Masu bincike na kasar Sin sun kammala gwajin sadarwa tsakanin duniyar dan Adam da duniyar wata, inda suka yi nasarar tabbatar da karfin sadarwa na jeka-ka-dawo ta fasahar Laser a cikin sararin samaniya.
Cibiyar fasaha da injiniya ta binciken sararin samaniya ta cibiyar kimiyya ta Sin ce ta sanar da hakan jiya Juma’a.Bayan shafe sama da shekara guda ana gwajin fasahar yayin da take kewaye sararin samaniya, tawagar masu binciken ta kafa wani tsarin sadarwa na jeka-ka-dawo ta fasahar Laser tsakanin tazarar sama da kilomita 400,000, wanda ya alamta fadada sadarwar fasahar Laser ta Sin daga da’irar kusa da duniyar dan Adam zuwa sararin samaniya mai nisa.
Idan aka kwatanta da sadarwa ta gargajiya ta mita mai gajeren zango, sadarwa ta fasahar Laser ta fi sauri da karfin daukar bayanai masu yawa da karfin tsaro da karin kananan na’urori.
A cewar cibiyar CSU, bisa amfani da kumbon bincike duniyar wata mai dauke da mutane da kuma kafa cibiyar binciken duniyar wata, a nan gaba, bincike a duniyar watan zai samar da adadi mai yawa na hotuna da bayanan kimiyya da tsarin sadarwa na gargajiya ba zai iya ba. Haka kuma, wannan tsarin samar da bayanai ta fasahar Laser tsakanin duniyar dan Adam da duniyar wata, za ta samar da sabuwar hanyar bayar da bayanai mai sauri ga ayyukan binciken wata da za a gudanar a nan gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














