ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

by Abubakar Abba
5 days ago
NPA

Hukumar Kula da sufurin Jiragen Ruwa ta kasa wato NPA, ta kawar da duk wani shakkun da wasu ke tunanin cewa, za a rinka gudanar da ayyukanta da ke kamanceceniya, da sabuwar hukumar sanya ido kan kula da tattalin arzikin tashoshin Jiragen Ruwa wato NPERA.

Kazalika, NPA ta kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin tabbacin cewa, babu wani batun cewar, hukumomin za su kasance, suna gudanar da ayyukan su iri daya a karkashin sabuwar hukumar ta NPERA.

Wannan tabbacin, NPA ta tabbatar da shi, na zuwa ne, biyo bayan, damuwar da wasu suka nuna a fannin na cewar,  mai yawa hukumar NPA da kuma sabuwar hukumar ta NPERA, za su kasance, suna gudanar da ayyukan su, da ke kamanceceniya da juna, musamman duba da cewa, tuni sabuwar hukumar ta NPERA, ta fara gudanar da ayyukan ta.

ADVERTISEMENT

Babban Janar Manaja na sashen samar da bayanai da tsare-tsare a hukumar ta NPA Ikechukwu Onyemekara, ya bayar da wannan tabbacin a madadin hukumar ta NPA.

Ikechukwu ya sanar da hakan ne, a jihar Legas a yayin tattaunawa da kungiyar ‘yan jarida, da ke dauko rahotannin fannin shige da ficen kaya a tashoshin Jiragen Ruwan kasar wato SCAN.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

A cewar Ikechukwu hukumar ta NPA, da kuma sauran hukumomin gwamnatin tarayya, da su ne, aka tattauna kan batun yin nazarin kirkiro da wannan sabuwar hukumar ta NPERA.

Ya ce, an gudanar da tattaunawar ce, tun kafin a mika batun kirkiro da hukumar, ga shugaban kasa, domin ya sanya hannu ta zama hukuma, wadda a yayin tattaunawar, sai da aka tabbatar da cewa, ayykuan hukumomin biyu, ba su karo da juna ba.

A cewar Ikechukwu, Babban Ministan kula da bunkasa fannin tattalin arziki Teku Adegboyega Oyetola, na yawan nanata karfafawa hukumomin gwamnati, da ke a karkashin kulawar ma’aikatar sa, guiwa, musamman domin su rinka yin aiki kafada da kafada da juna, domin kowannensu, ya sauke nauyin da aka dora masa.

“Maigirma Minista Adegboyega tare da kuma shugaban  hukumar NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, na ci gaba da tabbatar da cewa, daukacin hukumomin na gwamnatin, na ci gaba da gudanar da ayyukan su, ba tare da wata tangarda ba“.  a cewar Ikechukwu.

“Ina sane da cewa, tun kafin a gabatar da kudurin kirkiro da wannan sabuwar hukumar ta NPERA, daukacin hukumomin na gwamnatin na karbar umarni ne daga gun babban ministan Adegboyega, inda kuma aka tabbatar da an yi nazari kan duk wani abu, da zai iya janyo wani taranaki, wajen gudanar da ayyukan hukumomin biyu,” inji shi.

Ikechukwu ya ci gaba da cewa, babbar manufar da gwamnatin tarayya ke son cimma shi ne, na kara tabbatar da ganin ana gudanar da ayyukan ta yadda suka kamata da kuma kara tabbatar da gudanar da yin gasa a tsakanin tashoshin Jiragen Ruwan kasar, amma ba wai, batun haifar da rudani a tsakanin hukumomin gwamnatin da kuma a fannin sufurin Jiragen Ruwan kasar ba.

“Babu wani batun nuna damuwa, kirkiro da wannan sabuwar hukumar ta NPERA, abu ne mai kyau kuma hukumar NPA, ba ta wata matsala kan kafa sabuwar hukumar“. a cewar Janar Manajan.

“Babu ta yadda za a ce, gwamnati, ta kirkiro da wani abun da zai iya janyo haifar da matsala a dukkanin fannoninta, na bunkasa tattalin arzikin kasar amma babban kamata,  gwamnatin shi ne a rinka gudanar da daukin ayyukan ta, yadda suka kamata in ji Ikechukwu.

Bugu da kari, hukumar ta NPA ta kara tabbatar da cewa, tuni shirye-shiye sun kai matakin fara gudanar da yiwa kayan aikin tashoshin Jiragen Ruwan da ke a Jihar Legas, garanbawul, wanda kuma ake sa ran, fara gudanar da ayyukan na Apapa.

Ikechukwu ya bayyana cewa, a yanzu haka hukumar ta NPA, na kan ci gaba da gudanar da wayar da kan alumomin da ke da zama a daura da tashoshin Jiragen Ruwan kasar tashoshin kan mahimmancin ayyukan da hukumar ta NPA, ke son aiwatarwa, musamman, wadanda ke a kusa da inda za a fara gudanar da ayyukan.

“A yanzu haka, muna kan ci gaba da wayar da kan alumomin da ke zaune, a daura da tashoshin Jiragen Ruwan na jihar Legas, musamman duba da cewa, da zarar an fara gudanar da ayyukan za su fara jin kara, wanda hakan ya zama wajibi, mu dukufa, domin wayar masu da kai, kan ayyukan da za mu fara gudanar wa, ” a cewar Janar Manajan.

Janar Manajan ya kara da cewa, domin a ci gaba da gudanar da ayyuka a tashishin, za a gudanar da aikin ne, kasha-kashi.

“Za mu gudanar da aikin kashi-kashi ne, domin ba mu son gudanar da ayyuka a tashsohin, su tsata cak, wanda hakan zai bai wa Jiragen Ruwan, ci gaba da gudanar da zirga-zirgarsu, ba tare da wata tangarda ba,” Inji shi.

Da yake yin tsokaci kan kiraye-kirayen da ake yi na a dauki matasan a yankunan daura da tashoshin aikin wucin gadi, ya bayar da tabbacin  cewa, NPA za ta dauke su, domin yin kananna ayyuka, na wucin gadi.

“Ina bayar da tabbacin cewa, akwai wasu ‘yan kannan ayyuka da za a dauki matasan, amma na wucin gadi,”.

Kan batun korafin cewar, Ma’ikatar bunkasa fannin tattalin arziki Teku NPA ta ta fi mayar da hankalinta wajen bunkasa Tashar jihar Legas Ikechukwu, ya sanar da cewa, ayyukan sun hada har da na tashoshin Jiregn Ruwa da ke Gabashin kasar.

Ya kara da cewa, a kwanan baya Minista Adegboyega, ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta amince da a fara gyran tashoshin Jiregn Ruwa, na Gabashin kasar.

Ya ci gaba da cewa, wannan daukin na gwamatin, na daga cikin shirye-shiryenta na kara bunkasa kayan aikin da ke a tashoshin daukacin facin kasar, ba wai kawai, na Legas ba.

“Ba da dadewa ba Ministan ya sanar da cewa,  gwamnatin, ta amince da a fara gudanar da gyare-gyaren kayan aikin,  na wasu tashoshin Jiragen Ruwan kasar, ciknsu har da na Gabashin kasar, “ A cewar Manajan.

A cewarsa, koda yake dai, a yanzu, zai yi wuya tashohin na Gabashin kasar, su amfana da irin garabasar da tashoshin Jiren Ruwa na jihar Legas, suka samu, musamman, duba da irin matukar mahimmancin da suke da shi, ga alumomi da kuma masana’antun da ke a yankunan.

NPA
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Dangote
Tattalin Arziki

Matatar Man Ɗangote Ta Samu Ƙarin Ribar Dala Biliyan 2.5 A Ɓangaren Zuba Jari

August 1, 2026
Next Post
NPA

Dajin Sambisa Ya Kai Girman Ƙasar Belgium – Ministan Tsaro

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.