ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

by Rabi'at Sidi Bala
2 months ago

Shafin da ke zaƙulo muku fitattun jarumai da mawaƙa mnya da ƙanan, daga cikin masana’antar Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wani babban baƙon na musamman, wanda ya shafe tsahon shekaru masu yawa a cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood wato, HABIBU YARO HARUNA wanda aka fi sani da HABIBU YARO. Inda ya bayyanawa masu karatu batutuwa da dama masu yawan gaske game da abin da ya shafi masana’antar Kannywood da kuma rayuwarsa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi.

ADVERTISEMENT

Sunana Habibu Yaro Haruna, wanda aka fi sani da Habibu Yaro.

Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka?

LABARAI MASU NASABA

Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

Ni ɗan Kano ne, kuma na yi makaranta a kano, har yanzu ina zaune a kano.

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Na kasance a Kannywood ina ɗan yaro ƙwarai. Kuma sha’awace ta ja hankalina, kuma na kasance ina son wasan kwaikwayo tun ina ‘primary’.

Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?

Na ɗan jima, domin ina cikin masana’antar nan tun kafin a raɗa mata suna (tun kafin ta zama Kannywood).

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

Ina cikin ƴan gwagwarmayar wannan masana’anta, domin a lokacin da na zo wannan masana’anta ƙalilan ne a cikinmu suka gano cewa wannan harkar za ta iya zama sana’a, saboda ƙalubale da muka sha.

Ya batun iyaye ko ƴan’uwa lokacin da za ka sanar musu kana sha’awar fara fim, ko ka samu wani ƙalubale daga gare su?

Lokacin da na zo Kannywood dole kin san akwai ƙalubale kafin a yarda, kuma gashi mun zo inda muka zo.

Ya farkon farawar ta kasance?

Da farko na fara da ‘stage drama’ ne, wato wasan daɓe kafin in fara shiga ‘drama’ ta NTA da CTƁ, daga bisani na fara fitowa a finafinan siyarwa.

Da wanne fim ka fara

Finafinan kasuwa da na fara fitowa a ciki shi ne ‘Ki Yarda Dani’, kuma na fito a matsayin ɗan aiken gida a cikin fim ɗin.

Daga lokacin da ka fara kawo yanzu ka yi finafinan sun kai kamar guda nawa?

Na fito a finafinai ba masu yawa sosai ba.

Ko za ka iya faɗowa masu karatu kaɗan daga cikin finafinan da ka fito ciki?

Fim ɗin da na fito shi ne; Marainiya, wanda Alhaji ibrahim Mandawari ya shirya kuma ya bada umarni.

Cikin finafinan da ka fito ciki, wanne ne ya zamo bakandamiyyarka wanda ka fi so, kuma me ya sa?

Fim ɗin da na fi so shi ne ‘Marainiya’, wanda Alhaji ibrahim Mandawari ya shirya kuma ya ba da umarni.

Waɗanne irin nasarori ka samu game da fim?

Alhamdulillah na sami nasarori da yawa.

Ko akwai wani ƙalubale da ka taɓa fuskanta sanadiyyar fim, ko cikin masana’antar?

Maganar kuma ƙalubale babu wata rayuwa da babu ƙalubale amma Alhamdulillah.

Wane abu ne ya taɓa faruwa da kai na farinciki ko akasin haka wanda ba za ka taɓa iya mantawa da shi ba a rayuwa?

Akwai abubuwa da dama da suka faru da ni na ɓacin rai da na farinciki da suka faru da ni, wanda ba sai na faɗa ba, amma Alhamdulillah.

Ya ka ɗauki fim a wajenka?

Na ɗauki sana’ar fim a matsayin sana’a wacce take cike da arziƙi.

Ko kana da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?

Ina da iyayen gida a Kannywood, wasu na rigasu zuwa, wasu sun rigani zuwa. Amma maigidana wanda na rayu da shi, na taso a hannunshi shi ne Alhaji Ibrahim Muhammad Mandawari (Mai Unguwar Mandawari)

A can baya ka yi finafinai da dama, daga bisani kuma masu kallo suka daina jin motsinka, shin me ya faru?

A da ni ɗan wasa ne, daga bisani na zama ‘producer’ kuma marubuci, wannan shi ne dalilin da ya sa na rage fitowa, amma yanzu zan fito a cikin wani sabon shiri na mai suna ‘BALAN KUƊI’ wannan ni ne zan fito a matsayin Balan kuɗi.

Mene ne burinka na gaba game da fim?

Burina da masana’antar nan shi ne lafiya da zaman lafiya, da ƙaruwar arziƙi.

Ya za ka bambantawa masu kallo, bambancin finafinan baya da kuma na yanzu, sannan wanne irin ci gaba aka samu ko kuma koma baya a wannan lokacin game da fim?

Bambancin finafinan da, da na yanzu shi ne; labari, ilimi da ‘technology’.

Ko akwai wani fim wanda ka taɓa fitowa ciki, daga baya kayi da-ka-sanin fitowa cikinsa?

Ban taɓa fitowa a fim na yi da-na-sani ba.

Wane fim ne ya taɓa baka wahala wajen ɗukar shirin, kuma me ya sa?

Fim ɗin da na yi ya bani wahala, duk da dai ‘producing’ da ‘directing’ na yi, shi ne ‘Tsamiya’

Bayan fim kana wata sana’ar ne?

Bayan fim ina yin sana’ar Noma.

Wacce shawara za ka bawa masu ƙoƙarin shiga cikin masana’antar Kannywood?

Su kuma masu son shigowa ina basu shawara idan za su shigo su zo da niyyar sun zo Sana’a kuma su riƙe sana’ar da gaskiya.

Ko akwai wata shawara da za ka bawa sauran abokan sana’arka na fim?

Shawarar da zan ba wa ƴan uwa yan fim  ita ce, gaskiya da amana, tare da jajircewa akan abin da ka ke yi.

Ko kana da waɗanda za ka gaisar?

Gaisuwa ga Alhaji Ibrahim Muhammad Mandawari Mai Unguwar Mandawari, sai Salisu Muhd Officer, sannan kuma Ibrahim Bala, da kuma Sulaiman Abubakar Edited.

Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

MASU ALAKA

Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
Nishadi

Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Labarai

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

July 12, 2026
Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
Nishadi

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

June 14, 2026
Next Post
Masana Tattalin Arziki Sun Yi Watsi Da Rahoton NBS Kan Tattalin Arziki

Masana Tattalin Arziki Sun Yi Watsi Da Rahoton NBS Kan Tattalin Arziki

LABARAI MASU NASABA

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.