A kwanan nan ne ma’aikatar cinikayya ta Sin, ta fitar da “Matsayar Sin dangane da batun wai ana fitar da hajoji fiye da kima”, inda a ciki ta kore dukkanin zarge-zargen da aka yiwa Sin na “fitar da hajoji fiye da kima.” A wani ci gaban kuma, binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta Sin ta gudanar, ya nuna yadda kaso 81.7 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi, suka soki lamirin wasu kasashe, bisa yadda suka fake da zargin “Fitar da hajoji fiye da kima” don cimma burikan siyasar yankuna, ko bayar da kariyar cinikayya, da kakaba laifin hakan kan wasu sassa.
Masu bayyana ra’ayoyin sun kuma zargi irin wadannan kasashe da siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya, da ma yadda suke iya fakewa da batun tsaron kasa wajen aiwatar da matakai marasa dacewa.
Batun wai ana “Fitar da hajoji fiye da kima”, ya sabawa ka’idojin gudanar hada-hadar tattalin arziki, kuma irin wadannan zarge-zarge ba za su kawar da koma baya a fannin gogayyar ciniki da wasu masana’antu ke fuskanta ba.
Sakamakon binciken jin ra’ayin jama’ar ya nuna cewa, kaso 87 bisa dari na masu bayyana mahangar, na ganin a hada-hadar tattalin arziki bukatu da yawan samar da hajoji suna danganta, wato dai babu wani kaidin dindindin na daidaita yawan bukatu da hajojin da ake samarwa.
Bugu da kari, kaso 84.7 bisa dari na masu bayyana ra’ayin sun gamsu cewa, madaidaicin adadin hajojin da ake iya bukata na danganta ne da mabambantan kasashe, wato dai babu wani mizani da zai iya game kowa da kowa. (Saminu Alhassan)














