ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Taklamakan Zuwa Sahara: Yadda Hamada Ke “Haifar” Da Fata

by Sulaiman
3 months ago
Hamada

Jama’a, ko kun taba ganin furannin Rose da suka bude a cikin hamada? Lallai yanzu haka, a gundumar Yutian da ke yankin Hetian na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, furannin Rose na budewa a filayen hamada masu fadin kadada kimanin dubu 80. Manoma suna cikin farin ciki saboda girbin da suka samu a wannan yankin da a baya ta kasance ba ta da amfani, kuma ana fitar da kayayyakin da aka sarrafa da furannin Rose da aka girbe daga nan zuwa sassan duniya. Wadannan furanni, ba kawai suna samar da yanayi mai ni’ima ba ne, har ma suna ba da amsa ga wata tambayar da yankunan da ke fama da kwararowar hamada a duniya ke fuskanta, wato ta yaya ake hada magance kwararowar hamada da kawar da talauci, da daidaita muhalli da inganta rayuwa waje guda?Taklimakan ta kasance hamada mafi girma a Sin, kuma hamada ta biyu mafi girma a duniya da ke motsi, kuma yankin Hetian daidai yake a kudancin iyakar hamadar.

A sassan kudancin hamadar da aka fi samun iska mai karfi, tuddan rairayi su kan mamaye dausayi da kimanin mita 2 zuwa 5 a kowace shekara, kuma yadda za a tsayar da hamadar babban aiki ne da jihar ta Xinjiang ke sanyawa gaba wajen kiyaye muhalli. Bisa kokarin da masanan yaki da kwararar hamada da ma mazauna wurin suka shafe gomman shekaru suna yi, daga karshe suka cimma nasarar kewaye hamadar da wani shingen itatuwa mai tsawon kilomita 3,046 a ranar 28 ga watan Nuwamban bara, shingen da ya kasance irinsa mafi tsawo da aka kafa a duniya. Furannin Rose da suka bude kwanan nan kuma, sun kasance sashe na karshe na wannan babban aiki.

Amma me ya sa aka zabi dasa Rose? A hakika an hada magance kwararowar hamada da inganta rayuwar al’umma bisa dashen furannin. A baya, a kan shuka nau’o’in bishiyoyin da aka san su da sunayen Haloxylon da red willow, don neman cimma burin tsayar da yashi. Sai dai ban da tsayar da yashi, ba a samun komai daga yashin, don haka, al’ummar wurin ba su da himmar aikin, kuma da wuya a daidaita matsalar talauci da al’ummar suke fuskanta. Sauye-sauye sun faru ne sakamakon canjin tunani, wato ko za a samar da arziki daga yashin? Bisa nazarin da masu binciken kimiyya na wurin suka yi a kan hamada, da bugawar iska da ma yanayin ruwa na wurin, sun gano dabarar dasa furannin Rose da suke iya jure yanayin hamadar.

ADVERTISEMENT

Daga nan kuma, gwamnatin wurin ta fitar da manufar da ta hada aikin yaki da kwararar hamada da samun karin kudin shigar al’umma, don ba manoma kwarin gwiwar dasa bishiyoyin Rose, inda gwamnati ta ba manoman kudin tallafi na kimanin yuan(kudin Sin) 1500 a kan gona mai fadin eka 0.07, sa’an nan ta shigar da jerin masana’antu na samar da nau’o’in kayayyakin da ake sarrafawa da furannin Rose. Misali man Rose da shayi da sauransu, matakin da ya samar da kudade kimanin yuan miliyan 230 a gundumar Yutian a shekarar 2025, baya ga samar da karin kudin shiga ga al’ummar wurin sama da dubu 15. Matasan da a da suke fita ci rani sun koma, kuma an gina makaranta da asibiti da sabbin gidaje a wurin.

Sakamakon wannan tsari na “samar da arziki daga aikin inganta muhalli, kuma kara inganta muhalli bisa arzikin da aka samu”, an kawo karshen yadda gwamnati ke kashe kudade marasa iyaka ga aikin kare kwararowar hamada. A maimakon haka, aikin ya zama “sana’a mai riba” ga manoma. Manoma suna mayar da matukar hankali a kan aikin noman furannin, domin su ne tushen samun kudinsu. A sa’i daya kuma, furannin sun zama shingen da ke hana iska da yashi. Muhalli da rayuwa, sun hadu sosai a cikin gonakin.Ba a kasar Sin kadai ba ce, kwararar hamada kalubale ne ga kasashen duniya baki daya. A nahiyar Afirka, matsalar ta dade tana addabar kasashen yankin Sahel. A kasar Mauritania, kusan kashi 2/3 na fadin kasar na cikin hamadar Sahara, kuma matsalolin fari da kwararar hamada suna haifar da munanan illoli ga ci gaban kasar. Sai dai yanayin ya fara sauyawa. A kauyen Bir El Barka na yankin Trarza da ke yammacin kasar, an shimfida bututun ban ruwa nau’in ‘drip irrigation’ a Turance, ga shi kuma tsiron ganyayen lambu sun fito daga gonar rairayi. A gefen gonar kuma, allunan samar da wutar lantarki ta hasken rana suna samar da lantarki ga famfuna don fitar da ruwa daga karkashin kasa zuwa gonaki. Lallai wannan lambun nune-nunen fasahohin yaki da kwararar hamada na tsakanin Sin da kasashen Afirka reshen kasar Mauritania ya kayatar sosai.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A can wajen, bisa gudummawar da masanan kasar Sin suka bayar, an mai da hamadar ta zama dausayi bisa ingantattun fasahohi na kasar Sin, har ma an kai ga yin gwajin shuka nau’o’in amfanin gona tare da samun girbin wasunsu. Sai kuma a arewacin Nijeriya, masana kimiyya na kasar Sin sun bullo da wani tsarin gandun daji wanda ya hada da bishiyoyi masu saurin girma da ciyayi, don kare kwararar hamada.

An kuma yi la’akari da kudaden da bishiyoyin ke iya samarwa ga mazauna wurin a yayin da aka zabi nau’o’insu, don a sa’i daya su samar da kariya ga muhallin wurin, a daya bangaren kuma, su samar da karin kudin shiga ga mazauna wurin. Lallai al’amuran sun sake shaida cewa, muhallin zama da rayuwar al’umma ba su sabawa da juna ba. Sinawa tun zamanin baya na ganin cewa, samun dadi ga kowa shi ne dadi na gaske. Daga Taklimakan zuwa Sahara, kasar Sin na raba dabararta ta “samar da arziki daga aikin inganta muhalli da kara inganta muhalli bisa arzikin da aka samu” ga kasashen Afirka, sabo da ko da yaushe suna tare a aikin yaki da kwararowar hamada, kuma suna samun karin nasarorin a zo a gani bisa hadin gwiwarsu.

Hamada
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
  • Sulaiman
    Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
  • Sulaiman
    Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
  • Sulaiman
    2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Liu Guozhong Ya Halarci Taron Koli Kan Yadda Kasashen Afirka Za Su Fuskanci Cutar Ebola

Liu Guozhong Ya Halarci Taron Koli Kan Yadda Kasashen Afirka Za Su Fuskanci Cutar Ebola

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.