Tsohon ɗan takarar majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Dala, Hon. Ambasada Abdurrahman Mansir “Mainasara Salga”, ya bayyana cewa zai jagoranci gwagwarmayar ƙwato haƙƙin duk ƴan takarar da jam’iyyar ADC ta zalunta ta hanyar cire sunayensu bayan sun yi nasara a zaɓen fid da gwani.
Salga wanda ya samu ƙuri’a sama da dubu 8 a zaɓen fid da gwani na Dala, ya ce duk da nasarar da ya samu, jam’iyyar ta sauya sunansa tare da na wasu ta tura wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Ya ɗora alhakin rikicin da ke cikin ADC na Jihar Kano ga Hajiya Naja’atu, inda ya ce ita ce ke yin ɗauki-ɗora da kawo saɓani a jam’iyyar.
A cewarsa iIta ba wata zaƙaƙurar ƴar siyasa ba ce da ta taɓa yin gwagwarmayar samun nasara. Ya ce yanzu ta samu dama tana raba kan ƴan jam’iyya.
Ya kuma bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga rigima tsakanin Naja’atu da shugaban ADC na Kano, Hon. Musa Ungogo da Dakta Aƙilu Indabawa kan rabon muƙamai.
“Ni ba zan taɓa rabuwa da Hon. Musa Ungogo ba. Shi ne halastaccen shugaban ADC na Jihar Kano. Jam’iyyar tana hannunsa,”ya jaddada.
Salga ya ce Malam Ibrahim Khalil ne ya yi nasara a zaɓen fid da gwani na ADC, ba Ibrahim Little ba. Ya zargi Little da haɗa kai da Naja’atu wajen haifar da matsaloli aa jam’iyyar.














