ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dan Majalisar Wakilai, Ali Isa JC, Ya Fice Daga PDP

by Muhammad
5 months ago

Mai riƙe da muƙamin Minority Whip a Majalisar Wakilai, Hon. Ali Isa JC, ya yi murabus daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yana mai danganta hakan da rikicin cikin gida da kuma abin da ya kira rashin bin ƙa’idar dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Afrilu, 2026, wadda aka aika wa shugaban mazabar Kindiyo da ke ƙaramar hukumar Balanga a Jihar Gombe, Isa JC ya ce matakin nasa ya fara aiki nan take.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar mazaɓar Balanga/Billiri a Majalisar Tarayya, ya bayyana cewa ficewarsa ta samo asali ne daga damuwa kan yadda ake tafiyar da jam’iyyar, yana mai zargin cewa wasu ƙarfi sun kwace iko da tafiyar da ita ta hanyar da ta saɓa da manufofinta na asali.

ADVERTISEMENT

Ya ce: “An tilasta min ɗaukar wannan mataki ne sakamakon yadda wasu ƙungiyoyi marasa bin ƙa’idar dimokuraɗiyya suka ƙwace jam’iyyar domin manufofi da suka saɓa da ginshiƙanta, lamarin da ya haifar da shugabanci mai ɓangarori.”

Isa JC ya ƙara da cewa ya yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa mai zurfi da iyalansa, abokan siyasa, da sauran masu ruwa da tsaki.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Bayan tattaunawa mai zurfi da iyalaina, abokan siyasa, da sauran masu ruwa da tsaki, na fahimci cewa makomata ta siyasa, da kuma ta al’ummar da suka ba ni amanar wakilci, ba ta cikin PDP,” in ji shi.

Ya jaddada cewa fifikonsa shi ne jin daɗin al’ummar mazaɓarsa da kuma ci gaban siyasarsu, yana mai cewa akwai buƙatar samun wani dandali mafi dacewa domin kare muradunsu.

“Na yi imanin cewa al’ummar mazaɓata sun cancanci wani dandali da zai fi kare muradunsu da makomarsu ta siyasa,” ya ƙara da cewa.

Duk da ficewarsa, Isa JC ya gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi na wakiltar al’ummarsa a Majalisar Tarayya.

“Ina miƙa godiyata ga shugabanni da mambobin jam’iyyar da suka ba ni dama ta wakiltar al’ummar Balanga/Billiri. Zan ci gaba da kasancewa mai godiya a gare ku, ina kuma yi muku fatan alheri,” in ji shi.

Ficewar tasa na ƙara jaddada damuwar da ake da ita kan rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar PDP, yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Harba Rokar Lijian-1 Y12 Dauke Da Taurarin Dan Adam Takwas

Sin Ta Harba Rokar Lijian-1 Y12 Dauke Da Taurarin Dan Adam Takwas

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.