ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Ilimi, Duk Abin Da Ke ɓoye Ya Fito Sarari

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
6 months ago
Ilimi

A’uzu billahi minash shaiɗanir rajim. Bismillahirrahmanirrahim. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadinil fatihi lima ughliƙa wal khatimi lima sabaƙa nasirul haƙƙi bil haƙƙi wal hadi ila siraɗiƙal mustaƙim wa ala alihi haƙƙa ƙadrihi wa miƙdaril azim. Wa radiyallahu an ashabi rasulillahi sallallahu alaihi wasallam wala haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyil azim ya himmatash sheikh, ihdiri lana bi hazal mahdari walta’ɗifi bi nazratin ta’tilana biz zafari.

Yana daga cikin kayan ilimi dai, kamar yadda muka faɗa: ido ya bincika launinnika da launin abu, kunne sautika, harshe ɗanɗanon abu kaza ne, Hanci, ƙanshin abu kaza ba ƙanshin abu kaza ba, ƙarni, wari, ɗoyi, da sauransu, hannu kuma taushin abun, tsantsin abun da sauransu, wanda duk gabaki ɗaya suna kaiwa ƙwaƙwalwa, shi kuma hankali sai ya yi hukunci duk gabaki ɗaya. Wannan a taƙaice kenan.

  • El-Rufa’i Ya Kafa Tubalin Tsaro Da Ilimi A Jihar Kaduna – Jafaru Sani
  • ’Yan Jarida Da AGILE Sun Ƙulla Haɗin Guiwar Ƙarfafa Ilimin ’Ya’ya Mata A Sakkwato 

Haka tsarin abinci, don gane meye aciki, ta hanyar gwajin jini, ya kaza yake a ciki, abincika kaza a gane yaya yake, yawansa, dokokinsa da tsarukansa, hawan sa da saukan sa ya yake, da sauransu.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, ta hanyar gwajin jini, za a iya abincika rashin lafiyoyi, ya rashin lafiya kaza yake, ya kaza, ya zafin jiki yake, ya wannan hadaratul khams din nan suke: zafi, sanyi, ƙarfi, bushewa, lema. Duk likitanci yana cikin waɗannan abubuwa.

Yanzu da kaje asibiti zaka ga an sanya maka na’urar gwajin zafin jiki don gano rashin lafiyar jikin, sannan a bayar da magani kishiyar abin da aka gano.

LABARAI MASU NASABA

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

Toh wannan kenan, kamar yadda muka faɗa, tushen ilimi, shine ilimin lissafi. Lissafin gane kowane abu, musamman lissafin saba’ul masani, wannan lissafi na saba’ul masani (euler function), da pi number, kusan da su aka yi nuclear atom bomb, da shi akai kaza da kaza duk gabaki ɗaya. Da wannan lissafi, gaibu ta bayyana a sarari, babu wani abu da yake a ɓoye yanzun, da za a ce babu wanda zai iya saninsa, sai dai Hadrar Allah, itama ya zaɓi wasu bayin shi, Waliyyai Rabbaniyyina.

Rabbaniyyai, ana nufin bayin Allah, kamar yadda za a ce Kanawi – Ɗan Kano, Sokotowi – Ɗan Sokoto. Su, rabbaniyyai, bincike suke a hadarar Allah, “Arrahman, fas’al bihi kabira”, “wattabi’i sabila man anaba ilayya”, sun son Ubangiji, sabida bincike akansa. Don haka, babu wani Annabi ko bawan Allah da zai ce ku zama bayi na, “Kunu Ibadalli”, sai dai yace, ku zama bayin Allah, “Kunu Rabbaniyyina,” ku zama arifai ku san hadarar Allah, sai ku fahimci kaza da kaza.

Ƙur’ani yazo da bayanai filla-filla, ba wani abu da ya bari a baya, idan mutum ya duba Littafin “Sirril akbar”, zai ga wannan duk gabaki ɗaya filla-filla, domin ƙur’ani yazo da shi.

Albarkar wannan ilimin lissafin, yau duk gaibu ta zama sarari. Duk abin da shekara 200 da suka shige sunan sa ƙarya, ko kuma a ce, ba zai yiwu ba, yau ya zama gaskiya kuma ya yiwu. Ya zama gaskiya ya yiwu har ma yanzu ba wani abu da zamu ji an ce za’ayi a riƙa mamakin cewa, kaga ba zai yiwu ba, in dai ba dakikanci ba. Yanzu, Elon Musk ya ce, zai gina gari a duniyar wata, wannan, kamar anyi an gama ne. Kai ma in kana da iko je ka sai fili. Kar yau a ce za’ayi wani abu kace ƙarya ne, kai ma shiga cikin sahun, ayi da kai in kana da dama.

