Kasar Sin Ta Bukaci A Kawo Karshen Daukar Matakan Matsi Na Kashin Kai
Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya gabatar da wani jawabi na hadin gwiwa a madadin kasashe mambobi 28 a kwamiti na 3 na babban zauren MDD jiya Alhamis, inda ya yi kira ga kasashen duniya su nace wajen adawa, tare da kawo karshen daukar matakan matsi ko takunkumai na kashin kai. Ya ce duniya a yanzu na fama da matsalar kakaba takunkumai da daukar matakai na kashin kai, yana nanata cewa tarihi ya riga ya nuna cewa irin wadannan matakai da wani bangare guda ke dauka, su ne manyan abubuwan da ke haddasa rikici a duniya. A cewar Fu Cong, kasashe masu tasowa da al’ummunsu na ci gaba da fama da radadin irin wadannan matakai, wadanda ke take ka’idojin da suka hada da cikakken ‘yanci da daidaito da hadin gwiwa, da yin katsalandan cikin harkokin cikin gidan kasashe da saba wa muradu da ka’idojin kundin tsarin mulki na MDD da kuma tarnaki ga tsarin cudanyar bangarori da dama, da ma dokokin kasa da kasa. Kasashen 28 sun nanata adawarsu ga takunkumai daga bangare guda, tare da yin kira ga kasashen yamma ‘yan tsiraru, da su saurari kiran kasa da kasa na neman tabbatuwar adalci da daukaka kudurinsu na biyayya ga kundin tsarin mulkin MDD da dokokin kasa da kasa, kuma su gaggauta soke dukkan takunkuman da suka yi gaban kansu wajen kakabawa ba tare da gindaya wani sharadi ba. (Fa’iza Mustapha)



















