ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
3 months ago
Bindiga

Ƴan bindiga sun sake tilasta wa mazauna ƙauyuka 26 a Ƙaramar Hukumar Sabon- Birni da ke Jihar Sakkwato biyan kuɗaɗen haraji domin tsira da rayukansu, wajen ba su damar zuwa gonakinsu.

Majiyoyi daga yankin a gabascin Sakkwato sun bayyana cewa barayin dajin sun bayar da wa’adin kwanaki uku tare da gargaɗin manoma da su guji zuwa gonakinsu har sai sun biya kuɗin da suka buƙata.

Lamarin ya biyo bayan shigowar daminar bana wanda hakan babban ƙalubale ne kuma babbar barazana ga noma wajen samar da wadataccen abinci a yankin, wanda al’ummar suka bayyana cewa ƴan bindigar sun yi alwashin kisa ko sace duk waɗanda suka saba wa umurninsu a yayin wa’adin.

ADVERTISEMENT

Garuruwan da lamarin ya shafa sun haɗa da Garin- Faji, Cina Barka, Zululu, Ɗan- Gari, Garin- Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin- Ganga, Ɗan- Kware, Garje, Dogon -Faru, Son- Allah, Garin- Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin- Labo, Zango, Kaifin- Aska, Tsauna -Dogo, Tudun- Wada, Rambaɗawa, Ga- Itace, Nasarawa da Garin Idi.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya bayyana cewar umarnin ya haifar da tsoro a tsakanin manoma da ke shirin fara noman bana, yana cewa sun ce duk wanda aka kama yana noma, ko dai a kashe shi ko a sace shi, kuma ba zai samu ƴanci ba sai ya biya kuɗin fansa na naira 500,000. Ya ce tuni suka fara tattara kuɗaɗe domin biyan harajin.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Wani mazaunin ƙauyen Zululu wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gonarsa ranar Juma’a ne lokacin da ya ji labarin wannan umarni.

Ya bayyana cewa ƴan bindigar sun umarci mazauna yankin da su dakatar da duk wasu ayyukan noma na tsawon kwanaki uku har sai ƙauyukan da abin ya shafa sun biya harajin da ake ƙaƙaba masu.

A cewarsu, jami’an tsaro na ƙwace dabbobinsu, suna jaddada cewa ba za a yi wani aikin noma ba har sai an biya harajin da aka ƙaƙaba masu tare da cewa suna tsammanin sarakunan gargajiya da malaman addini za su haɗu su tattauna da barayin dajin domin sanin adadin kuɗin da kowane ƙauye zai biya.

Ya ce “Muna biyan kuɗi kafin mu fara noma, sannan wani lokaci bayan kowane watanni biyu ko uku sai su sake zuwa. Ko bayan mun biya yanzu, za su iya dawowa bayan kusan watanni uku su ce babu wanda zai girbi gero har sai an sake biyan wani haraji.

Bindiga
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ posts Bio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato
Bindiga
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.