ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

DSS Ta Kama Mutane 5 Da Ake Zargi Da Hannu A Satar Ɗaliban Makaranta A Neja

by Sadiq
3 months ago

Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta kama mutane biyar, ciki har da ‘yan ƙasar Nijar biyu, bisa zargin samar da makamai ga ‘yan bindigar da suka sace ɗalibai da ma’aikatan Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke garin Papiri a Jihar Neja a watan Nuwamban 2025.

Hukumar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-103 guda 15, mujallu 15 da harsasai 1,434 a yayin samamen.

Majiyoyin tsaro sun ce an kama Yusuf Mohammed, wanda aka fi sani da Bature, da Mubarak Ibrahim a kan hanyar Zariya zuwa Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta karɓo makamai.

ADVERTISEMENT

Bincike ya kai ga kama Goni Ibrahim, wani dillalin makamai daga yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar, da abokinsa Tukur Sani.

Daga baya kuma an kama Alhaji Adamu, wanda aka fi sani da Gado Banufe, a Yauri ta Jihar Kebbi.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Ana zarginsa da samar da makamai ga masu aikata laifuka a yankin.

Jami’an tsaro sun ce bincike ya nuna cewa mutanen biyar ɗin na cikin masu kai wa ‘yan bindigar da suka kai hari makarantar makaman da suke amfani da su.

A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, ‘yan bindiga sun kai hari makarantar tare da sace ɗalibai da malamai da dama.

Yayin da wasu suka tsere, sun sace sama da mutum 250 zuwa dajin Kainji.

Daga bisani, a ranar 21 ga watan Disamba, 2025, gwamnati ta tabbatar da ceto tare da dawo da sauran mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya.

A gefe guda kuma, Ƙungiyar Kiristocin Arewa (NCA), ta yaba wa DSS da Darakta-Janar ɗinta, Oluwatosin Ajayi, kan kama waɗanda ake zargin.

Shugaban ƙungiyar, Joseph John Hayab, ya ce ya kamata a riƙa yaba wa hukumomi idan sun samu nasara, kamar yadda ake sukar su idan sun gaza.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 12, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato

Sabon Hari Cikin Dare: Mutane 5 Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata A Filato

LABARAI MASU NASABA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.