ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babban Magatakardan Kungiyar SCO: Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Na Da Matukar Ma’ana

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 week ago
SCO

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Daga ranar 31 ga watan Agustan da muke ciki zuwa ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, za a gudanar da taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a kasar Kyrgyzstan. Kafin kaddamar da taron, wakilin CMG ya yi hira da babban magatakardan kungiyar, Nurlan Yermekbayev, wanda ya bayyana cewa, shawarar inganta jagorancin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar tana da matukar ma’ana.

A cewar mista Yermekbayev, an jaddada bukatar samun daidaito tsakanin al’ummun duniya, da dora muhimmanci kan moriyar dan Adam, a cikin shawarar inganta jagorancin duniya. Kana a nata bangare, kungiyar SCO tana tsayawa kan yayata ra’ayin neman daidaito, da tattaunawa maimakon ja-in-ja, da girmama juna, da yarda da kasancewar mabambantan al’adu a duniya, da kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai daya.

Ban da haka, mista Yermekbayev ya ambaci wata sanarwar da kungiyar SCO ta gabatar a watan Yulin bana, inda ya ce, dukkan mambobin kungiyar sun cimma matsaya daya ta adawa da matakin takunkumi na kashin kai, wanda ya zama keta kundin tsarin Majalissar Dinkin Duniya da ka’idojin kasa da kasa, da saba wa burin dan Adam na neman ci gaba mai dorewa. A cewarsa, yayin da ake tafiyar da al’amuran duniya, bai kamata a amince da matsawa wani lamba, da nuna fin karfi, da bayar da umarni ba. Maimakon haka, ya kamata a yi shawarwari, da daukar matakai na diflomasiyya da siyasa.Haka zalika, mista Yermekbayev ya yi tsokaci kan ci gaban da aka samu bisa hadin gwiwar mambobin kungiyar SCO. Ya ce, darajar cinikin da ake yi tsakaninsu na ta karuwa, inda jimillar ciniki ta shekarar da muke ciki ta riga ta zarce dala biliyan 700. Ban da haka, ana ta samun karuwa a fannonin zirga-zirgar mutane tsakanin mambobin kungiyar SCO, da adadin jigilar kayayyaki, da zuba jari, da amfani da kudin kasashen wajen gudanar da ciniki a tsakaninsu. (Bello Wang)

ADVERTISEMENT
SCO
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
SCO
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Masu Binciken Sin Sun Kammala Gwajin Sadarwa Tsakanin Duniyar Dan Adam Da Ta Wata Ta Amfani Da Fasahar Laser

Masu Binciken Sin Sun Kammala Gwajin Sadarwa Tsakanin Duniyar Dan Adam Da Ta Wata Ta Amfani Da Fasahar Laser

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci