ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Kashe Ƴansanda Da Sojoji 17 A Yobe

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago

Rundunar Ƴansandan Nijeriya ta tabbatar da kisan jami’anta 17 da kuma wasu sojoji da ba a bayyana adadinsu ba a wani hari da ƴan ta’addan Boko Haram suka kai Makarantar Horar da Runduna ta Musamman ta Sojojin Nijeriya da ke Buni Yadi, a Ƙaramar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Kakakin rundunar ƴansandan, Anthony Okon Placid, ne ya tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 16 ga Mayun 2026.

Placid ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:15 na dare a ranar 8 ga Mayun 2026.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana cewa jami’an ƴansandan suna cikin horarwar dabarun yaƙi da ta’addanci lokacin da ƴan bindigar suka kai wani harin haɗin gwiwa daga wurare daban-daban kan sansanin sojin.

“Jami’an sun sadaukar da rayukansu wajen bautawa ƙasa bayan harin ta’addanci da aka kai Makarantar Horar da Runduna ta Musamman ta Sojojin Nijeriya da ke Buni Yadi,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

Ya ƙara da cewa wasu sojoji ma sun mutu yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin, sai dai bai bayyana adadin sojojin da suka mutu ba. Rundunar sojin Nijeriya ma ba ta fitar da cikakken adadin ba.

Majiyoyi a Buni Yadi sun ce maharan sun yi artabu mai tsanani da jami’an tsaro wanda ya ɗauki sama da sa’o’i uku.

“‘Yan ta’addan sun janye da misalin ƙarfe 4:00 na safe bayan sun kashe jami’an ƴansanda 17 da sama da sojoji 20,” in ji wani ɗan ƙungiyar Sa Kai.

Ya ƙara da cewa sojoji sun kwashe gawarwakin jami’ansu nan take bayan artabun, yayin da ƴansanda ba su samu damar kwashe gawarwakin jami’ansu ba sai washegari.

“Daga baya ƴansanda sun kwashe gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’a da ke Damaturu, daga inda motocin ƴansanda suka kai su Maiduguri,” in ji shi.

Ya bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin artabu da aka gani a baya-bayan nan, yana mai cewa jami’an tsaro da mazauna yankin sun yarda cewa ba su taɓa ganin irin wannan ba tun bayan fara tayar da ƙayar bayan Boko Haram.

“Musayar wutar da muka gani a wannan dare ta bambanta. Ba mu taɓa ganin irinta ba tun bayan fara rikicin Boko Haram,” in ji shi.

Ya kuma ce daga ƙarshe ƴan ta’addan sun ja da baya bayan sun fahimci cewa ba za su iya ƙwace sansanin ba, ko sace makamai da lalata kayan aikin soja.

A baya ma ƴan Boko Haram sun sha ƙoƙarin ƙwace sansanonin soja a yankin saboda muhimmancin Buni Yadi wajen ayyukan yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas.

Sufeto Janar na Ƴansanda, Olatunji Disu, ya bayyana jami’an da suka mutu a matsayin jarumai masu kishin ƙasa da jajircewa wajen kare tsaron ƙasa.

Ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa rundunar ƴansanda tare da haɗin gwiwar rundunar soji da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka kai harin domin hukunta su.

A wani ɓangaren kuma, Kwamishinan Ƴansandan Jihar Yobe, Usman Jibrin, ya kai ziyara Makarantar Horar da Runduna ta Musamman ta Sojojin Nijeriya a madadin Sufeto Janar, inda ya gana da kwamandan makarantar, Birgediya Janar A.C. Enuagu, sauran jami’an soja da kuma ƴansandan da suka tsira daga horarwar.

Ya ƙarfafa wa sauran waɗanda ke samun horarwa gwiwa da su ci gaba da kammala shirin horarwar domin girmama abokan aikinsu da suka rasu.

Ya sake jaddada cewa rundunar ƴansanda tare da haɗin gwiwar rundunar soji da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da aiki domin tabbatar da kama maharan tare da hukunta su.

Mazauna garin Buni Yadi sun nuna alhini matuƙa kan kashe jami’an ƴansanda da sojojin.

Wani mazaunin yankin, wanda ya ce ya yi karatu tare da ɗaya daga cikin jami’an da aka kashe, ya bayyana cewa al’umma sun yi ƙoƙarin neman a ba su gawarwakin domin gudanar da jana’iza.

“Abin takaici, an ƙi amincewa da buƙatarmu a Asibitin Koyarwa na Jami’a da ke Damaturu kafin a kai gawarwakin Maiduguri inda aka yi musu jana’iza,” in ji shi.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Next Post
Kotu Ta Ba Da Belin El-Rufai Kan Naira Miliyan 100

Kotu Ta Ba Da Belin El-Rufai Kan Naira Miliyan 100

LABARAI MASU NASABA

SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.