ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Harkar Fim, Sayar Da Abinci Ne Babbar Sana’ata – Aisha Yola

by Sulaiman and Rabi'at Sidi Bala
4 weeks ago
Aisha Yola

A yau shafin namu yayi cozali da daya daga cikin fitattun jaruman finafinan Hausa da ke masana’antar Kannywood, wato HAJ. AISHA MUHAMMAD ADAM wacce aka fi sani da HAJ. AISHA YOLA. Inda ta bayyanawa masu karatu irin matsalolin da suke fuskanta a cikin masana’antar Kannywood, kana ta yi bayani game da irin kalubalen da suke fuskanta ga masu kokarin shiga masana’antar. Jarumar ta bayyanawa masu karatu batutuwa masu yawa da suka shafi rayuwarta da kuma sana’ar ta.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka: Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki

Sunana Hajiya Aisha Muhammad Adam, wacce aka fi sani da Haj. Aisha Yola.

ADVERTISEMENT

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

Ni bafulatana ce gaba da baya (Hausa Fulani), mahaifina bafulatani ne dan garin Adamawa. Mahaifiyata kuma bafulatana ce ‘yar garin Gombe, amma mun girma mu a garin Kano. Batun karatu nayi sakandare Jss 3, ban je SS1 ba, amma karatun addini mun yi daidai gwargwado. Na taba yin aure ina da yara biyar, maza uku, mata biyu.

LABARAI MASU NASABA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Ni ma’abociyar kallon finafinan hausa ce, kuma abin na burge ni.

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Zan yi kamar shekara goma.

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

To, da farko dai ni ba da fim na fara ba, ina tare da mawaka ne, nayi dan harkokin siyasa na san mawaka sosai kafin na san ‘yan fim, dan mun yi yahon siyasa da mutane sosai ya zamana muna tare da mawaka. Kuma na shiga ‘Industry’ ne ta hannun mawakiya marigayya Rabi Mustapha Allah ya ji kanta da rahma, kawata ce, ita ta jaho ni ta kawo ni ‘industry’ ta danka ni a hannun Ghali Dizet Abdallah. Sai ya zamana duk mawaka na sani kafin na san ‘yan fim. Daga baya da tafiya tayi tafiya sai mutane suke ce min nayi fim to, daman ina sha’awar abin sai na tsunduma cikin harkar fim. Mutum na farko da ya jaho ni harkar fim shi ne Lawan Ahmad, dan ya zama kamar amini a waje na, muna abota da shi sosai, sai ya janyo ni ya saka ni a harkar fim. Amma ba shi ya fara yi min fim ba. Kamfanin ‘kamfa mobies’ su suka fara saka ni, Kawu Kamfa Mobie yaron gidana ne na dauke shi kamar kani, yana daukata a matsayin uwa, shi yake cewa, “Momi zan sa ki a fim”, na ce, “zan iya?” ya ce, “za ki iya”. Da zai yi aikin fim dinsa daga kamfaninsa ‘Kamfa Mobies’ Gudu A Duhu sai ya ce zan sa ki a ciki.

Ya batun iyaye ko ‘yan’uwa lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?

Wallahi ba ni da wata matsala da su, hasali ma da na zo na fadawa mahaifina, yana da kyakkyawar fahimta da ni ya ce ba komai, tunda sana’a ce, in je nayi sana’a ta. Kuma ‘yan’uwan mahaifina da na mahaifiyata duk ba wanda ya ba ni matsala sun goyi bayana dari bisa dari, daman lokacin mahaifiyata bata raye.

Ya farkon farawar ta kasance?

Abin da baka taba yi ba dole sai ka yi inda-inda, sai ka yi wasu abubuwa da baka iya ba, dole sai ka yi hakuri an nuna maka. Za ka rika ganin kamar mutane suna kyararka ko fada ake maka, ba fada bane gaskiya ake fada maka dan ka gyara. Amma dai an sha fama.

Da wane fim ki ka fara?

Gudu A Duhu, wanda na fito a matsayin surukar Ali Nuhu, kuma na fito a maman Maryam Babban Yaro, sai nayi fim na biyu ‘Baya da Kura’, sannan a lokacin na zo nayi ‘Abbana’.

Daga lokacin da ki ka fara kawo yanzu, kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

To, za su kai kamar guda biyar ko bakwai.

Cikin finafinan da ki ka fito wanne ne ya zamo bakandamiyyarki?

Izzar So, a shi ne fim din da kowa ya fi sanina a wancen lokacin, duk inda na fita ana matar matawalle Haj. Habiba.

