa “Gina kwarewa cikin hadin gwiwa”. (Marubuciya: MINA)



















