ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

by Abubakar Abba
2 weeks ago
Kannywood

Abotaka a tsakanin ‘yan Adam, wata abace, da ake fatan ci gaba da yi a tsakanin abokai, har  iya tsawon rayuwarsu.

Wannan batun ya taso ne, in aka yi la’akari  da cewa, a wasu lokutan, musamman ma a masana’antar Kannywood a kan samu sabani, a tsakanin, jarumi ko jaruma musamman ma wadanda suka yi matukar  shahara, a masana’antar da wani abin kan bijero, ya shiga tsakaninsu, har abotakarsu ta samu matsala.

An kwashe shekaru ma su yawa, irin wadannan jaruman abotakarsu da ta kai matakin makura har ma tamkar sun zama ‘yan uwan juna ne, ana ganin, babu abin da zai  iya haddasa wani sabanin abotakarsu.

ADVERTISEMENT

Kazalika ma, irin wannan abotakar, ta kan kai ga matakin daya na iya kare mutunci da kimar  dayan, a duk wata irin sarkakiyar da daya ya samun kansa a ciki, inda a wasu lokutan, jarumi ko jaruma,  kan gina sana’a tare.

Sai dai kuma duk da hakan, idan mai aukuwa ta auku, jaruman su kan shiga ‘yar tsama da juna, wanda hakan, ke kawo sabanin abotakar ta su.

LABARAI MASU NASABA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

Dalilan Da Suka Sa Ba Zan Iya Auren Ɗan Film Ba —Bilkisu Bishasha

A wasu lokutan ma, rashin jituwar, kan kasance a asirce ne, wasu lokutan kuma ta kai ga har ta bayyana, a sarari ana gani.

Dangantaka a tsakaninsu, na kasancewa ne, ta hanyar yin biyayya, fahimtar juna da kuma taimakawa juna, musamman a yayin da daya daga cikinsu, ya shiga cikin wata chakwakiya.

Amma idan wani sabani, ya shiga tsakaninsu, inda har ta kai su ga, yin baran-baran da juna.

Takun sakar a tsakanin, har ta kai ga, miliyoyin masoyansu kan tofa na su albarkacin bakin, musamman ma maganar zarge-zarge, wadanda hakan ke kara yin tasiri ga kara abotakar jaruman da hakan ta faru da su.

Rahotannin sun nuna cewa, a shekarun da suka wuce, batun lalacewar abotaka a tsakanin wasu jarumai, maza da mata a masana’antar, ta zamo abin tattaunawa, a tsakanin masu bibiyar masana’antar.

Bugu da kari kuma, tattaunawar ta fi yin kamari, a shafukan sada zumunta na zamani. Wasu daga cikin masoya bayan jaruman, su kan yi mamaki, kan lalacewar abotar, idan aka yi la’akari da cewa, a baya, za a ga jarumi ko jaruma, sun kasance, abokai na kut-da kut, tare da yi wa junansu, biyayya.

A nan, za mu yi nazari kan wasu daga cikin jarumai da juruma a Kannywood, da suka tsinci kansu, a cikin wannan maudu’in

Ali Nuhu Da Adam A. Zango:

Fitattun jaruman Ali Nuhu da Adam A. Zango na daya daga cikin irin abotakar da ake zargin ai ta samu sabani.

Jaruman biyu, tun farkon tasowarsu, a Kannywood, aminan juna ne, wanda hakan, ya kara sanyawa, suka yi matukar tashe, a masana’antar.

Sai dai, an yi zargin cewa, abotarsu ta fara yin baya ne a 2019, inda hakan har ta kai ga, masoyansu, suka fara ganewar hakan.

Duk da kokarin da wasu masoyansu suka yi, na sulhunta su, an yi zargin cewa, har yanzu suna ci gaba da zaman Doya da Manja.

Momee Gombe Da mawaki Hamisu Breaker:

Su ma ana zargin, suna a cikin irin waccan da’irar , jaruma Momee Gombe da mawaki Hamisu Breaker, sun shafe shekaru, a matsayin abokan juna.

A lokacin suna danyen Ganye, an sha ganinsu, a cikin faifan bidiyo suna rera waka tare kuma su kan halarci taruka tare.

