Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya nuna damuwarsa kan yadda wasu suka duƙufa wajen yaɗa labaran ƙarya da ke cewa ya rasu.
Yuguda ya ce tabbas yana rage kuma cikin koshin lafiya, inda ya nuna cewa jama’a da dama sun yi ta buga masa saya domin jin gaskiyar abin da aka yaɗa.
Yuguda guda a wani hira da aka yi da shi a ranar Asabar, ya tabbatar wa duniya cewa lafiyarsa lau a yanzu amma a kwanakin baya can an masa aiki sakamakon ciwon kasusuwarsa na baya.
A ranar Juma’a ne dai wasu suka yi ta haɗawa a kafafen sadarwar zamani labarin cewa Yuguda ya rasu, lamarin da ya tada hankalin mutane da dama a jihar Bauchi.
Da yake ƙaryata batun da kansa Malam Isa ya ce, “Ina raye. Na tabbatar maka jiki da jini wata rana mutum zai iya yin rashin lafiya. A kwanakin baya na yi rashin lafiya. Tabbas kuma ranka yana hannun Allah ko wani irin ciwo ƙarami ko babba Allah zai ya ɗaukan ranka a kowani lokaci.
“Amma na tabbatar maka lafiyata lau. A kwanakin baya na yi rashin lafiya amma yanzu Allah ya ba ni lafiya,” ya tabbatar.
Yuguda ya ƙara da cewa a halin da ake ciki ma yana gida ne domin samun hutu kamar yadda likitoci suka buƙata.
“Yanzu yawanci ina gida ne domin bayan an min aiki a bayana aka ce na huta. Da yake girma ya zo ana iya samun ƙasusuwarmu na baya sakamakon tsabaragen yawan zama sun yi ta gogan juna in ba a yi nasara ba to zai iya zama ajalinka ko kuma ka zama paralysis (shanyewar ɓarin jiki) ya zama baka iya tafiya ba ka iya tashi daga kugunka har kasa.”
Yuguda ya ce yana godiya wa Allah domin a yanzu lafiyarsa kalau da ransa.
“Maganar jita-jitar nan na tabbatar ni bani da makiyi a duniyar nan amma akwai su kam. Ba yadda za ka ce baka da maƙiya to amma ni na ɗauka a rayuwarta bana da Maƙiyi domin ina tabbatar maka ban taɓa kwana da kowa a zuciyata ba.
“Kuma duk wanda ya ce yana gaba da ni, yana gaba da kansa ne, saboda ni bana da lokacin gaba da wani. Kullum ina rokon Allah, Allah sa na cika da imani na gama da duniya lafiya. Bana faɗa da kowa.”
“Ina godiya wa Allah da raina da lafiya na kuma ina tare da masoya na. Da yawan mutanen Bauchi sun fi mutum dubu 10 da suke ta kirani don jin gaskiyar lamarin hakan ya sa dole sai na kashe wayana, ai wannan shine za ka ce ka gode wa Allah hakan na nuna ka bar baya mai kyau kenan.
“Saboda haka ina tabbatar wa masoyana Musulmai da Kirista a faɗin kasar Nijeriya musamman jihar Bauchi bisa yadda suka yi ta damuwa da labarin da suka ji da yadda suka damu da jin labarin na karya.”
“Mutanen Bauchi sun yi gungu da dama wasu ma na kuka har sai da suka ji murya na suka yarda ina raye, na gode Allah saka da alkairi,” ya shaida.