Toh don haka, da ilimin Ƙur’anin nan, ɗanAdam ya san asraran halitta. Cewa ba wanda ya san gaibu, idan jahili ne bashi da ilimin da zai san ta sai ya barwa Allah kayan sa. Bai hana malami yazo ya san ta ba. Malami, ba ana nufin malamin fikihu ba, da duk kan girmamashi, ana nufin Malamai masana asraran halitta, da suka hada da malaman physics, malaman binciken tarihi dake haƙo ƙasa, malaman Chemistry da sauransu. Duk wanda ya san falsafa, dole ya san akwai Allah, ko ya sani ko bai sani ba dole ya yadda da Allah, dole ya yi imani da Allah, ko ya ce bai yadda ba, toh ya yadda da wani karfi da yafi karfin halitta. Waɗanda suka yi ‘atom bomb’ ɗin nan, sun fi kowa tsoran Allah, sun fi kowa tsoran kansu, sunfi kowa tsoran wannan Bomb din, don haka suke tsawatarwa kada kowa yayi, su kuma su cigaba da yi don acigaba da jin tsoran su.

Toh ubangiji tabaraka wa ta’ala da ya fadi gaibu, adali ne, haka kawai ba zai faɗi abu ba kuma ya cigaba da ɓoye shi don kar a san wannan abun, ba don hakan ya faɗe shi ba. Ya kawo danAdam ne don ya san komai, yayi kusa da shi ta ibada, yayi kusa da shi ta ilimi, yayi kusa da shi ta ma’arifa, ba wani abu da ya kange cewa ba za’a san wannan ba.

Ba jahilin malami, sai wanda zai riƙa ɓoyewa almajirin sa ilimi, don kar su san wani abu, sai dai shi kaɗai kawai, ya yi ta alfahari da shi, ai ni ne kadai na sani, to meye birgewa? Babbar birgewa, almajiran ka duk sun san me kake faɗa, kayi ta faɗan abu a gaban su, kuma sun gane me kake faɗa. Shehu Ibrahim Kaulaha, yana cewa, “albarkan salati ga manzon Allah SAW, na jagoranci ƴan tsere kuma bana tsoran su cimmin, a cikin kowane fanni na jagoranci ƴan tsere, wallahi bana tsoran su cimmin, su yi ta zura gudu dai.” Toh wannan, shine birgewar malami, yana so ma almajirin sa ya fishi, abin da bai kai ba ya kai.

Ubangiji tabaraka wa ta’ala ya faɗi gaibu, kuma ya faɗi ma ganin ta. Babbar ayar da tayi maganan zancen gaibu, itace surar Aljannu (suratul jinni), sabida ɓuyarsa, shima yanzu ya zama sarari, turawa suna da abin da zasu ganshi, suna da abin da zasu kama shi, suna da abin da zasu yi magana da shi, misalin Injiniyoyi masu gina Gada da tituna acikin daji, duk za kaga wannan ilimin mai ban mamaki. Ubangiji tabaraka wata’ala ya faɗa cewa, “Alimul gaibi fala yuzhiru ala gaibihi ahadan – Allah shine masanin gaibu, baya tsinkayar da wani daya a gaibun sa, sai wanda ya yarda shi.” Ashe yana tsinkayarwa kenan. Misali, babu mai shiga wannan wurin taron, sai wanda aka ba shi katin gayyata, ashe masu katin gayyata za su shiga, tun da akwai kati a hannunsu. Ta ƙaƙa, wani zai zo ya ce, “baku ji ya ce bai yadda kowa ya shiga ba, sai wanda yazo da kati, ai yana nufin ba wanda zai shiga kenan”, Wannan mahaukacin ina ne haka. Yanzu wa ya karyata? Allah ya ce, zai tsinkayar da wanda yaso, na daga manzonninsa, kuma “fa innahu yasluku min baini yadaihi wa min khalfi rasada – shima zai sa masa mai tsare shi ta gaba da ta baya, sabida kar ya cakuɗa wannan ilimin da san ransa ko da halittar sa ta ɗanAdam, “iza tamanna alƙash shaidanu fi umniyyatihi, fayansakullahu ma yulƙish shaiɗanu, summa yuhkimmullahu ayatihi”, komai tsarkin annabin, da zai ji tsoron wani abu na ɗabi’ar ɗanAdam, da Shaiɗan ya samu hanyar zuba na shi.

Ta wajen wahayi, kuma ta wajen gangariyar ilimi, Shaidan kala-kala ne: akwai shaiɗan ɗin ilimi, wanda zai sa ma kokwanto a karatu, ga ilimi ka sani amma kokwanto ya shiga ka zaɓi wani abu wanda ba daidai ba, ya kasance yana karkatar da mutum daga kan yakini izuwa tawahhuri; Akwai shaiɗan na wajen cin abinci; ta wajen saduwa, ta wajen son mulki da dawwama.

Ilimi
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)

MASU ALAKA

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
Dausayin Musulunci

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

September 4, 2026
Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
Dausayin Musulunci

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

August 28, 2026
Ilimi
Dausayin Musulunci

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

August 21, 2026
Next Post
Ƙoƙarin Amurka Na Ganin An Haramta Shari’a A Nijeriya Ya Haifar Da Cece-kuce

Ƙoƙarin Amurka Na Ganin An Haramta Shari’a A Nijeriya Ya Haifar Da Cece-kuce

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.