DPO din ‘yansanda na karamar hukumar Jahun a Jihar Jigawa, SP Abubakar Musa ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa ya rasu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adamu ne ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ya raba wa manema a ranar Asabar.
- Wasu Daga Cikin Manhajojin Da Ke Bata Wayar Android
- Alex Ampaabeng:Matakan Yaki Da COVID-19 Na Sin Za Su Taimaka Wajen Dawo Da Tsarin Samar Da Hajoji A Duniya
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 9:00 na dare a ofishin DPO din da ke sashen Jahun bayan doguwar jinya.
A cewarsa, “SP Abubakar Musa ya rasu jiya da misalin karfe 9:00 na dare a lokacin da yake bakin aikinsa.”
Ya bayyana cewa an garzaya da marigayin zuwa babban asibitin Jahun wanda daga bisani aka ka shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Emmanuel Ekot Effiom ya jajantawa iyalan mamacin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp