Gamayyar kungiyoyin rajin kare hakkin dimokradiyya da fararen hula, sun roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC da su amince da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bai wa jam’iyyun siyasa wa’adin zuwa ranar Juma’a 17 ga watan Yunin 2022 da su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da mataimakinsa ga hukumar.
- 2023: Wasu ‘Yan Jam’iyyar APC Sun Nemi Tinubu Ya Dauki Gwamnan Neja Mataimaki
- 2023: Ban Ce Zan Dauki Mataimaki Musulmi Ba – Tinubu
A wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, gamayyar kungiyoyin da suka hada da kungiyar kare hakkin ‘yan asalin kasa (PAIR) da Civil Society Action for National Inclusion (CSANI), da Society for Equity and Gender Advocacy (SEGA), sun ce, Mustapha ya yi fice a cikin duk wasu da ake yi wa hasashen basu mataimakin.
“Boss Mustapha mai rikon amana ne kuma ba shi da wata hayaniya ko wani cikas da zai durkusar da shirin APC na ci gaba da rike madafun iko a 2023,”
“A matsayinsa na Kiristan Arewa, mustapha zai dace da ma’aunin da ake bukata, tare da rage fargaba a wurin al’umar Kirista. da kuma tabbatar da cewa za a kare muradun Arewa,” in ji kungiyar.
A cikin sanarwar da Isa Pai, Chukwudi Emmanuel da Fola Akin suka sanya wa hannu, sun bayyana cewa, “a tsawon shekaru, Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya ya nuna kwazo a cikin ayyukansa, jajircewa da kuma biyayya ga manufofin shugaban kasa Muhammadu. Buhari.
“A matsayinsa na shugaban kwamitin shugaban kasa kan COVID-19, Boss Mustapha ya nuna cewa yana iya aiwatar da lamuran da Suka shafi kasa cikin gaggawa, abin da ake bukata shi ne mutumin da zai iya jagoranci, tsarawa, kai tsaye da mayar da hankali.”
Don haka kungiyar ta yi kira ga “Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar APC da su aiwatar kamar yadda suka saba yi.
“Yayin da gaba ta karshe ko gab da kammala zaben dan takarar mataimakin shugaban kasa, Boss Mustapha ya fi kowa dacewa a halin yanzu ta fuskar tarihinsa mara lahani, aikin gwamnati da kasa, alkibla da manufa.”