ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gayyato Jakadun Kasashen Waje 17 Ya Kara Wa Bukukuwan Sallah Armashi A Katsina

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
4 months ago
Katsina

Yanzu haka gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta kudiri aniyar kara inganta bukukuwan Sallah da aka saba gudanarwa a masarautar Katsina da kuma Daura.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta ce dole ne kowane hakimi ya tabbatar ya yi hawan sallah sai dai idan akwai wata matsala da ta bayyana wanda ba zai samu damar hawa ba.

  • Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
  • Saraki Ya Soki Gwamnatin Kwara Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro

A bisa haka Gwamna Radda ya ce idan har mai martaba sarkin Katsina zai yi hawa to babu dalilin da zai sanya hakimi ko wakili ace bai yi hawa ba sai da kwakkwaran dalili.

ADVERTISEMENT

Tun bayan hawan wannan gwamnati a shekarar 2023 gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya zo da wasu sabon tsare-tsare da za su ci gaba da kara inganta hawan sallah wanda ya ce shi kadan abin da ya rage na al’ada da za a iya nunuwa duniya a wannan lokaci.

A wannan shekarar Jihar Katsina ta karbi bakuncin Jakadun kasashen waje 17 domin shaida yadda ake gudanar da bukukuwan Sallah a masarautar Katsina da kuma Daura.

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

Baya ga halartar hawan sallah, an gudanar da wani kwarya-kwaryan yawon bude ido ga wadannan Ambasadoji domin ganin abubuwan tarihi da Jihar Katsina take da su shekara da shekaru wanda kuma suka bayyana gamsuwa da yadda suka ga abubuwan

Wani abin da ya dauki hankali da birgewa game da wannan ziyara ta Jakadun shi ne yadda suka yi shiga irin ta Malam Bahaushe wanda ta ba su damar sajewa da Hausawa, tare da fitar da tsoron da ya kama duk mai sha’awar zuwa Katsina saboda matsalar tsaro.

Idan za a iya tunawa Jihar Katsina ta yi suna a baya wajen shirya mafi kyan hawan sallah a kasar Hausa inda baki daga kasashen waje ke yi tururuwa domin kashe kwarkwatar ido a lokacin bukukuwan Sallah.

Sannu a hankali wannan lamari ya rika ja da baya, sai da ta kai, za a yi hawan sallah har gama amma baki musamman turawa ana iya kirga wadanda suka halarci bikin sallah saboda yadda abubuwa suka ja baya.

To sai dai yunkurin gwamnatin jihar Katsina na kara inganta wannan dadadiyar al’ada, ana iya cewa tana samun ci gaba da ta fannoni daban-daban musamman yadda aka ga cewa gwamna Radda da gaske yake a kan batun hawan.

Yanayin yadda tsarin hawan sallah a Katsina yake abin birgewa ne so sai. Shagulgulan Sallah dai kwana biyu kawai wato ranar idi da kuma ranar hawan bariki kamar yadda ake kiran da tun asali.

A ranar farko gwamnan jihar Katsina zai kai ziyara fadar mai martaba sarki a yayin da shi ma Sarki zai kai ziyara a fadar gwamnatin jihar Katsina domin gaisuwar Sallah da kuma yin hawa.

Wato abubuwan da suka bambanta wannan hawa ba yanzu da kuma na sauran lokuta a baya su ne kamar haka; yanzu akwai doka dole ne kowane hakimi ya yi hawa sai dai idan akwai wata matsala.

Na biyu kuma gwamnati na fitar da kudi domin taimaka wa masu wannan hidima fiye da lokutan baya, wanda hakan ke kara masu kaimi na ganin sun burge jama’a musamman baki.

Abu na Uku kuma shi ne yadda aka dawo da ziyarar manyan baki a wannan hawan sallah musamman da yanzu gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ke gayyato jakadun kasashen waje domin su shaida yadda wannan al’ada take a jihar.

Sai dai a wannan shekarar gwamnatin jihar Katsina ta shirya wani abu da bata saba yi ba, inda ka shirya wasu tsare-tsare domin wadannan baki da aka gayyato wato jakadun kasashe wajen har 17.

Ita dai wannan tawaga ta Jakadun kasashen waje wanda jakadan kasar Bulgium ya jagoranta Ambasada Peter Leenknegt ta iso Katsina a jajibirin Sallah inda suka samu tarba daga gwamna Radda da mukaraban gwamnatin sa

Sannan sun sauka ne a filin tashi da sauka na Malam Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina domin halartar bukukuwan Sallah da suka gudanar a masarautar Katsina da Daura

Daga cikin Jakadun da suka ziyarci birnin Katsina sun hada da jakadan kasar Masar Mohammed Fouad da na Kasar Natharland Bengt Ban Loosdrecht da na kasar Spain Felid Costales Artieda da na kasar Poland Michael Cygan.

Sauran sun hada da na kasar Switzerland Patrick Felid Egloff da na kasar. Slobakia Martin Podstabek da na kasar Argentina Nicolas Perazzo da na kasar Congo Pascaline Gerengbo Yakibu da sauran jakadun kasashen waje

Ziyarar na daga cikin shirye-shiryen bikin Durbar na 2026, wanda ke nuna dimbin al’adun gargajiya na al’ummar Jihar Katsina.

Da yake jawabi kan muhimmancin ziyarar, Gwamna Radda ya bayyana zuwan jakadun a matsayin alamar kara bunkasar sha’awar duniya kan al’adun jihar Katsina.

“Mun yi matukar farin ciki da karbar wannan tawaga ta jakadu masu daraja da suka zo domin ganin al’adunmu na musamman wanda hakan wata alama ce alama ce ta hadin kai, zaman lafiya da kuma asalin al’ummarmu,” in ji gwamnan.

Ya kara da cewa ziyarar za ta kara karfafa alakar diflomasiyya tare da tallata Jihar Katsina a matsayin wuri mai jan hankalin yawon bude ido na al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa.

Gwamna Radda ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na kiyaye al’adun gargajiya na jihar tare da inganta zaman lafiya da ci gaba.

Tunda farko an shirya wa Jakadun wassani gargajiya da suka hada da Dambe da kokuwa da shadi da sauran abubuwan gargajiya domin nishadantar da su a matsayin baki.

Kazalika an zagaya da su wuraren tarihi da muhimman wuraren da gwamnatin jihar Katsina ta gudanar da aikin raya kasa a karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda a jihar Katsina.

Tambaya dai ita ce nawa aka kashe wajen gayyato Jakadun kasashen waje domin su halarci wannan bukukuwa na Sallah, sannan gayyato su zai karawa wannan al’ada tagomashi ko kuma?

Katsina
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Ko Shirin Da Gwamnatin Jihar Katsina Ke Yi Wa Manoma Zai  Amfane Su A wannan Daminar?
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mutum 1,000 Daga Jam’iyyar ADC Sun Koma PDP A Jihar Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina
Katsina
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe
  • Sulaiman
    GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara
  • Sulaiman
    Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
  • Sulaiman
    Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

MASU ALAKA

Sabbin Ministoci
Labarai

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
Labarai

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
Manyan Labarai

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Next Post
Zargin Cin Hanci: Babu Wani Shirin Tsige El-Rufai – Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna

Mahaifiyar El-Rufai Ta Rasu, Akwai Yiwuwar Ba Zai Halarci Jana'izarta Ba

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.