ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
3 months ago
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki ma’aikatan gandun daji mutum 1,000 waɗanda za su tsare dazuzukan da ke fama da matsalolin tsaron a Jihar baƙi ɗaya

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana haka a jin kaɗan bayan kammala wani taron gaggawa da yi da Malamai a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ya amince a ɗauki ma’aikatan gandun daji guda dubu ɗaya, domin tsare dazuzuka a Jihar Katsina.

ADVERTISEMENT

“Ina miƙa godiya ta bisa wannan al’amari na amincewar shugaban ƙasa da ya amsa rokon mu na ɗaukar ma’aikatan gandun daji 1,000 wanda za a ɗauki matasa maza da mata wanda kuma za su yi aiki tare da hukumomin tsaro” inji shi

Gwamnan wanda ya nuna irin ƙoƙarin da ake yi na ganin an kawo ƙarshen matsalolin tsaro ta hanyar haɗa kai da Malaman Addini a matsayin wani bangare da za a iya samun cigaba da zaman lafiya tare da lalubo hanyar magance matsalolin tsaro.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Dikko Raɗɗa wanda ya ce tattaunawa da malamai ya zama wajibi domin ta haka ne za su san girman matsalar tsaro tare da neman hanyar warware matsalolin ta fuskoki da dama.

Ya ce dalilin wannan zama da malaman addini shi ne domin su ji kai tsaye daga wajen Malaman sannan su fahimci yanayin halin tsaro da ake ciki daga ƙarshe a nemi shawarar su wajan magance ta.

Ya ƙara da cewa girman wannan matsala ta kai inda ba za a iya barin jami’an tsaro da ita ba su kaɗai, shigowar al’umma musamman malamai zai zama hanyar samun zaman lafiya

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa akwai masu taimakon ƴan bindiga a cikin al’umma, ta hanyar bada bayanan sirri da kuma sayar da shanun da aka barayin dajin suka sato

Kazalika gwamna Raɗɗa ya yabawa gwamantin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu saboda taimakon da ta yi na ƙara turo jami’an tsaro a Jihar Katsina

“Yanzu mun ƙara samun jami’an tsaro da dama da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda da jami’an hukumar farin kaya ta DSS wanda hakan ke ƙara ƙarfafa mana gwiwa cewa dole mu nuna godiya ƙwarai da gaske” inji shi

Daga ƙarshe ya yi kira ga al’ummar Jihar Katsina da su kasance masu lura da abubuwan da ke zuwa suna dawowa domin ta haka ne za taimakawa gwamnati wajen dawowa da zaman lafiya.

Tsaro
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
Tsaro
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin PDP Da ADC Yau

Mutum 1,000 Daga Jam'iyyar ADC Sun Koma PDP A Jihar Katsina

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.