ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Barkewar Cutar Sankarau Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Jihar Sokoto

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Sankarau

Mazauna Kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto sun bayyana fargaba kan barkewar cutar sankarau da ake zargin ta hallaka mutane da dama, galibi yara da matasa.

A cewar rahoton Daily Trust, majiyoyi daga cibiyar lafiya ta kauyen sun ce lamarin ya tsananta a ‘yan kwanakin nan, inda ake samun mutuwar mutane kimanin biyu zuwa uku a kowace rana, musamman wadanda shekarunsu ke tsakanin biyu zuwa 20.

Barkewar cutar ta haifar da firgici a cikin al’umma, yayin da mutane ke ta tururuwar zuwa asibiti suna neman magani kan abin da suka kira “cutar da ba a sani ba”.

ADVERTISEMENT

Wani ma’aikacin lafiya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce cibiyar lafiya ta cika makil da marasa lafiya.

“Mutane na zuwa asibiti da yawa kowace rana domin neman magani. Mun cika sosai kuma ba mu san ainihin cutar da ke kashe mana mutane kusan kullum ba,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

Bayanan sun nuna cewa yawancin wadanda suka kamu da cutar sun mutu kafin a yi cikakken gwaji. Daga baya an shawarci mazauna yankin da su guji kwana a cikin dakuna a kulle saboda tsananin zafi da ake ganin na taimakawa wajen yaduwar cutar.

Mazauna yankin sun bayyana alamomi kamar suma, tsananin ciwon wuya, amai, gudawa, zazzabi mai tsanani, da kuma kumfa a baki a wasu lokuta, alamomin da suka yi kama da na cutar sankarau.

Wani mazaunin yankin ya bayyana yadda cutar ke saurin tsananta:

“A wasu lokuta, yaro zai fara korafin ciwon wuya kafin daga bisani ya suma.”

Duk da matakan jinya na farko, mazauna yankin sun nuna damuwa cewa cutar na ci gaba da yaduwa, wanda ya sa wasu ke zargin ko ba sankarau ba ce kawai.

“An gaya mana cewa sankarau ce, amma cutar ba ta tsaya ba. Shi ya sa mutane ke fara zargin ko wata cuta ce daban,” in ji su.

Sai dai wani jami’in asibiti ya ce mutuwar mutane uku kacal aka tabbatar a cibiyar, yana mai cewa yawancin wadanda suka mutu sun rasu ne a gida. Ya kara da cewa yawancin marasa lafiyar na mutuwa cikin awanni 24 bayan fara alamun cutar.

Dagacin Kauyen, Mudassir Abdullahi Kurawa, ya tabbatar da barkewar cutar, inda ya ce an samu mutuwar mutane tsakanin 10 zuwa 15 a cikin al’umma kadai, ba tare da hada da kauyukan da ke makotaka ba.

Ya ce yawancin wadanda suka kamu yara ne masu shekaru tsakanin biyu zuwa 10, kuma alamun cutar sun fara bayyana kimanin makonni uku da suka gabata.

Ya kara da cewa a ranar Asabar kadai an kwantar da marasa lafiya 15, inda uku daga cikinsu suka rasu jim kadan bayan isarsu asibiti.

A bangaren gwamnati, Kwamishinan Lafiya na Jihar Sokoto, Faruk Abubakar Wurno, ya tabbatar da cewa gwamnati ta fara bincike kan lamarin.

Ya ce an tura ma’aikatan lafiya yankin tare da samar da magunguna kyauta domin dakile cutar.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba yayin da ake ci gaba da kokarin shawo kan lamarin da gano ainihin cutar.

Sankarau
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
Labarai

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Sabbin Ministoci
Labarai

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
Labarai

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Next Post
Gaskiya Daya Ce

Gaskiya Daya Ce

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.