Tawagar matar ɗan takarar gwamnan Jihar Nasarawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hajiya Maryam Aliyu Ahmad Wadada, ta tsallake rijiya da baya bayan wasu matasa suka kai mata hari a Lafia.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, 9 ga watan Agusta, a yankin tsakanin Kasuwar Kwaro da Titin Sama a cikin birnin Lafia.
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda tawagar ta yi ƙoƙarin barin wurin cikin gaggawa yayin da wasu matasa ke ihu, jifan motoci da duwatsu.
Rahotanni sun ce Hajiya Maryam tana dawowa ne daga fadar Sarkin Lafia, inda ta je gaisuwa, lokacin da lamarin ya faru.
An ce kafin rikicin ya auku, tawagar tsohon ɗan takarar gwamnan jihar, Muhammad Abubakar Adamu, tsohon Sufeto-Janar na ’yansandan Nijeriya, tana taro a Kasuwar Kwaro.
Majiyoyi sun ce yayin da tawagar Hajiya Maryam ta wuce a karo na farko, babu wata hatsaniya.
Sai dai yayin dawowarta, yawan matasa da magoya baya ya ƙaru, lamarin da ya haifar da rikici.
Jami’an tsaro da ke tare da tawagar sun yi ƙoƙarin daƙile matasan tare da taimaka wa tawagar ta bar wurin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da musabbabin lamarin ko samun labarin jin raunuka ko asarar dukiya.
Haka kuma, ɓangarorin da abin ya shafa ba su yi magana kan lamarin ba.














