Jihohi yanzu a faɗin tarayyar Nijeriya suna amsar ku san kuɗaɗen da suke amsa sau ɗaya a shekarun baya yanzu an ƙara masu kasi biyu ne, abinda gaba ɗaya hakan ya nuna kowace Jiha tana samu kashi uku maimakon kashi ɗaya a shekarun da suka gabata, manufa anan ita ce irin kason da suka samu daga Gwamnatin tarayya ya ƙaru, sai dai kuma kamar yadda ƴan ƙasa suka ce duk da irin maƙudan kuɗaɗen da suka amsa,ƙuncin rayuwa da tsadar sai ƙaruwa ta ke yi kowace rana.
Tun ranar da Shgaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin manfetur bayan da aka kammala rantsarda shi wato 29 ga Mayu 2023, daganan kuma aka ɓullo da tsarin da Naira ita ce za ta ƙwaci kan ta a kasuwa, bugu da ƙari kuma kuɗaɗen da ake rabawa tsakanin Gwamntocin tarayya, Jihohi,da kuma ƙananan Hukumomi sun ƙaru matuƙa, musamman ma idan aka kwatanta irin kuɗaɗen da ake rabawa kafi a cire tallafin manfetur. Yayin da Jihohi suka amshi Naira Tiriliyan 3.35 a 2022, sai ga shi sun samu Naira 8.19 Tiriliyan a shekarar 2025.
A Jihohin Kano, Legas, Taraba, Zamfara, Kogi da Akwa inda wakilai suka tambayi ɗimbin mazauna Jihohin, ma’aikata da ƴankasuwa waɗanda suka koka akan irin matsalar tattalin arziki wanda ya shafi tsadar rayuwa duk kuwa da yake kuɗaɗen shi ga daga Gwamnatin tarayya sun ƙaru.
Kanota yi babban samu daga Naira biliyan 99.31 a shekarar 2022 zuwa Naira bilyan 279.69a shekarar 2025; Legas ma’ ta ƙara samun ci gaban daga Naira Biliyan161.29 zuwa Naira bilyan 531.51;Taraba ma sai ga shi daga Naira biliyan 51.74 zuwa Naira biliyan 157.56; yayin da Zamfara ta samu ƙarin girma daga Naira biliyan 56.62 zuwa Naira biliyan 167.20. Kogi ma ta samu ƙarin girma na kuɗaɗen shiga daga Naira biliyan 60.78 zuwa Naira biliyan 176.24, yayin da Akwa Ibom ita ma ci gaba ta samu daga Naira biliyan 314.18 zuwa Naira biliyan 497.98.
Hakanan toshe ko hana Jiragen ruwa ruwa wucewa ta mashigar– Strait ta Hormuz – abinda ya ke faruwa sanadiyar yaƙin da ake yi tsakanin ƙasashen Iran da kuma Amurka ya sa farashin gangar ɗanyen mai ta tashi daga dala $70 zuwa fiye da dala 100 kuɗin kowace gangar ɗanyen mai ya zarce $100. Irin hakan ya ƙara girman lalitar Gwamnatin tarayya, yayin da kuma su ƴan Nijeriya suna ƙara fuskantar matsananciyar rayuwa sanadiyar ƙarin kuɗin mai, kayan abinci, da kuma zirga- zirga.
Hakanan ma an raba Naira Tiriliyan 2.04 a tsakanin Gwamnatocin tarayya, Jihohi, da kuma ƙananan Hukumomi a watan Maris 2026, wannan ko hakan ya nuna da akwai ƙaruwar Naira biliyan 150 daga Naira Tirliyan 1.89 da aka raba a watan Fabrairu.
An samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga, ne saboda sabuwar dokar Haraji wadda ta maida lamarin ya wuce na yadda, a shekarun baya maganar takarda ce ake yi, amma yanzu yadda kuɗin za su riga shiga ne muraran, sai kuma doka ta 9,da ta hana kamfanonin mai su riƙa turawa Kamfanin kula da albarkatun mai na ƙasa (NNPCL) da kuma Hukumar kula da manfetur da ake samu daga Tudu (NUPRC), inda aka basu umarni na su riƙa biya kai tsaye zuwa asusun ajiya na gwamnatin tarayya.Har ila yau dokar ta hana cire kuɗaɗe daga wasu kuɗaɗen shiga da ake samu daga harkokin mai inda a shekarun baya NNPC tana cire kashi 30.
Duk da yake gwamnatin tarayya t amince da Naira 70,000 a matsayin mafi ƙrancin albashi a watan Yuli 2024,daga Naira 30,000,da wasu Jihohi suke biya, wasu ma na biyan fiye da hakan, duk da hakan ma’aikata suna magannar cewa tsadar rayuwa da yadda darajar Naira take ƙara yin ƙasa albashin ya zama ba wani abu bane kuma.
Duk da haka dai lalacewar darajar Naira yana shafar kuɗaɗen shigar da Gwamnatin tarayya ke samu, masana sun ce Jihohi yanzu suna kuɗaɗe sosai fiye da shekarun baya amma kuma al’ummar suna fama da matsin rayuwa ta uyadda abubuwa suka taɓarɓare.
Bankin duniya a cikin rahoton da yake badawa akan Nijeriya dangane da ci gaban Nijeriya da aka fitar a watan Afrilu 2026, ya nuna cewar lamarin talauci a Nijeriya abin ya yi tashin gwauron Zabo zuwa mutane miliyan 140 a 2025, wanda shi ne kuma kashi 6 na al’ummar Nijeriya.Rahoton mai taken, “Nijeriyar gobe dole ta fara daga yau: An yi magana ne kan rayuwar fako ta yaro,” ya bayyana cewa lamarin fatara ta ƙaru daga kashi 56 a shekarar 2023 zuwa kashi 61 a shekarar 2024.
Hakanan ma a shekarar 2022 wani rahoton da ya shafi Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ya nuna cewa da akwai mutanen da suka kai da akwai mutane miliyan 133 mazauna Nijeriya da suka zama tare da fatara, basu da dama ta yadda za a kula da lafiyarsu,abinci da kuma mallakar gida.
Halin Da Ake Ciki A Kano
Binciken da DailyTrust ta yi a wasu sassan birnin Kano ya nuna cewa samun kuɗaɗen shiga na Jihohi har yanzu abin ba kai ga sun gani a ƙasa ba, har su samu wani sauƙin tafiyar da rayuwa saboda,sun koka ne akan yadda suke yin fafaukar gwagwarmaya domin su samu damar tafiya da yadda halin na ƙasar ya ke,ta yadda za su samu abin baiwa bakin salati.
Wani ma’aikaci a Jihar mai suna, Musa Abdullahi, ya ce an shiga wani halin da albashin shi ba zai iya tafiyar da rayuwar iyalain shi ba.
“Farashi kayan abinci ya ninka idan aka kwatanta yadda suke a shekarar da ta gabata.Ya ce abinda zai saya sun yi matuƙar kaɗan. Muna jin cewa an ƙara kuɗaɗen da ake ba Jihohi kowane wata,amma mu zuwa yanzu ba mu ga wani abinda zai nuna cewar an yi masu ƙarin, haka abin yake tafiya kullun babu wani ci gaba sai kace karatun Ɗankama kamar dai yadda ya furta,”.
Ita ma wata ƙaramar ƴarkasuwa, a kasuwar ‘Yankaba,Zainab Sani, cew ta yi lamarin ya shafi dukkan masu saye da sayarwa.
“Mutane basu sayen kamar shekarun baya. Mu ma masu sayarwar muna ta faɗi tashi ne saboda farashin na kaya kullun ƙaruwa suke yi. Ta ce kuɗaɗen zurga- zurga da na haya sun ƙaru kamar yadda ya ce,’’.
