ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Ware Ɓangaren El-rufa’i: Rikicin Cikin Gida Ya Kaure A Jam’iyyar ADC, Kaduna

by Shehu Yahaya and Sulaiman
4 months ago
ADC

Wani sabon rikicin cikin gida na kara ta’azzara a jam’iyyar ADC a Jihar Kaduna, yayin da ake zargin wasu jiga-jigan jam’iyyar da kokarin rage karfin siyasar magoya bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, gabanin zaben shekarar 2027.

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun shaidawa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga gwagwarmayar neman iko da tikitin gwamna, na majalisar dokoki ta kasa da kuma na majalisar dokokin jihar, inda bangarori daban-daban ke fafatawa domin mallakar tsarin jam’iyyar tun kafin fara zabukan fidda gwani.

Rahotanni sun nuna cewa Salihu Mohammed Lukman na daga cikin fitattun mutanen da ake zargin suna amfani da tasirinsu a matakin kasa wajen tsara makomar siyasar ADC a Kaduna da kuma wadanda za su samu tikitin takara.

ADVERTISEMENT

Wannan lamari ya haddasa damuwa a bangaren magoya bayan El-Rufai, inda ake zargin cewa ana kokarin mayar da wasu daga cikin amintattunsa saniyar ware duk da rawar da suka taka wajen gina jam’iyyar a jihar.

Daga cikin wadanda ake cewa abin ya shafa akwai tsohon kwamishina Ja’afaru Sani, tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Bashir Saidu da kuma Hafsat Baba, wadanda ake kallon su a matsayin manyan kusoshin siyasar El-Rufai a Kaduna.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Magoya bayan wannan bangare sun kuma yi nuni da matsalolin shari’a da siyasa da wasu daga cikin kusa da El-Rufai ke fuskanta, musamman Bashir Saidu, a matsayin wata alama da ke nuna cewa ana matsa musu lamba daga ciki da wajen tsarin jam’iyyar.

A gefe guda kuma, wasu majiyoyi sun ce shigowar tsohon dan takarar gwamna na PDP, Isa Ashiru, cikin ADC ya sauya yanayin siyasar jam’iyyar a Kaduna, inda ake zargin wasu masu fada a ji suna son ganin shi ne ya zama zabin jam’iyyar na takarar gwamna a 2027.

Haka kuma ana rade-radin cewa an samu sabani tsakanin Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman, da Salihu Lukman, yayin da ake zargin akwai wani shiri na sake fasalin tsarin shugabanci da tasirin siyasa a jam’iyyar.

Majiyoyi sun kara da cewa ana yunkurin maye gurbin Sanata Lawal Adamu da Shuaibu Idris Mikati, yayin da ake kuma tunanin maye gurbin Sanata Abdu Kwari da Khalid Soba.

Rikicin ya kara daukar hankali ne bayan da shugabancin ADC na kasa ya dakatar da tsarin zaben cikin gida da ake gudanarwa a Kaduna.

A wata sanarwa da sakataren kwamitin zaben ADC na jihar, Dakta Mohammad Umar, ya fitar, an sanar da ‘yan takara da sauran masu ruwa da tsaki cewa an dakatar da tsarin zaben bisa umarnin sakataren jam’iyyar na kasa har sai an bayar da sabbin umarni.

Wannan mataki ya kara haifar da zargi daga bangaren magoya bayan El-Rufai, wadanda ke ganin cewa ana amfani da shugabancin jam’iyyar na kasa wajen hana su karfafa matsayinsu a cikin ADC tare da bai wa wasu masu iko damar tsara sakamakon zabukan fidda gwani.

Sai dai da yake magana ta wayar tarho, sakataren yada labarai na ADC a Kaduna, Darius Kurah, ya musanta rade-radin da ake yadawa.

Ya ce sabani da fahimtar juna abu ne da ya saba a siyasa, sannan ya musanta cewa akwai wani shiri na maye gurbin Sanata Lawal Adamu da Shu’aibu Idris Mikati.

“A dalilin tabbatar da hadin kai a jam’iyyar ne muka dage zabukan fidda gwani domin bai wa ‘yan takara damar cimma matsaya ta bai daya. Idan hakan bai yiwu ba, za mu koma tsarin zaben kai tsaye,” in ji shi.

ADC
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
ADC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
ADC
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Babban Darektan UNESCO

Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Babban Darektan UNESCO

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.