ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal Ya Zama Ɗan Takarar APC A Zamfara, Ya Yi Alƙawarin Ƙara Ayyukan Ci Gaba

by Sulaiman
4 months ago
APC

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alƙawarin ci gaba da ƙara ayyukan raya ƙasa domin inganta rayuwar al’ummar jihar.A ranar Alhamis ne gwamnan ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC domin zaɓen gwamnan jihar Zamfara na shekarar 2027.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na gwamna na APC a Zamfara, Alhaji Babagana Uba, ya sanar da cewa an amince da Gwamna Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar jam’iyyar baki ɗaya bayan samun ƙuri’u 301,893.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an gudanar da amincewar ne a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar Zamfara, tare da sa ido daga jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce: “Kwamitin zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Zamfara ya ayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC shi kaɗai domin babban zaɓen shekarar 2027.

“Kwamitin ya karɓi sakamakon amincewa daga jami’an tattara sakamako na dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar, waɗanda Malam Abubakar Mohammed Nakwada, shugaban tattara sakamako na APC a jihar, tare da sauran mambobin tawagar tattara sakamako suka sanya wa hannu.”

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Shugaban kwamitin ya kuma bayyana sakamakon amincewar da aka samu daga ƙananan hukumomi daban-daban kamar haka: Anka 16,607; Bakura 18,112; Birnin Magaji 15,440; Bukkuyum 11,406; Bungudu 24,406; Gummi 23,024; Gusau 61,072; Kaura Namoda 18,315; Maradun 15,624; Maru 17,341; Shinkafi 15,204; Talata Mafara 22,884; Tsafe 19,354; da Zurmi 22,506.Da yake jawabi bayan ayyana shi a matsayin ɗan takara, Gwamna Dauda Lawal ya gode wa al’ummar Zamfara bisa amincewa da goyon bayan da suka nuna masa.

Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da tattalin arziki.

“A yau rana ce mai tarihi a siyasar jihar Zamfara, domin dukkan manyan masu ruwa da tsaki sun haɗu ƙarƙashin inuwa ɗaya cikin haɗin kai,” in ji gwamnan.

“Da aka ayyana ni a matsayin ɗan takarar jam’iyyarmu ta APC, ina godiya ga dukkan mambobin jam’iyya da al’ummar jihar bisa amincewar da suka yi da gwamnatina.

“Wannan gagarumin goyon baya da soyayya da aka nuna mini zai ƙara ƙarfafa mini gwiwa wajen ci gaba da ƙoƙarin ceto da sake gina jihar Zamfara.

“Ina kuma godiya ga shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani da sauran mambobinsa da suka tabbatar da gudanar da zaɓen cikin nasara a jihar Zamfara.”

APC
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Kashe Ƴansanda Da Sojoji 17 A Yobe

Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Kashe Ƴansanda Da Sojoji 17 A Yobe

LABARAI MASU NASABA

APC

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
APC

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
APC

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
APC

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.