ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kin San…Yadda Za Ki Zauna Da Mijinki Mai Mata Fiye Da Daya?

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
4 months ago
Mata

Aure na da babbar hikima da daraja a musulunci, kuma Allah ya halatta wa maza su auri mata har hudu, idan har za su yi adalci. Idan mijinki yana da mata fiye da daya, ga wasu shawarwari da za su taimake ki don zaman lafiya da kwanciyar hankali.

1. Fahimtar Matsayinki a Aure:

Kamar yadda kowa yake da hakki a aure, ki san cewa Allah ne ya kaddara hakan.

ADVERTISEMENT

Idan mijinki ya kara aure, hakan ba yana nufin baya kaunarki ba.

Ki fahimci cewa Allah ne ya ce suyi, namiji daban yake da mace, don haka yana da bukatar kulawar mata fiye da daya.

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

2. Kar ki ji kishi mai hana hakuri:

Kishi dabi’a ce ga mata, amma kada ya kai ga yin mugun hali.

Idan kika dinga kishi sosai, hakan zai hana ki nutsuwa kuma zai iya haifar da matsaloli da mijinki.

A yi kishi cikin hikima, ba tare da cin zalin wata daga cikin matan ba.

3. Yin hakuri da adalcin miji:

Miji yana da hakkin bai wa kowacce mace kulawa da lokaci, kudi da bukatun aure.

Idan ba zai iya zama da kowacce daidai ba, yana iya haifar da matsala.

Idan kina ganin yana nuna wariya, ki yi magana da hikima ba tare da hayaniya ba.

4. Kar ki yi kokarin rabawa da zuciya:

Wata mace idan mijinta ya kara aure, sai ta fara son ganin rabuwar sa da sabuwar matar.

Wannan ba daidai ba ne, domin Allah yana kin cutar da wani ba tare da hakki ba.

Idan mijinki yana adalci, ki runguma da zuciya daya.

5. Girmama ‘yar uwarki (Matar Mijinki):

Kamar yadda kike son ayi miki adalci, ita ma tana da hakkinta.

Ki guji yi mata zagon kasa ko tona mata asiri.

Ku zama ‘yan uwa, domin ku ne abin alfaharin juna.

6. Ki zauna lafiya da mijinki:

Ki yawaita kwalliya da gyaran jiki don ya ci gaba da jin dadin kasancewa da ke.

Ki guji magana mara dadi ko yawan gunaguni, don kada ki fusata shi.

Ki bi shi da ladabi da hikima, domin hakan yana sa miji ya kara son mace.

7. Dogara ga Allah da yin addu’a:

Idan kina jin damuwa ko matsala, ki dogara ga Allah.

Ki nemi shawara daga malamai idan matsalolin sun yi yawa.

Ki yawaita yin istighfari domin Allah ya daidaita muku zaman aure.

Zaman aure da kishiya ba abu ne mai sauki ba, amma idan kika dage da hakuri da hikima, za ki zauna lafiya. Allah ya albarkaci zaman ku, ya baku zuri’a mai albarka.

Shawara ga mace ta biyu ko mai niyya da shirin zama mata ta biyu:

Ki yi hakuri. Tabbas, bayan an kai ki, za ki fuskanci kalubale da dama. Zai yiwu ki ji kamar mijinki ya rage miki kulawa, ba kya samun isasshen lokaci da hankalinsa, kuma watakila ya fi bada lokaci ga matarsa ta farko. Wata rana kina tare da shi, amma yana ta waya da ita. Wani kuwa har bai iya daga wayarki idan yana wajenta. Irin wannan abubuwan na iya faruwa, kuma wani lokaci ma fiye da haka.

Ki yi hakuri. Ina tabbatar miki cewa yana cikin matsanancin hali. Yana kokarin shawo kan matarsa ta farko, domin a mafi yawan lokuta, maza ba su fahimci kissa da dabarun mata ba. Wasu matan suna amfani da kuka, marairaicewa, da neman tausayi wajen janyo hankalinsa. Wata kuwa tana nuna wa mijinta cewa an tauye mata hakkinta da auren da ya kara, wanda hakan ke sa shi jin cewa bai kyautata mata ba.

Abin da ya sa kika shigo da’irarta ya sa zai fi tausaya mata fiye da ke, musamman idan suna zaman lafiya. Idan kuwa suna da matsaloli tun kafin ya aureki, to shi ma yana iya fuskantar irin wannan hali daga gare ta.

Yadda za ki yi da lamarin:

Ki yi hakuri, ki ba su lokaci.

Kar ki yi korafi, kar ki nuna tashin hankali.

Kar ki ambaci sunanta ko matsalarta a cikin maganarki.

Ki kauda kai daga duk abin da suke yi.

Ina tabbatar miki, idan kika ci gaba da yin hakuri da kawaici, wata rana zai fara tunanin cewa bai kyauta miki ba. Zai soma tsarguwa da abubuwan da matar farko ke yi, har ya soma juyowa gare ki. A hankali, zai fara fahimtar sharrinta ko salon da take amfani da shi.

Idan kuwa kika dage da korafi da mita, zaifi ma jin tausayinta fiye da ke. Ki fahimta cewa hakuri ne kadai zai baki nasarar samun hakkinki, amma fada da tirjiya ba lallai su amfanar da ke ba.

In kuwa ba za ki iya hakuri da wannan ba, to ki shirya yin fada da ba lallai ki yi nasara akansa ba. Idan kuma baki shirya duk wani kalubale ba, to ki hawura da auren namiji mai mata.

Mata
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Mata
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Mata
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada

Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al'ada

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.