A shekarun baya-bayan nan, wasu kasashen yammacin duniya sun siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya don ba da kariya ga karfin sana’o’insu da matsayin kasuwanninsu, sun yi zarge-zarge kan kasar Sin na “fitar da hajoji fiye da kima”, da “matsin lamba daga kasar Sin 2.0”, ta yadda suka bayar da matakan ba da kariya ga cinikayya ta hanyoyi daban daban.
A jiya ranar 28 ga wannan wata, ma’aikatar cinikayya ta Sin, ta fitar da “Matsayar Sin dangane da batun wai ana fitar da hajoji fiye da kima”, inda a ciki ta kore dukkanin zarge-zargen da aka yiwa Sin na “fitar da hajoji fiye da kima” ta bayar da kididdiga da misalai masu yawa.
Dalilan da suka sa wasu kasashen yammacin duniya suke fuskantar matsalolin samun ci gaba, sun hada da gyaran hanyoyin samar da kayayyaki na duniya, da tashe-tashen hankali a wasu yankuna, da matsalolin da aka haifar domin yin kwaskwarima da sauransu, ba wai tasirin sana’o’in kasar Sin ba.
A hakika, kasar Sin tana yin amfani da fifikon kasuwa, da bunkasar sana’o’i, da ci gaban kimiyya da fasaha don kara samar da damar kasuwanni, da bunkasa, da yin kirkire-kirkire ga dukkan duniya, wato kiyaye samar da “damar kasar Sin 2.0”.
Ya kamata kasashen da abin ya shafa su bi odar tattalin arziki, su yi nazari da kansu yadda ya kamata, domin zarge-zarge kan kasar Sin ba zai warware matsalolinsu ba. A kwanakin baya, hukumomin binciken jin ra’ayoyin jama’a na kasa da kasa da dama, ciki har da cibiyar nazari ta Pew ta kasar Amurka, bincikensu ya nuna cewa, ra’ayoyin kasa da kasa dake shafar kasar Sin na kara kyautata a fadin duniya. Wannan ya shaida cewa, zarge-zarge iri-iri da ake yiwa kasar Sin ba za su iya canza ra’ayoyin jama’ar duniya ba, kuma suna amincewa da ra’ayin “damar kasar Sin 2.0”. (Zainab Zhang)













