ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ACF Ta Ƙaddamar Da Gidauniyar Tallafa Wa Ilimi A Arewa

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
ACF

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta ƙaddamar da wani kwamiti na musamman kan Kuɗaɗen Tallafi (Endowment Fund Committee) domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, bunƙasa ilimi, da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai na zamantakewa da tattalin arziki a faɗin Arewacin Nijeriya.

Tsohon Babban Sufeton Ƴansandan Nijeriya, Mohammed Dikko Abubakar (MD Abubakar) ne ke jagorantar wannan kwamiti, inda ake sa ran zai samar da ingantaccen jagoranci na fuskantar nasara da kuma sanya ido kan aiwatar da manufofin gajiyar da asusun.

Yayin da yake jawabi a gurin ƙaddamarwar ranar Talata, Shugaban ƙungiyar ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya bayyana cewa kafa wannan kwamiti wani gagarumin mataki ne na faɗaɗa damar samun ilimi, tallafa wa ci gaban al’umma, da kuma inganta ɗorewar ci gaba a yankin Arewa.

ADVERTISEMENT

Dalhatu ya bayyana cewa asusun tallafin zai zama dandamali na magance manyan ƙalubalen ci gaba da ke fuskantar Arewacin Nijeriya.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta taɓa ƙaddamar da Asusun Tallafi na Naira Biliyan 100

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

yayin bikin cikar ta shekaru 25 (Silɓer Jubilee), inda ya lura cewa duk da cewa masu taimako sun yi alƙawarin bayar da Naira Biliyan 7.8, Naira Biliyan 3.9 kacal aka iya karɓa zuwa yanzu.

A cewarsa, kuɗaɗen da aka karɓo ɗin suna nan ajiye cikin amana a wani asusun banki da ke (Jaiz Bank).

“Kuɗin suna nan lafiya ƙalau, kuma muna sa ran kwamitin ba wai kawai zai ƙaddamar da shirye-shiryen ayyukan jinƙai masu amfani a faɗin Arewa ba, har ma zai ƙarfafa gwiwar waɗanda suka yi alƙawuran baya domin su cika su. Kyawawan ayyukan da za mu yi da kuɗaɗen da muke da su a halin yanzu tabbas za su janyo hankalin mutane su ƙara ba mu wasu kuɗaɗen,” in ji shi.

Ayyukan da ke gaban kwamitin

Ana sa ran sabon Asusun Tallafin zai tara kayan aiki da kuɗaɗe domin: Shirye-shiryen bunƙasa ilimi. Tallafa wa matasa. Koyar da dabarun jagoranci.

Sauran ayyukan da ke da nufin inganta rayuwa da walwalar al’ummomi a faɗin Arewacin Nijeriya baki ɗaya.

ACF
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Birtaniya Da Nijeriya Sun Ƙulla Yarjejeniya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

Birtaniya Da Nijeriya Sun Ƙulla Yarjejeniya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.