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

Alhamdulillah Ala kulli halin, ni Haj. Aisha ina alfahari da harkar fim, ba dan komai ba sabodada kana zaune a unguwarku ma wani bai sanka ba, amma sanadiyyar harkar fim idan ka fito makotanka ma sha’awa suke su ga sun yi magana da kai, ko kuma sun nunawa duniya sun san ka. Ballantana wadanda suke gefe ma ba su sanka ba, ‘yan’uwanka ma alfahari suke suna so su ji an ce wance ‘yar’uwarmu ce ko wance ai mun santa to, Alhamdulillah. Saboda an samu nasara me tarin gaske da kuma ci gaba, duk inda mutum ya je yana da alfarma akwai abubuwa da yawa da ban isa yayi su ba, amma darajar fim da kuma daukakar da Allah ya bawa mutum sai ka ga ya je waje yayi abu ba tare da bata lokaci ba, ba tare da shan wahala ba. Ni ina ganin wannan ma wata babbar nasara ce.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta sanadiyyar fim, ko cikin masana’antar?

Ban taba ganin kalubalen da ya zame min matsala ba, har da zai dame ni. Saboda na san duk abin da mutum yake nema idan ma ya ga wata ‘yar matsala da bata kai ta kawo ba to, ya ajjiye akan cewa matakin nasara ce, kuma Allah zai bashi sa’a.

Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?

Abubuwa ne da yawa, na farko kamar yadda kake tafiya wani garin ko ka shiga cikin jama’a kai mu’amula da su, ka ga yadda al’umma suke yo wa caa! a kanka, saboda so da kauna. Wannan abun yana saka ni cikin farinciki da nishadi, da kuma wajen da za ka je kana ganin baka isa ba, sai ka ga kai ka isa ma.

Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?

Kwarai da gaske, ina da iyayen gida na gaske ba ma ubangida daya ba, iyayen gida, suna da yawan da ba za su fadu ba.

Ya ki ka dauki fim a wajenki?

Na dauki fim sana’a, kuma nayi niyyar zan kare mutuncina da na iyayena, kuma Alhamdulillah, ina iyakar kokarina. Duk da dai ita rayuwa ta duniya za ka iya yi wa wani daidai, wani kuma ba za ka yi masa daidai ba, ba me iyawa sai Allah.

Mene ne burinki na gaba game da fim?

In Allah ya so ya amince ina da burin zama ‘producer’, domin na rika yin finafinai nawa na kaina. Ko da Allah ya kawo min miji nayi aure, ko a gidana zan rika yi.

Ya batun aure?

Akasari mata da muke harkar ‘Industry’ a Kannywood, muna fuskantar wasu kalubale daga wasu mutane da basu fahimce mu ba a kan aure. Wasu na ganin cewa, abu ne muke yinsa na shashanci ko kuma ba abu ne me mahimmanci ba, duk da aure shi lokaci ne kuma zuwa yake yi, duk lokacin da Allah ya nufa mace za ta yi aure duk son da take yi wa ‘Industry’ in lokacinta ya yi za ta yi aure. Amma ba dan wani abu ba, akasari za a gani a kashi goma mutanen da za su ce suna son mu, mu ‘yan fim kashi takwas ko tara, ba son Allah da Annabi ne ba, ba son aure ba ne. Kawai so ne na sha’awa ana ganinmu a fim, domin ana son mu. Kuma idan mutum an yi auren shi ya sa ake fuskantar kalubale sai a ga kwana biyu uku mace ta je gidan miji aure ya mutu. Sai a rika danganta mu da cewa, mu ‘yan fim ba ma son zaman aure, ba wai ba ma son zaman aure bane.

Ko akwai wani fim wanda ki ka fito cikinsa, daga baya ki ka yi da-kin-sanin fitowa cikinsa?

Akwai finafinan da nake matukar so, amma ban yi da-na-sanin fitowa cikin su ba, suna da yawa wadanda nake alfahari da su, babu wanda na yi da-na-sanin fitowa cikinsa. Saboda rol din da ake ba ni kusan wanda nake so ne, kuma ina alfahari da shi.

Wane fim ne ya taba faranta miki rai, kuma me ya sa?

Suna da yawa akwai; Abbana, irin rol din da aka ba ni, na ji dadi sosai yadda nake fitowa ba ni da lafiya, yadda ita Aisha Aliyu Tsamiya ta nuna cewa bayan na rasu Abbanta take so, wannan fim din har gobe na ganshi ina jin dadinsa. Sai Hauwa Kulu, mu talakawa ne ni da ‘ya ta da kuma mahaifinta ya zo ya rasu, irin yadda aka wulakanta ta a matsayinta na ‘ya mace aka yi mata fyade, wannan fim din kullum yana taba zuciyata, ba dan komai ba mu muna da ‘ya’ya musamman ‘ya mace, darajarta da mutuncinta in aka taba mata shi abin yana sosa min rai. Ina son fim din amma kuma kullum fim din yana saka ni kuka da tausayi. Sai kuma Izzar So, ina son Izzar so, saboda lokacin da na shiga karaktar izzar so ina matukar jin dadi in na fito ina aktin abin yana saka ni nutsuwa yadda nake girmama mijina Ali Nuhu, nake darajanta shi a matsayina na mace me hankali a gidansa. Sai kuma Labarina ina sonsa musamman yadda nake taka rawa matsayin matar baban Aliyu ina jin dadi.

