ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Jinkiri Da Dimbin Hasashe Abba Kabir Yusuf Ya Rungumi Tafiyar Tinubu

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago
Abba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a karshe ya yanke alaka da Rabiu Musa Kwankwaso, surukinsa, jagoransa kuma uban gidansa a siyasa.

Yusuf ya kasance a karkashin inuwar Kwankwaso tsawon kusan shekaru 25, inda ya rike mukamai daban-daban, ciki har da mukamin kwamishina a Jihar Kano, har zuwa shekarar 2023, lokacin da Kwankwaso ya tsayar da shi takarar gwamna, duk da kasancewar akwai wasu ‘yan takara mafi shahara da bayyana.

  • Yadda Shugaba Tinubu Ya Yi Tuntuɓe Ya Faɗi A Turkey 
  • Murabus Ɗin Ganduje: ‘Yan Kwankwasiyya Na Shirin Ɗaukar Wani Mataki

Yusuf ya bi ubangidansa Kwankwaso daga PDP zuwa APC, daga nan ya koma PDP, sannan zuwa NNPP. Wannan hadin gwiwa ta kasance wadda aka jarraba kuma ta tabbatar da kanta tsawon lokaci.

ADVERTISEMENT

Irin abin da ‘yan siyasa kadai ke iya watsarwa sannan su murmure daga girgizar da ya haifar cikin kankanin lokaci ko ma ba tare da bata lokaci ba.

Hanyar Zama Namiji Mai (’yancin kai)

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

A ranar Litinin, 26 ga Janairu, Yusuf ya koma kan abin da shi da uban gidansa a siyasa suka taba kin kusantowa, wato abin da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje wani tsohon abokin tafiyar Kwankwaso na dogon lokaci wanda daga baya ya kauce masa ya kuma jefar da hula ya aikata.

Tun bayan da ya samu nasarar zabe mai cike da cece-kuce ta hukuncin Kotun Koli a watan Janairun 2024 hukuncin da ya soke na Kotun Zabe da kuma Kotun Daukaka Kara magoya baya, masoya da masu karfafa gwiwa suka fara rada wa gwamnan kunne da ya ajiye kwalbar shayarwa, ya tsaya da kafafunsa da kansa.

Idan aka waiwayi al’amura, wannan dole ne ya kasance hukunci ne na ko a ci ko a mutu ga Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba Gida-Gida.” Wani mawuyacin hali ne

Amma daga karshe, ya tsallaka kogin Rubicon, ya kubuta daga abin da mutane da dama ke kallon a matsayin wa’adin mulki na uku na surukinsa a Fadar Gwamnatin Kano.

Amon Martani Daga Roma

A cikin abin da ya yi kama da amo daga tsohuwar Roma, Kwankwaso ya ayyana ranar 23 ga Janairu ranar da Yusuf ya sauya sheka a matsayin Ranar Cin Amana ta Duniya. Idan Kano ta zama Roma, shin Yusuf zai zama sabon Julius Caesar, Kwankwaso kuma Pompey? Kamar yadda Caesar ya yi a zamanin Roma, gwamnan ya bijire wa gargadin kada ya tsallaka kogin Rubicon abin da a wancan lokaci ya kasance babban matakin shelanta yaki.

Amma ganin cewa iska ta iko na tura jirgin Yusuf gaba, yayin da Kwankwaso ke cikin hunturun Pompey, gwamnan ya zabi lokaci mafi rauni don kai hari.

Natsuwar Da Ke Cike Da Fargaba

Abin mamaki, Kano na cikin kawaici a halin yanzu. Motsi na Kwankwasiyya mai cike da tsananin biyayya, rundunar masu sanya jar hula da ke daukar Kwankwaso a matsayin gwarzo, jar hular kuma alamar aminci kamar sun karbi abin da suka kira cin amanar Yusuf kamar dai yadda suka yi a lokacin Ganduje a baya: suna jira ne kawai, cikin natsuwa mai cike da fargaba.

A cikin duniyar siyasa mai cike da kifayen Shark, kare kai shi ne doka ta farko. Me nake samu a ciki? Shin akwai hanyar da zan bi in samu wa’adi na biyu, musamman ganin jita-jitar cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, na da burin tsayawa takara? Ko kuwa an tanadar min mafita lafiya idan na bar mulki? Manyan masu ruwa da tsaki su kan fara da tabbatar da tasu maslahar, daga bisani ne ake tattauna muradun mabiyansu.

Mataki Na Gaba Ga Al’ummar Kano?

Me ke gaba? Kano sau da yawa na karya ka’idojin siyasa. Siyasar jihar tana da zurfi, tana da halin bijirewa al’ada cikin hadari, amma kuma tana da tasiri mai nauyi. Wannan ne ya sa jam’iyyar NEPU ta Aminu Kano ta doke jam’iyyar NPC mai goyon bayan masu mulki, kuma ya sa PRP ke doke NPN a kai a kai.

A shekarar 2003, jam’iyyar ANPP ta Ibrahim Shekarau ta doke jam’iyyar PDP mai karfi a fadin kasa karkashin Kwankwaso, kafin Kano ta haifi motsin jar hula mai tsananin biyayya ko da ba tare da wani takamaiman dalili ba bayan shekaru takwas.

Yanzu haka, da yiwuwar sake jeri na siyasa inda Yusuf, Ganduje da Shekarau za su kasance a bangare guda, yayin da Kwankwaso ke a daya gefen, an riga an jefa kuri’ar kaddara.

“Shirme!” in ji wani aminin Kwankwaso. “Idan Kano ta yi yunkurin taka rawa a zaben gwamna na 2027, to sauyin shekar Yusuf na iya zama abin da zai rufe masa makomar siyasa gaba daya. Tunanin cewa kasancewa a jam’iyyar da ke kan mulki tabbacin nasara ce, tana iya zama kuskure mai hallakarwa ba gare shi kadai ba, har da sauran gwamnonin da suka sauya sheka.

Jar Hulata

Kusan nan take bayan sauyin shekarsa, an fara bayyana cewa Yusuf yana da tabbacin samun tikitin takarar gwamna na APC a zaben shekara mai zuwa. Tun kafin ya bar NNPP, yana da hakkin fifiko (right of first refusal) kan tikitin jam’iyyar. Kuma har yanzu yana sanye da jar hularsa.

Tuni ma an fara ganin hadakar jan hular da alamar Tinubu. Shin Yusuf zai tafi APC tare da Kwankwaso? Kada wani ya yi mamaki idan hakan ta faru, duk da hayaniyar zargin cin amana. ‘Yan siyasa ba lallai su kasance masu nufin abin da suke fada ba.

Abin da ke gaba na yi wa kowa alkawarin zama abin sha’awa da kuma daukar hankali matuka.

Ishiekwene shi ne Babban Edita (Editor-In-Chief) na jaridar LEADERSHIP, kuma marubucin littafin ‘Writing for Media and Monetising It.

Abba
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Maniyyatan Nijeriya
Manyan Labarai

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026
Next Post
Fasahar Electronic Call-up Da NPA Ta Wanzar Ta Samar Da Sauki —Tsohon Kwaminsihan Sufuri

Fasahar Electronic Call-up Da NPA Ta Wanzar Ta Samar Da Sauki —Tsohon Kwaminsihan Sufuri

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.