Rahotanni sun ce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta sanya farashin Yuro miliyan 150 kan ɗan wasan gabanta, Victor Osimhen, ga duk wata ƙungiyar da ke son ɗaukarsa.
Chelsea na daga cikin ƙungiyoyin da ke nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan na Super Eagles, wanda ya zama abin nema a kasuwar ‘yan wasa sakamakon bajintar da yake nunawa.
Jita-jitar barin Galatasaray da Osimhen zai yi ta ƙara ƙarfi ne bayan kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya bayyana cewa an cire ɗan wasan daga tawagar Nijeriya da za ta buga wasannin sada zumunta ne saboda batun canja ƙungiya.
Wannan bayani ya jawo muhawara tsakanin magoya baya da masu sharhi kan ƙwallon ƙafa, inda da dama ke ganin Osimhen na iya komawa wata ƙungiya kafin fara kakar wasa mai zuwa.















Discussion about this post