Taron Dattawan Hawul da Askira-Uba na jihar Borno, gami da iyalan waɗanda abin ya shafa, sun fashe da kuka tare da nuna matuƙar damuwa a yayin da suka yi kira na musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamna Babagana Umara Zulum. Sun roƙi shugabannin da su gaggauta ɗaukar matakin ceto mutane 116 da suka haɗa da ɗalibai 78 da wasu mutane 38 da suka kwashe kwanaki 100 cif suna hannun masu garkuwa da mutane.
Da ya ke jawabi a madadin dattawan a taron manema labarai da suka gudanar a Abuja a ranar Juma’a, Sakataren ƙungiyar dattawan, Malla Gadzama, ya bayyana cewa ɗalibai 42 na makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba an sace su ne tun ranar 15 ga watan Mayun 2026. Ya koka da cewa iyalan waɗannan yara sun shafe kwanaki 100 na raba-ido, da baƙin ciki, da tsoro, da kuma fargaba marar musaltuwa. Gadzama ya kuma tunatar da yadda aka sace wasu dalibai da malamai a jihar Oyo a ranar ɗaya, amma tuni aka ceto su, saɓanin nasu na Borno da har yanzu suke tsare a jeji.
Sakataren dattawan ya yi kira ga Gwamna Zulum da ya yi amfani da dukkan ƙarfin ofishinsa don haɗa kai da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro wajen gano mutanen. Haka zalika, wani ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Askira-Uba da Hawul, Hon. Midala Balami, wanda shi ma yana cikin tawagar taron, ya koka kan rashin taɓuka abin kirki daga ɓangaren gwamnati duk da cewa ya gabatar da batun a gaban zauren majalisar tarayya a matsayin lamari mai matuƙar muhimmanci a lokacin da abin ya faru. Ya nemi gwamnati ta tashi tsaye wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa, wanda hakan shi ne babban nauyin da ya rataya a wuyanta.
A wani ɓangaren kuma, Gwamna Babagana Zulum ya karɓi bakuncin wasu daga cikin iyalan yaran na garin Mussa a gidan gwamnati da ke Maiduguri a ranar Juma’a, inda ya kwantar musu da hankali tare da tabbatar musu da cewa gwamnati na ci gaba da aikin ganin an ceto yaran nasu lami lafiya. Gwamnan ya isar da sakon jaje daga Shugaba Tinubu sannan ya tabbatar da cewa shugaban ƙasar ya riga ya ba jami’an tsaro umarnin ceto dukkan waɗanda lamarin ya shafa.
Wannan batu dai na ci gaba da janyo hankalin al’umma, yayin da iyalan da abin ya shafa suke ci gaba da zura idon ganin ranar da za a ceto ƴaƴansu da sauran ƴan uwansu daga wannan halin kuncin.














