ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gaskiya Daya Ce

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Gaskiya

Aboki na gaske shi ne wanda zai lura da moriyarka. To, a bisa wannan sharadi, za mu san cewa, ba shakka kasar Sin wata abokiya ce ta gaske ga kasashen Afirka.Daga yau Juma’a, kasar Sin ta kaddamar da manufar yafe harajin kwastam kan kayayyakin da kasashe 53 dake nahiyar Afirka, wadanda suka kulla huldar diflomasiyya da ita, ke fitarwa zuwa kasuwanninta.

Ta haka, za a biya bukatun kasashen Afirka na fitar da karin kayayyaki zuwa karin wurare daban daban, tare da samun karin kudin shiga.Mene ne ainihin tasirin manufar nan ta yafe wa kasashen Afirka harajin kwastam? Za a samu amsa ta hanyar nazari kan misalin kasar Habasha.

Kasar Sin ta fara yafe wa kasar Habasha harajin kwastam tun daga karshen shekarar 2024, bisa la’akari da matsayin kasar na daya daga cikin kasashe mafi fama da koma bayan tattalin arziki a duniya.

ADVERTISEMENT

Daga baya, tsakanin shekarar 2024 da ta 2025, kasar Habasha ta fitar da waken gahawa (‘ya’yan kofi) fiye da tan dubu 34 zuwa kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 27%, bisa jimillar lokacin da ya gabace shi.Haka zalika, dimbin bukatun da ake samu daga kasuwannin kasar Sin, ya sa kamfanoni masu samar da gahawa na kasar Habasha iya mai da hankali wajen raya bangaren sarrafa waken gahawa, ta yadda aka inganta tsare-tsaren bangaren samar da gahawa na kasar Habasha sosai.

Manufar kasar Sin ta yafe wa kasashen Afirka harajin kwastam tana cike da sahihanci, saboda tana haifar wa kasashen Afirka da fa’ida, kana maimakon ta kasance wani nau’in tallafi mai dauke da sharadi, ita ce manufar da take tabbatar da moriyar dukkan bangarorin Afirka da Sin, da makomarsu ta samun ci gaba na bai daya.Za mu iya ci gaba da daukar gahawa a matsayin misali.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Ta hanyar yafe harajin kwastam da ake karba kan waken gahawa da ake shigar da su kasuwannin kasar Sin daga kasashen Afirka, to, mutanen kasar Sin za su iya sayen waken da farashi mai araha, kana su kamfanonin Sin da Afirka za su kara nuna niyyar zuba jari don habaka masana’antun sarrafa waken gahawa, tare da samar da karin guraben aikin yi a Afirka.

To, wannan misali ya nuna yadda ake tabbatar da moriyar dukkan bangarorin Sin da Afirka ta manufar nan ta yafe harajin kwastam.Ban da haka, za mu iya fahimtar sahihanci da manufar nan ta kunsa, ta hanyar kwatanta ta da manufofi na sauran kasashe.

A lokacin da wasu kasashe ke daukar matakan kashin kai don cin zarafin sauran kasashe, da kwace dukiyoyinsu, manufar da kasar Sin ta dauka ta zama mai samar da alfanu ga kasashen Afirka, wadda za ta tabbatar da kyakkyawar makomar hadin gwiwar bangarorin Sin da Afirka.

“A wannan lokacin da muke ciki, na fama da yanayin rashin tabbas a duniya, manufar nan da kasar Sin ta dauka tallafi ne da aka bayar kan lokaci, wanda ya kansace nau’in tallafin da ake samu daga ‘yan uwa”, in ji shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar kasashen Afirka ta AU, Mahamoud Ali Youssouf. (Bello Wang)

Gaskiya
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Gaskiya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani (2)

Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da 'Ya'yansu Alkur'ani (2)

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.