Shi ma waniu mazaunin, Ibrahim Jazuli, wanda shi yana tuƙa Keken NAPEP, cewa ya yi kuɗin mai sun ƙaru, ga kuma yadda kuɗaɗen rayuwar yau da kullun hakan ya sa yana da wuya mutum ya ce zai riƙa ajiye kuɗi.
Kamar yadda ya ce “Dukkan kuɗaɗen da nake samu suna tafiya ne a lamarin abincina da kuma kula da Keke na. Babu wani abinda ya rage. Rayuwa ƙara yin tsada ta ke nina gaji kamar yadda ya bayyana kamar dai yadda yadda abin yake damuwar sa,’’.
Da baya son a anbaci sunan say a ce gwamnati ta san irin halin da ake ciki na matsalar tattalin arziki, ta kuma ɗauki matakai domi maganin wahalhalun da ake sha.
Kamar yadda jami’in ya ƙara yin bayani, gwamnatin Jiha ta wani abu na faɗaɗa kan tsare- tsaren kawo ma jama’a taimako, sun haɗa da kayan abincin da za a sayar a farshi mai rahusa ga ƴan kasuwa masu ƙaramin ƙarfi na yin kasuwanci.
Ya ci gaba da bayanin “Muna zuba jari akan abubuwan more rayuwa da ɓangaren aikin gona domin a bunƙasa yadda za a samar da noma kayan abinci domin a ɗaukaka noman a ƙauyuka da kuma rage yawan dogaro da ake yi na shigo da kayan abincin daga wani wuri, wanda hakan ke ƙara yawan farashin kamar yadda jami’in ya ce,”.
Ya ce duk da yake ana samun ƙaruwar kuɗaɗen da ake ba Jihohi kowane wata domin samar da tallafi akan waɗansu lamurra sai dai akwai waɗansu abubuwan da kan biyo ta bayan gida , danagane da wani matakin.
Yadda Lamarin Yake A Legas
Legosian mazauna birnin Legas ,yawancin mazauna birnin sun nuna rashin jin daɗinsu kan irin wahalhalun da suke fuskanta,inda suka ce kuɗaɗen da suke samu yanzu isar su tafiyar da harkokin buƙatunsu, musamman ma kayan abinci.
Wata mai zama a Legas, Dayo Oluwa, ta ce akwai ƙari kuɗaɗen haya da kuma kayan abinci abubuwan da sun shafi kuɗaɗen da suke shigo ma iyalin ta, wanda hakan ne yasa dole suka ɗauki mataki dangane da irin nau’in abincin da za su riƙa saye ba domi kome ba sai saboda ƙaruwar farashin.
“Abubuwan da muke saye da sauƙi a shekarun baya yanzu sun yi matuƙar tsada kamar yadda ta ce,”.
Ta ce yanzu iyalin ta suna sauya ko canza kayan abincin da suka kmata su saya da masu arha ba domin kome ba sai don a samu hanyar da za a ci gaba da tafiyar da rayuwa.
Kamar yadda ta ce, kayan abinci kamar Nama, Kifi, waɗanda ashekarun baya ana samunsu a cikin abinci, yanzu maganar gaskiya an maye gurbinsu da wasu kayan abincin da ƙwai ko ponmo (fatar Saniya ), wadda ta ce bin babu tsada ana iya saye.
Oluwa haka ta ƙara yin bayani suna fuskantar wahala wajen yadda suke i- iyawa da tsadar kayan girki ko dafa abincin,saboda ta bar amfani da kananzir ta koma amfani da gas, wanda ta ce shi ma yana da tsadar gaske.
Shamsedeen Sedio,shi ma’aikaci ne, ya ce yanzu ya yi tsarin yadda zai samu cin abincoi sau biyu a rana.“ Da safe yana kashe, Naira 1,000 sai kuma wata Naira 1,000 da rana saboda irin yadda nake fuskantar matsin tattalin arziki. Sai ya lura sosai domin ya san yadda zai kashe kuɗin sa, shi ma’aikaci ne kalbashin shi bai taka kara ya karya ba kamar yadda ya bayyana,’’.















Discussion about this post