Masu bibiyarsu, sun sha famar yin tsegumi, cewar, abotaka a tsakaninsu, ta fara yin tsami.

A baya, saboda irin abotakarsu, har ana yi  masu kallon masoya ne, sai dai kuma, sun sha karyata hakan.

Sai dai, kuma ana ganinsu a taruka a shekarun baya, amma irin hakan ya ragu, ba kamar yadda, aka saba ganinsu ba a shekarun baya.

Abubakar Bashir Maishadda Da Alhaji Sheshe:

Wadannan fitattun jaruman, shakikan abokai ne, a sheakarun baya, sai dai, ana zargin abotarsu, ta fara samun nakasu.

A baya, sun yi aiki a tare a fina-finan da suka hada da kamar irin na Ana Dara Ga Dare da Mariya.

An yi ta rade-radin cewa, abotakarsu ta fara raguwa ne, bayan Maishadda, ya bude wata sabuwar kasuwar da ake zargin cewa, Sheshe ya kauracewa, inda hakan ya fara jefa shakku, a zukatan masoyansu.

Sai dai kuma, daga baya, sun sake haduwa a wasu wuraren daukar fim da kuma a wasu taruka, wanda hakan ya nuna cewa, tamkar, an samu damar sasanta su ne.

Domin a fahimci yadda ake samun lalacewar abotaka a masana’antar a tsakanin wasu jaruman ko jaruma, mai fashin baki a masana’antar Sharif Yusuf, yayi karin haske kan lamarin, sai dai, ya yi nuni da cewa, batun ya danganta ta yadda aka faro shi.

“Samun sabani wani abu ne, da za a iya warwarewa, a cikin ruwan sanyi, amma a Kannywood, masana’anta ce, da al’ummar gari, musamman masoya, ke bibiya sau da kafa, “ inji Yusuf.

Ya ce, ba wani sabon abu ba ne, a lura da samun sabani a tsakanin jarumi da jaruma, a Kannywood ba, inda ya kara da cewa, masu kafafen sada zumunta na zamani su ma suna kara ruruta wutar hakan, idan wata rashin fahimta, ta auku a tsakanin jarumi da jaruma.

“Abotaka a tsakanin jarumi da jaruma, na samo asali ne, ta hanyar yin hadaka ko kuma gudanar da aiki, tare, “cewar Sharif.

“Masana’antar Kannywood, cike take da gasa da ban da ban, inda za ka ga, abokai, a masana’antar, musamman ma wadanda suka shaku da juna, na neman wata dama, da tayi kama, ko neman wata bukatar karramawa da wata lambar yabo ko sahalewar wata dama wanda hakan ke janyo, samun sabanin abotaka a tsakanin jarumi ko jaruma,” a cewarsa.

A cewarsa, koda kuwa akwai kyakkyawar fahimtar abotaka a tsanin jarumi ko jaruma, matsala na iya kunno kai a tsakaninsu.”

Ya ce, gasa a tsakanin jaruman na kara taka gagarumar gudunmawa, wajen samun sabani a tsakaninsu, inda ya kara da cewa, samun kudade, neman kwangila, suma na taimaka wa.

Ga masoyansu, idan hakan ta auku, su kan nuna rashin jin dadinsu, musamman ma idan rashin jituwar, ta zamo ta hakika.

Akasari ma, idan har aka samu wata rashin fahimta, musamman a tsakanin jarumi ko jaruma da suka yi shura a masana’antar Kannywood, duniya na nan a gefe, ta sanya ido, tana kallo.

Kannywood
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

MASU ALAKA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
Nishadi

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

September 5, 2026
Kannywood
Nishadi

Dalilan Da Suka Sa Ba Zan Iya Auren Ɗan Film Ba —Bilkisu Bishasha

August 23, 2026
Nishadi

Tazarcen Tinubu A 2027: Bai Kamata A Yi Wa Ƴan Kannywood Kuɗin Goro Ba —Na Buraska

August 16, 2026
Next Post
Kannywood

Sabon Ɗan Wasan Man-United Baleba Zai Shafe Makonni Uku Yana Jinya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.