ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

by Rabi'u Ali Indabawa
1 month ago
Nijeriya

Rundunar ’Yansandan Birnin Landan ta Birtaniya (Metropolitan Police) ta tabbatar da kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a kisan wani mawaki dan asalin Nijeriya kuma dan kasar Birtaniya, Mark Orabiyi, wanda aka kashe ta hanyar caka masa wuka a lambun wani gida da ke kusa da titin Rayleigh Road.

Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Intanet rundunar ’yansandan.

’Yansandan sun ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an bincike sun garzaya wurin da abin ya faru inda suka tarar da Orabiyi da raunukan caka masa wuka. Duk da kokarin ma’aikatan agajin gaggawa, an tabbatar da mutuwarsa a wurin.

ADVERTISEMENT

“Jami’an sun isa wurin tare da ma’aikatan Ambulance na Landan kuma suka tarar da wani mutum mai shekaru 35 da raunukan wuka a lambun wani gida da ke kusa da Rayleigh Road.

“Duk da kokarin ma’aikatan jinya, abin takaici an tabbatar da mutuwarsa a wurin.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Ko da yake ba a kammala tantance gawar a hukumance ba, an bayyana sunan mamacin a matsayin Mark Orabiyi. Har yanzu jami’ai na musamman na ci gaba da bai wa iyalansa tallafi,” in ji sanarwar.

A cewar rundunar, iyalan mamacin sun bayyana shi a matsayin kaunataccen da, dan’uwa, kawu da kuma aboki.

“Mark kaunataccen da ne, dan’uwa, kawu da kuma aboki. Ya kawo soyayya, haske da farin ciki ga iyalinmu da kuma duk wanda ya san shi.

“Za mu ci gaba da tunawa da kyautatawarsa, kyakkyawar dabi’arsa da kuma baiwar da Allah ya yi masa. Kasancewarsa ta shafi rayuwar mutane da dama, kuma tarihinsa zai ci gaba da kasancewa a cikin zukatanmu har abada. Allah Ya jikansa da rahama,” kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Sai dai rundunar ’yansandan ta ce an kama wasu mutane uku da ba a bayyana sunayensu ba dangane da lamarin.

Wadanda ake zargin sun hada da maza biyu da kuma mace guda.

Sanarwar ta kara da cewa: “An kama mutane uku a ranar Juma’a, 5 ga Yuni, bisa zargin kisan kai. Wani mutum mai shekaru 27 an sake shi bisa beli yayin da ake ci gaba da bincike.

“Bayan yi musu tambayoyi, an saki wani mutum mai shekaru 24 da kuma wata mace mai shekaru 25 ba tare da daukar wani karin mataki a kansu ba.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wani mutum mai shekaru 20 ya samu raunukan caka masa wuka da dama a lamarin, amma ba su kai ga barazana ga rayuwarsa ba, kuma an kai shi asibiti domin jinya.

Da take mayar da martani, Babbar Jami’ar Bincike, Joanna Yorke, wadda ke jagorantar binciken, ta yi kira ga jama’a da su taimaka da bayanai domin gano gaskiyar abin da ya faru.

“Wannan lamari ne mai matukar tayar da hankali, kuma zuciyata tana tare da iyalan Mark da wadanda yake kauna.

“Bincikenmu na ci gaba cikin sauri. Ina kira ga duk wanda yake a yankin lokacin da lamarin ya faru da ya tuntubi ’yansanda.

“Muna son jin ta bakin duk wanda yake da bidiyon CCTB ko wani hoton bidiyo daga safiyar ranar da abin ya faru wanda zai taimaka mana a bincikenmu,” in ji Yorke.

A wani rahoto makamancin wannan, PUNCH Metro ta ruwaito cewa wata kotu a Birtaniya ta tsare wani mutum mai shekaru 32, Madwell Oguanaya, bisa zargin kashe wani dan Nijeriya mai shekaru 41, Taiwo Ekerin, bayan wani hari da ya faru a Lewisham da ke Landan.

Rundunar Met Police ta ce an tuhumi Oguanaya da laifin kisan kai bayan Ekerin ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wata arangama.

Nijeriya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

LABARAI MASU NASABA

NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026
NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

July 24, 2026
Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

July 24, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Kama Hanyar Cin Gashin Kanta

Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Kama Hanyar Cin Gashin Kanta

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.