ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burina Na Gaba Bayan Fim Shi Ne Aure —Khadija

by Rabi'at Sidi Bala
2 months ago
Fim

Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jaruman finafinan hausa manya da kanana, daga cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata bakuwar ta musamman wato, KHADIJA ABDULLAHI wacce aka fi sani da MAMAN YESMIN  cikin shirin Kwana Casa’in. Inda ta bayyana wa masu karatu batutuwan da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta ta fim, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki.

ADVERTISEMENT

Sunana Khadija Abdullahi, wacce aka fi sani da Maman Yesmin Kwana Casa’in.

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

Ni cikakkiyar ‘yar Gwagwalada ce, na girma a Gwagwalada nayi aure, bayan rasuwar mijina ina da yara guda uku.

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?

Saboda ni ma’abociyar kallon finafinan hausa ce, a wancen lokacin ana zuwa rantin din fim kaset irin me zare, kuma duk inda wani shago yake a garin Gwagwalada kowa ya sani sai na tafi na je na yi rantin. Ni kuma ina matukar son Aisha Dan Kano marigayiya kenan ita da Mansura Isah. Sai na ji ina sha’awa, na yi ta rokon Allah ya cika min burina har Allah ya cikan burina.

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Zan kai kamar shekara goma sha biyar da fara fim, amma daga farko da na fara na zo na dan katse sai da na dau wasu shekaru sannan na kara dawowa to, a yanzu da dawowa ta shekara shida kenan. Amma idan gaba daya tun daga farkon farawa zuwa yanzu ne shi ne shekara sha biyar.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

Ina cikin kallo a dakin yayata sai na ga wani fim na dauki lambobin dake jiki guda biyu sai na kira, daya na Sani Danja ne, daya kuma na wani ana ce masa Shamaki. Sani Danja ya ba ni time ya ce na je na same shi a cikin Abuja, sai na ga har na kagu na ga lallai an sakani a fim din nan. Sai na kara kiran na biyun shi ma sai ya tura min da lambar wani ana ce masa Kandahar yana nan a garin Abuja a ‘Wuse II’ na kira shi muka yi magana da shi, ya ce iyayena lallai za su yarda na ce ban da matsala iyayena za su yarda. To daga nan cikin yardar Allah sai ya siyi labari guda biyu da Babban Masinja da Baban Jari da Dan Jariri sai muka je muka yi wannan fim din tare da su Bosho da mutane da yawa, dan Bosho ne ma ya fito miji na a wancen lokacin.

Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?

Bayan na yi fim din nan guda biyu iyayena sun ji dadi har mamana idan ta ganni za ta ce ‘yata ta yi kyau, sai kuma aka 0fara samun gulmace-gulmace daga ‘yan gari “yanzu ki ka bar ‘yarki ta tafi ta je tana fim bayan an ce ‘yan fim karuwai ne” maganganu dai kala-kala. Sai ta zo tana fada min, na ce Mama karuwan nan ko a cikin daki fa idan mace ta so tayi karuwanci za ta yi karuwanci”, sai ta yi kamar ta amince daga karshe ma dai ta zo ta ce ita bata amince ba sai dai na je nayi aure. Muka zo ana ta fama ina ta lallashinta har ubangiji Allah ya sa ta amince ta yarda sai na zo na zauna a Kaduna. Bayan na zauna a karkashin ofis din iga ‘Wash Production’ na fara fassarar fim din Indiya shekara biyu, sai na ga wannan fim din fa shi nake so, daga karshe kuma sai na tsunduma ciki ka’in da na’in.

Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu, kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Gaskiya nayi finafinab da ba zan iya misalta su ba dan wasu sunan ma ba manta, amma akwai kamar su; Kwana Casa’in, Dadin Kowa, Labarina, Karan Batta, Dakin Amarya, Aliya, Kishiyar Uwa, gaskiya ba zan iya lissafa su ba, amma dai sun fi guda talatin.

