Shugaban Majalisar Malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya ce ba ya nadamar goyon bayan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa waɗanda dukkansu Musulmai ne ba.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Sheikh Jingir, ya ce ya daɗe a kan wannan matsayi tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce goyon bayansa ba ya taƙaita ga Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ba, domin zai goyi bayan duk wani ɗan siyasa da ya yi imani da kare muradun Musulmi a Nijeriya.
Malamin ya ce yana da ’yancin bai wa Musulman Nijeriya shawara kan wanda za su zaɓa, kamar yadda Kiristoci ma suke da ’yancin bayyana ra’ayinsu.
Sheikh Jingir ya kuma ce ya san tun farko cewa kalamansa za su fuskanci tarbaƙi, amma hakan ba zai sa ya daina bayyana abin da ya yi imani da shi ba.
A ranar Asabar a Kano, malamin ya sake bayyana goyon bayansa ga takarar Musulmi da Musulmi, lamarin da ya jawo muhawara a sassan ƙasar.
Sai dai Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Nijeriya ta yi Allah-wadai da wasu kalaman Sheikh Jingir, tana mai cewa za su iya rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna tsakanin addinai.
Hukumar ta kuma buƙaci ’yansanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su binciki tare da gurfanar da shi kan zargin furta kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a.