Ko akwai wasu matsaloli a cikin masana’antar Kannywood wadanda ki ke ganin ya kamata a gyara su?

Ba za mu ce ba mu da matsala ba, muna da matsala, duk inda aka ce an tara mutane sun kai shida, goma, sama da haka, dole sai ka samu mutum kowa da irin yadda Allah yayi halinsa, da zuciyarsa. Abin da yake min ciwo shi ne, matsala za ta samu dan’uwanka alla-alla kake kai za ka je ka yi bayani a media duniya ta gani, ka tona masa asiri, ko ka fadi abin da yayi wanda ba shi da kyau. Me makon a matsayinka na dan’uwansa ka jaho shi ka kira ho shi, ka nuna masa abin da yake bai kamata ba, ka daina. Sai ka je ka fadawa duniya. Kuma in ka fadawa duniya suna ganinmu ai mun zama uwa daya-uba daya sai su ga mun zama ba mu da hadin kai. A junanmu muna cin dunduniyar junanmu, muna kawo kalubalen junanmu. Ya kamata mu rika hakuri da junanmu, mun riga da mun zama tsintsiya daya, madaurinki daya. Kowa da yadda yake rayuwarsa, amma idan ka san halin mutum za ka iya cin maganin zama da shi, mu kasance masu son junanmu, domin babu abin da ba zamu samu ba muddin za mu kaunaci junanmu. Dan wannan masana’antar tamu masana’anta ce me dimbun alkhairi da albarka, me dimbun arziki da Allah yayi mana ita. Ko yau mutum ya zo idan Allah ya rubuta mutum yana da nasibi a cikinta sai Allah ya azurta shi a ciki kuma sai ya samu abin da ba ya taba tsammani.

Misali ki zama shugaba, wane irin ci gaba ki ke ganin za ki kawo ga masana’antar Kannywood?

Shugabanci yana da wahala, da Allah zai sa mu rike gaskiya, komai dacinta ko za a ji haushinmu, mu fito mu yi abu tsakaninmu da Allah kuma mu fadi gaskiya, duk da duniya ta canja yanzu, dole za mu samu masu goyon baya.

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Eh! Ina sana’a wacce na taso da ita, ina harkar abinci, saboda da ina da ‘Restaurant’. Amma yanzu babu, har yanzu ina harkar abinci duk wani taro da ake yi ko biki, ko suna, ko taron siyasa, in ana bukatar abinci na gargajiya ko na turawa na zamani duk ina yi, ina karbar kwangila ina yi wa mutane har gobe.

Ya alakarki take da sauran jarumai, da kuma wadanda ku ke tare da su tun kafin ki fara fim?

Alaka ce me kyau, tunda nake tare da su babu wanda muka taba fada a junanmu, idan mun hadu muna mutunta juna muna gaisawa, a yi wasa da dariya. Idan wani abu ya faru na farinciki ko jaje zan je, haka in aka ji nawa za a zo min. Muna zumunci muna alaka me kyau. Haka wadanda kafin na shiga harkar fim, wadanda muke tare da su, muna ci gaba da zumuncinmu, sai dai uzuri da suke dan yi min na abubuwa da za su faru za a ga ban je ba, saboda rashin samun lokaci kaina, sai dai daga baya ka je ka yi wa mutum murna, ko jaje.

Ko akwai wadanda za ki gaisar?

‘Yan’uwana da abokan sana’a ta, duk kaninsu ba wanda ba na alfahari da su, da masu kallo na da kuma abokanan sana’a. Ina alfahari da furodusas din mu da kuma daraktocinmu ta yadda suka yarda da cewa muna yi musu abin da suke so, har suke neman mu suke saka mu a kan aikinsu. Masu kallo Allah ya saka da alkhairi, idan mun yi kuskure a taimakk a gyara mana domin mu masu kuskure ne. Ina yi mana fatan alkhairi, Allah ya kara mana lafiya da zama lafiya, ya ba mu shugabanni na gari. Gidan jaridar LEADERSHIP HAUSA ubangiji Allah ya tabbatar musu da alkhairi, Allah ya sa wannan abun da suke yi ya kai ga gacin abin da ake nema. Allkh ya kara basu kwarin gwiwa da kokari na kan yadda duk suke ganin cewa za su yi kokari mu ma jarumai su tambaye mu damuwarmu ko matsalar mu, mu fada musu su fadawa duniya domin su dada fahimtar mu. Ina yi muku fatan alkhairi, na gode.

Aisha Yola
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
  • Sulaiman
    Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
  • Sulaiman
    Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus
  • Sulaiman
    ’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP
Aisha Yola
Rabi'at Sidi Bala
+ posts Bio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A 29-05-2027
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

MASU ALAKA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Nishadi

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

May 23, 2026
Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano
Nishadi

Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano

May 16, 2026
Next Post
Aisha Yola

Ko Kin San...Yadda Za Ki Zauna Da Mijinki Mai Mata Fiye Da Daya?

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.