A finafinan da ki ka fito ciki, wanne ne ya zamo bakandamiyyarki?

Bakandamiyata Kwana Casa’in, dan shi ya fito da ni kuma shi na fi so, har gobe har jibi ina son Kwana Casa’in.

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

Na samu nasarori sosai game da fim, sai dai mu ce Alhamdulillah.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da fim?

Gaskiya kalubalen da na samu bai wuce ace ‘yan fim karuwai ne, ana zagi da sauransu, a kullum mahaifiyata ta kan ce “ana zaginku ana cewa ba ku da tarbiyya, ki kasance me jin tsoron Allah, me addini, me biyayya da rikon amana” a kullum. Sai kalubale na biyu bayan na je Kwna Casa’in nayi ‘season4, 5’ daga karshe sai aka ce an kashe ni. Saboda tsananin kaunar Kwana Casa’in da nake, na rantse da Allah har kasa fita waje nayi, kowa sai cewa yake bamu ganki a wannan ‘season 6’ din ba, na ci kuka kamar raina zai fita. Na tashi nayi Sallah cikin dare na ce ya ubangiji idan wani lefi nayi ne a wannan aikin aka cire ni aka ce na mutu Allah ya fito min da mafita. Saboda a lokacin ban san ya rubutun labari yake ba. Ina ta addu’a sai gashi Allah ya kawon mafita ina ta shiga finafinai iri daban-daban, amma fa gaskiya ina son Kwank Casa’in.

Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?

Akwai Kandahar, akwai Abdullahi Abu uku, Baba kanin Baba Small, akwai Ibrahim Bala shi ma babban Ubangidana ne, domin a kamfaninsa nake, a kamfaninsa nayi rijista da na shiga garin Kano Alhamdulillahi gaskiya na ji dadi, sannan kuma a zan dan dawo daga baya, akwai wani ana ce masa Isah dan kaciya ne shi ma ta facebook muka hadu da shi, kuma shi ne sanadiyyar da ya hada ni ma da Abdullahi Abu Ukun da nake magana na garin Kaduna. Ina godiya ga iyayen gidana, sun taka rawar gani a gare ni kuma dalilinsu na taka wannan mataki ina godiya, Allah ya saka musu da alkhairi, Allah ya tsare gabansu da bayansu.

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Bayan fim ba ni da wata sana’a da ta wuce fim, ni fa fim ita ce sana’a ta, amma in sha Allahu nan ba dadewa zan fito da wata sana’ar.

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Burina na gaba a fim nayi aure.

Kamar yaushe ki ke saka ran yin aure?

Allah ne bai nufa ba, da tuni na kai shekara biyu a gidan miji, kin san shi aure da mutuwa da haihuwa wani abu ne rubutacce wajen ubangiji.

Misali wani daga cikin abokan aikinki ya ce yana sonki zai aure ki, shin za ki amince ki aure shi ko kuwa ba ki da ra’ayin auren dan fim?

Zan iya aurar sa idan na yarda da tarbiyyarsa, addininsa, kamun kansa, rike amanarsa, da duk abin da ya dace. Saboda masana’anta ce da ba zan iya zaginta ba, ta yi min riga, ta yi min wando ta yi min komai, a ciki nake ci da sha har na biyawa yarana kudin makaranta, har kuma na biyawa iyayena wasu bukatu.

Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice shin wace ce Kannywood ya cikinta yake?

Abin da zan iya cewa ga mutanen waje wadanda suke kalubalentar masana’antar, su gane cewa a duk fa inda kake akwai nagari, kuma akwai bata gari, duk wata sana’a ta duniya kasuwanci ne ko zaman ofis ne, akwai nagari akwai bata gari. Ni wannan masana’anta babu abin da zan iya cewa sai Alhamdulillah, na dauke ta kamar yadda zan je kasuwa na zuba kudina na saka jari a cikinta. Domin sai da na yi rijista na cike fom na biya kudin rijista sannan yanzu nake cin ribar wannan kudin rijista da na yi.

Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga masana’antar kannywood?

Ina kira ga ‘Yan mata wadanda ba su taba yin aure ba, idan za su shiga masana’antar su yi kokari dan Allah su je su yi karatu, idan suka yi karatu su yi aure, sannan su dawo su zauna a masana’antar nan. Idan kuma Allah ya nufa dole-dole za ki yi ba tare da kin yi aure ba ina kira da ki kasance me kamun kai. Ana cewa ‘yan fim ba su da tarbiyya, ta ya za ki taso a gaban iyayenki ba su yi miki tarbiyya ba ki fito ki ce dan fim shi zai yi miki tarbiyya? ba zai yu ba fa, duk wanda ki ka ga ya zama lalatacce a cikin wannan masana’antar to, daman can tun daga gidan iyayenshi lalatacce ne, haka ma idan ya zama nagari. Dan haka duk abin da za ki yi to, ki yi shi da sanin iyayenki sai ya fi yi miki albarka

Ko akwai wata shawara ko wani sako da ki ke da shi ga sauran abokan aikinki?

Muna fuskantar kalubale mun ‘yan fim duk abin da za mu yi duk motsinmu yana kan idon al’umma ne, walau idan ki ka yi me kyau za ki samu babban yabo, idan ki ka yi mara kyau za ki samu zagi. Ina jan hankalinmu mu ‘yan fim da mu kasance masu taka-tsan-tsan duk al’amarin da zamu yi, mu rika yin abubuwan mu a cikin tsafta, mu rika yin abubuwanmu cikin addini, a duk inda za mu shiga mu kama mutuncin kanmu, mu kama darajar kanmu, mu kama girmanmu. Saboda mu din nan sa mu bayar da fagen da wani zai zo ya zage mu zai zage mu, idan muka kasance masu biyayya masu tarbiyya ko lacation ne yau aka dauke mu zuwa wani gari muka je muka kama kanmu, muka kama darajarmu, ba ma wasa cikin maza, ba ma wani abubuwa to, babu yadda za a yi mutum ya fito ya zo ya zage ka.

Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?

Na gode! na gode!! nagode!!! Allah ya saka da alkhairi, domin idan ba da su ba, ba zan taka tsaunin da na taka a yanzu ba, Alhamdulillahi duk inda zan fita za a ganni ace Maman Yesmin ko kuma ace Maman Aliya na Dadin Kowa.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Da farko ina godiya ga Allah subhanahu wa ta’ala da Allah ya hada ni da Shamaki ya hada ni da ubangida wanda ake ce masa Kandahar, daga karshe na fada hannun Abdullahi Abu uku, wanda ke garin Kaduna, shi ne silar da har na taka garin Kano ya hada ni da Ibrahim Bala. A ranar da muka hadu da Ibrahim Bala washegari ya kira ni ya ce min za ki iya yin fim din kwana casa’in, na ce eh zan iya. Ba zan iya misalta farincikin da na shiga a ranar ba. Ibrahim Bala ya taka rawar gani sosai a kaina, ya turo min da takardar ‘audition’ na ci na zo na fara fim. Ranar da aka fara saka min camera a kwana casa’in nayi kukan farinciki sosai. Ina jinjina sosai ga Ibrahim Bala domin a dalilinsa na yi kwana casa’in da Labarina.

Muna godiya ki huta lafiya.

Ni ma na gode sosai

Fim
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A 29-05-2027
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

MASU ALAKA

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Nishadi

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

May 23, 2026
Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano
Nishadi

Har Yanzu Burina Bai Cika Ba A Waka —Hadiza Maikano

May 16, 2026
Next Post
FIFA Ta Ci Tarar Nijeriya Da Congo

FIFA Ta Ci Tarar Nijeriya Da Congo

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.