ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buƙatar Taimaka Wa Al’umma Ba Sai Sun Yi Roƙo Ba

by Ibrahim Bala
2 months ago
Taimaka

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

A yau zan yi jan hankali ne ga ɗaukacin musulmi gaba ɗaya a duk inda suke, ba iya maza ba har ma da matan. Muna da wata ɗabi’a, da ta shiga zuciyarmu yanzu, za ka ga idan kana tare da mutum ko da kun fi shekara goma sha ko ashirin, wani ma tare kuka taso, za ka ga wasu Allah ya rufa musu asiri a ciki.

Kuma akwai wanda da kyar ma yake iya siyan abinci ya kai wa iyalinsa, wai idan bai roƙa ba, ba za a iya taimaka masa ba, kuma ana ji ana kallo.

ADVERTISEMENT
  • Sin Ta Samun Gaggarumin Ci Gaban Ayyukan Taimakon Masu Bukata Ta Musamman 
  • Gwamna Bala Ya Yi Alhinin Rasuwar Yariman Bauchi, Garba Muhammad Sambo

Haba ƴan’uwa musulmi, “Almuslumu akul muslum” Annabi ne ya faɗa, duk inda musulmi yake ɗan’uwan musulmi ne, ballantana wanda aka taso.

Wasu ma za a ga jini ɗaya ne, amma mutum yana cikin wani yanayi kai ka san ka ninninka shi a samu, ƙila ba ya iya siyan abincin yau da gobe a gidansa, kullum sai ya sayi wanda za a dafa, kai kuma akwai na wata ɗaya ko biyu a gidanka, amma wai sai ya roƙe ka za ka taimake shi, idan bai roƙe ka ba, ba za ka iya taimakonshi ba.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

Wannan ba daidai ba ne ba, wannan ba tausayi bane ba, ba halayya ce ta musulmi ba, ba ɗabi’a ce irinta sahabbai ba, ba halayya ce ta Annabawa ba.

Akwai tausayawa, akwai zumunci, ka taimakawa ɗan’uwanka musulmi ba sai ya nemi taimakonka ba, kai ka san ya kamata ka taimaki wane. Sai ka ga mutum ya mutu, sai akai buhun shinkafa, wai ana taimakawa iyalansa, wannan ƙarya ne, mugunta ce, ba daidai bane ba. Wani ya yi fafutuka tsawon shekara ashirin ko talatin yana ta neman ko da rabin kwata ne ya sayawa iyalansa, ba za a iya taimaka masa ba, kuma Allah ya taimaka masa.

A ciki ma za ka ga akwai wanda zai iya saya masa gidan, ya bashi mota, ya bashi jari, amma ba za a yi ba, wai sai ya mutu sai a je a ɗan sayarwa iyalansa gida.

Kai ka ji wani rashin tunani, ka taimakawa mutum tun da rayuwarsa da lafiyarsa, kai ko bashi ne mutum kake binsa, ya kamata tunda ransa da lafiyarsa ka bashi ya je ya biya.

Waye ba a bi bashi, idan mutum ba shi da hali kai ka sani, kana tare da shi ka taimaka masa ya ji daɗi. Ƴan’uwa idan muna so mu ga daidai, mu ƙare rayuwarmu lafiya sai mun taimaki ƴan’uwanmu. Wallahi ɗabi’un da muke bi, muke ɗauka ba daidai bane ba.

Mu taimakawa mutum ba sai ya kasa ba, ya kwanta ya kasa tashi, ko yunwa da talauci sun kashe shi, sannan zamu je mu kai wa iyalansa buhun shinkafa, haba wannan ba ɗabi’ar kirki ba ce ba.

Mu taimakawa mutane suna neman taimako, wani ko shekara ɗari zai yi ba zai tambaya ba, idan ka san kana tare da mutum yana neman taimako ka taimake shi ba sai ya tsuguna yana neman taimakon ka ba, ba sai ya kira ka a waya ya zubar da mutuncinsa ba.

Taimaka
Ibrahim Bala
+ postsBio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Zamfara

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 21 A Zamfara, Wasu Da Dama Sun Ɓace

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

June 24, 2026
Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.